Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me za ka yi idan an zolaye ka?

Me za ka yi idan an zolaye ka?

 Zolaya ba batun wasa ba ne. Wani bincike da aka yi a kasar Britaniya ya nuna cewa matasa fiye da kashi arba’in cikin dari da aka ba da labari cewa sun kashe kansu a sakamakon zolayar da aka yi musu ne.

 Mene ne zolaya?

 Zolaya ba kawai a ce an duki mutum ba. Ya kunshi abubuwa na biye.

  •   Zagi. Celine ’yar shekara 20 ta ce: “’Yammata sukan yi zagi sosai. Ba zan taba manta da irin sunayen da suke kirana da su da kuma abubuwan da suke gaya mini ba.” Suna sa in ji ni ba komi ba kuma an ki ni, ban da haka, ban da amfani. Gwamma duka da zagi.”

  •   Ware kai daga mutane. “Wata yarinya mai suna Haley ’yar shekara 18 ta ce: “’Yan ajinmu sun soma guduna. Kuma a lokacin cin abinci ba sa so in zauna tare da su. Na yi shekara guda ina cin abinci ni kadai kuma ina ta kuka.”

  •   Zolaya ta Intane. “Wani yaro mai suna Daniel dan shekara 14 ya ce: “Da kalilan kalmomi kawai za ka iya bata sunan mutum ko kuma rayuwarsa ta Intane. Hakan ba kara gishiri ba ne, yana faruwa!” Kari ga haka, zolaya ta Intane ya kunshi aika hotuna da sakonnin banza ta wayar salula.

 Me ya sa mutane suke zolayar wasu?

 Ga wasu dalilai nan.

  •   Su ma an taba zolayar su. Wani matashi mai suna Antonio ya ce: “Na gaji da yadda tsarata suke zolayana sai ni ma na soma zolayar wasu. Amma daga baya na gane cewa bai dace in rika zolayan wasu ba!”

  •   Ba su da gurbi mai kyau. Wani littafi mai suna Life Strategies for Dealing With Bullies da Jay McGraw ya rubuta, ya ce: “A yawancin lokaci yara da suke zolayar wasu suna hakan ne don sun ga yadda iyayensu da ’yan’uwansu da danginsu suke zolayar wasu.

  •   Suna yi kamar sun fi kowa karfi, amma hakan ba gaskiya ba ne. Wata mai suna Barbara Coloroso ta rubuta a littafinta mai suna The Bully, the Bullied, and the Bystande, cewa: “Yaran da suke zolayar mutane, a yawancin lokaci suna nuna kamar sun fi wasu karfi don su boye wani abu ko kuma kasawarsu ne.

 Su waye ne aka fi zolayar su?

  •   Wadanda suke ware kansu. Matasan da suke ware kansu da ba sa cudanya da mutane, su ake yawan yi wa zolaya.

  •   Matasan da suke dabam. A kan zolayi wasu matasa saboda irin tufa da suke sanyawa, don kabilarsu ko kuma addininsu, har ma da wanda ya nakasa, abin da dai zai sa mai zolayar jin dadin yin zolayarsa.

  •   Matasan da ba su da gaba gadi. Ana yawan zolayar matasan da ba sa daraja kansu. Wadannan ne aka fi zolayarsu da yake an san cewa ba za su iya ramawa ba.

 Me za ka yi idan aka zolaye ka?

  •   Ka kyale su. Wata matashiya mai suna Kylie ta ce: “Masu zolaya suna son su yi nasara wajen sa ka ji kamar kai ba kome ba. Idan ka kyale su lokacin da suke zolayarka za su rabu da kai.” Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-hikima ya kan danne shi ya kwabe shi.”—Misalai 29:11.

  •   Kada ka rama. Ramako ba shi ne zai magance matsalar ba, amma kara matsalar zai yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta.”—Romawa 12:17; Misalai 24:19.

  •   Kada ka sa kanka cikin matsala. Idan zai yiwu, ka guji wurare da kuma yanayoyin da za su sa a yi maka zolaya.Misalai 22:3.

  •   Ka gwada yadda za ka iya ba da amsar da ba ka zata ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amsa magana da tattausan harshe takan kwantar da hasala.”—Misalai 15:1.

  •   Ka yarda da hakan. Alal misali, idan aka zolaye ka cewa kana da kiba, za ka iya yarda ka ce, “Da a ce zan iya rage kiban nan!”

  •   Ka bar wurin. Nora ’yar shekara 19 ta ce: “Idan ka yi shiru zai nuna cewa ka manyanta kuma ka fi wanda yake maka zolayar karfi. Kuma hakan yana nufin kana da kamewa, wato halin da wanda yake maka zolayar bai da shi.”

  •   Ka kasance da gaba gadi. Wata yarinya mai suna Rita ta ce: “Masu zolaya suna sanin lokacin da muka damu kuma a wannan lokacin ne za su zolaye mu don mu ji kunya.”

  •   Ka gaya wa wani. Wani bincike ya nuna cewa fiye da rabin mutanen da ake zolayar su ta Intane ba sa gaya wa kowa abin da suke fuskanta, watakila saboda kunya (musamman idan maza ne) ko kuma suna jin tsoron ramawa. Amma ya kamata mu sani cewa, masu zolaya sukan ji dadin yin hakan a boye. Amma gaya wa wasu game da yanayin mataki ne na farko da zai sa a daina yi ma ka zolaya.