Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

A Shirye Na Ke In Bar Gida?

A Shirye Na Ke In Bar Gida?

 Tunanin barin gida yana da dadi kuma yana da ban tsoro. Ta yaya za ka sani ko za ka iya zaman kanka?

 Ka bincike dalilan da ya sa ka ke so ka bar gida

 Akwai dalilai da yawa da za su sa ka yi tunanin barin gida, ba duka ne ke da kyau ba. Alal misali, wani sa’úrayi mai suna Mario ya ce, “ina son in bar gida saboda in guje yin ayyuka a gida.”

 Gaskiyar ita ce, kila ba za ka sami ’yanci sosai in ka fita ba. Wata mai suna Onya mai shakara 18 ta ce: “Idan ka bar gida, dole ne ka kulla da wurin da ka ke zama, ka yi wa kanka tanadin abinci, ka biya bukatun kanka kuma babu iyayenka kusa da za su taimaka maka!”

 Gaskiyar batun: Ya kamata ka fahimci dalilin da ya sa ka ke so ka bar gida, hakan zai taimake ka ka sani ko ka kai barin gida.

 Ka yi tunani da kyau

 Yesu ya ce: “Gama wane ne a cikinku, kadan yana so ya gina soro, ba shi kan fara zaunawa tukuna, ya yi lissafin tamanin gini, ko yana da abin da za ya gama shi?” (Luka 14:28) Ta yaya ne za ka yi “lissafin” ko ka isa barin gida? Ka bincike kanka a wuraren nan.

ZA KA IYA RIKE KUDI YADDA YA KAMATA?

 Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kudi za ta iya kāre mutum.’ Mai-Wa’azi 7:12.

  •  Za ka iya yin ajiyar kudi?

  •  Kai mai son kashe kudi barkatai ne?

  •  Kai mai yawan son rancen kudi ne?

 Idan amsarka e ce ga wadannan tambayoyi, to burinka na son zama da kanka ba zai kasance da sauki ba!

 Wata mai suna Danielle ta ce: “Yaya na ya bar gida sa’ad da yake shekara 19. A cikin shekara daya, kudinsa duk sun kare, banki ta karbe motarsa don bai iya biyan bashin da ya karba ba, kuma ba wanda yake so ya ba shi bashin kudi, yanzu roko yake ya komo gida.”

 Abin da za ka iya yi yanzu: Ka tambaye iyayenka ko nawa ne suke kashewa kowane wata. Yaya suke daidata kasafin kudin da suke samowa da wanda suke kashewa? Yaya suke iya yin ajiyar kudi?

 Gaskiyar batun: Idan ka koyi yin amfani da kudi yayinda ka ke tare da iyayenka, hakan zai taimake ka ka daidaita sha’anin kudi a lokacin da ka ke zaman kanka.

  KANA DA JURIYA?

 Littafi Mai Tsarki Ya ce: “Kowane mutum za ya dauki kayan kansa.” Galatiyawa 6:5.

  •  Kai mai shiririta ne?

  •  Sai iyayenka sun tunashe ka kafin ka yi ayyukanka na gida?

  •  Kana yawan ketare dokar dawowa gida da sauri?

 Idan amsarka e ce ga wadannan tambayoyin, to kila zai yi maka wuya sosai ka yi zaman kanka.

 Wata mai suna Jessica ta ce: “Idan kana zaman kanka, za ka ga cewa akwai abubuwan da ba ka jin dadin yin su, amma kuma dole ka dinga yin su. Ba wanda zai ce maka ka yi su, saboda haka, dole ka karfafa kanka kuma ka yi su.”

 Abin da za ka iya yi yanzu: Ka yi kokari ka dauki wata daya kana ayyuka dabam dabam a cikin gida. Alal misali, ka share gidan da kanka, ka wanke tufafinka, ka yi cafene, ka dafa abinci kowane yamma ka kuma yi wankewanke bayan cin abincin. Hakan zai taimaka maka ka san yadda rayuwarka za ta kasance idan ka soma zaman kanka.

 Gaskiyar batun: Idan za ka yi zaman kanka dole ne ka zama mai juriya.

Barin gida ba tare da yin shiri ba, yana kama da mutum ya yi tsalle daga jirgin sama kuma bai koyi yin amfani da laima mai saukar ungulu ba

  KANA IYA KAME KANKA?

 Littafi Mai Tsarki Ya ce: “Ku kawar da dukan wadannan; fushi, hasala, keta, tsegumi.”​—Kolosiyawa 3:8.

  •  Yana maka wuya ka yi cudanya da wasu?

  •  Kana iya kame kanka yayinda zuciyarka ta baci?

  •  Kana son a dinga bin ra’ayinka a kowane lokaci?

 Idan amsarka e ce ga wadannan tambayoyin, to watakila zai yi maka wuya ka zauna tare da abokin haya ko kuma idan ka yi aure nan gaba.

 Wata mai suna Helena ta ce: “Zama tare da abokiyata ya fallasa inda na ke da kasawa.” Na ga cewa ba zan bukaci wasu su gane bakin ciki wanda damuwa ke jawo mini ba. Dole in nemi hanyar da zan magance damuwar da kaina.

 Abin da za ka iya yi: Ka koyi zaman lafiya tare da iyayenka da kuma ’yan’uwanka. Hakika, idan ka iya jurewa da kasawar wadanda ka ke zama da su yanzu, hakan zai nuna yadda za ka iya jurewa da kasawar duk wanda za ku zauna tare a nan gaba.

 Gaskiyar batun: Zaman kanka ba hanyar guje wa nawayarka ba ne, amma wata hanya ce da za ka koyi abin da zai taimake ka. Zai dace ka nemi shawara wajen wadanda suke zaman kansu. Ka tambaye su, to mene ne suka so su sani a dā da suka sani yanzu. Yana da kyau mutum ya yi hakan a duk wani shawara da zai yanke!