Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Abin da Zai Taimaka wa Masoyan da Suka Rabu

Abin da Zai Taimaka wa Masoyan da Suka Rabu

 Wani mai suna Steven ya ce: “Bayan da muka rabu da budurwata, sai na ji kamar zan mutu. A gaskiya ban taba bakin ciki kamar haka a rayuwata ba.”

 Ka taba fadawa cikin irin wannan yanayin? Idan amsarka e ce, wannan talifin zai taimaka maka.

 Yadda mutum zai iya ji bayan rabuwa

 Idan saurayi da budurwa suka rabu, su biyun za su iya yin bakin ciki.

  •  Idan kai ka ce ku rabu, za ka iya tunani kamar Jasmine, wadda ta ce: “Idan na tuna yadda na sa masoyina na dā bakin ciki, hakan yana sa zuciyata ta dame ni sosai. Ba na so in sake yin irin wannan halin.”

  •  Idan kuma ba kai ka ce ku rabu ba, watakila za ka ji kamar za ka mutu. Wata mai suna Janet ta ce: “Na yi fama da abubuwa dabam-dabam,” kuma hakan “ya haɗa da fushi da tunani iri-iri da bakin ciki mai tsanani. Sai bayan shekara daya kafin na yarda cewa mun rabu da gaske.”

 Gaskiyar al’amarin: Rabuwa tana iya sa mutum ya yi bakin ciki sosai kuma ya ji ba dadi, kamar yadda wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya fada cewa: “Zuciya mai bakin ciki tana shanye karfin mutum.”​—Misalai 17:​22, Littafi Mai Tsarki Juyi Mai Fitar da Maana.

 Abin da za ka iya yi

  •  Ka tattauna batun da wani da ya manyanta. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi kauna yake yi, kuma an haifi dan’uwa domin kwanakin shan wuya.” (Misalai 17:17) Idan ka gaya wa iyayenka ko wani da ya manyanta yadda kake ji, hakan zai iya taimaka maka ka kasance da ra’ayi mai kyau.

     Janet ta ce: “Na yi watanni da yawa ina zama ni kadai kuma ban gaya wa kowa abin da yake damu na ba. Amma daga baya na gane cewa abokai za su iya taimakawa. Sai da na fada abin da ke damu na kafin na sami kwanciyar hankali.”

  •  Ka koyi darasi daga abin da ya faru. Wani karin magana da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta ce: “Ka nemi hikima da basira!” (Misalai 4:​5, Littafi Mai Tsarki) Idan mun shiga tsaka mai wuya, a lokacin ne za mu san irin halin da muke da shi kuma za mu san ko mun manyanta ko a’a.

     Steven ya ce: “Bayan da muka rabu, wani abokina ya tambaye ni cewa,Me ka koya daga dangantakarka da budurwarka ta dā, kuma ta yaya hakan zai taimaka maka a nan gaba?’”

  •  Ka yi addu’a. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka.” (Zabura 55:22) Yin addu’a zai iya taimaka wa mutumin da yake fama da irin wannan bakin cikin kuma zai sa shi ya kasance da ra’ayi mai kyau.

     Wata mai suna Marcia ta ce: “Ka yi addu’a kowane lokaci. Jehobah ya san yanayin da kake ciki fiye da yadda kai ka sani.”

  •  Ka taimaka wa wasu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na wadansu kuma.” (Filibiyawa 2:4) Idan kana taimaka wa wasu, hakan zai iya sa ka manta da rabuwar.

     Wata mai suna Evelyn ta ce: “Rabuwa da masoyinka ba abu mai sauki ba ne kuma tana da zafi sosai. Amma a hankali abubuwa za su daidaita. Da na kwantar da hankalina sai na manta da batun.”