Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Daina Bakin Ciki?

Ta Yaya Zan Daina Bakin Ciki?

 Me za ka yi?

 Ka yi la’akari da yanayoyin nan:

 Ba abin da yake sa Jennifer farin ciki. Tana kuka kowace rana ba gaira ba dalili. Ba ta son ganin mutane kuma da kyar take cin abinci. Ba ta iya barci da kyau kuma yana mata wuya ta tattara hankalinta a wuri daya. Hakan ya sa Jennifer damuwa kuma ta tambayi kanta cewa: ‘Me yake dami na? Zan sake dawowa yadda nake a dā kuwa?’

 Mark yana kokari sosai a makaranta a dā. Amma yanzu ya tsane makaranta kuma hakan ya sa ba ya cin jarrabawa. Dā yana jin dadin motsa jiki amma yanzu ya daina. Abokansa sun rasa abin da yake damunsa. Iyayensa ma sun damu sosai. Wannan matsalar na dan lokaci ne ko za ta ci gaba?

 Kana fama da irin matsalar da Jennifer da Mark suka fuskanta? Idan e ce amsarka, me za ka iya yi? Ga matakai biyu. Za ka iya zaban daya.

  1.   Ka magance matsalar da kanka

  2.   Ka gaya wa wanda ya manyanta

 Za ka iya gani kamar Mataki na A shi ne mafita, musamman ma idan ba ka so ka yi magana da kowa. Amma shi ne mafita kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Biyu sun fi daya, . . . Gama idan daya daga cikinsu ya fādi, dayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya fādi yana shi kadai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi.”​—Mai Wa’azi 4:​9, 10, Littafi Mai Tsarki.

 Alal misali, a ce ka bata a cikin wata unguwa da ke cike da masu aikata laifi. Ga shi dare ya yi kuma kana ganin mutanen da ba ka sansu ba a gefe-gefe. Me za ka yi? Za ka iya kokari ka nemi hanya da kanka. Amma zai dace ka tambayi wani natsattsen mutum ya nuna maka hanya, ko ba haka ba?

 Bakin ciki yana kama da wannan unguwa mai hadari. A wasu lokuta, mutum zai iya yin bakin ciki, amma idan hakan ya ci gaba da faruwa, zai dace ya nemi taimako.

 KA’IDAR LITTAFI MAI TSARKI: ‘Wanda ya ware kansa, yana gāba da sahihiyar hikima.’​—Misalai 18:1.

 Mataki na B ya fi, don idan ka gaya wa iyayenka ko wani da ya manyanta, za su iya ba ka shawara mai kyau, kuma idan sun taba fuskantar wannan yanayin, za su gaya maka abin da ya taimaka musu.

 Za ka iya ce: ‘Iyayena ba za su iya fahimtar yadda nake ji ba!’ Amma ka tabbata ba su sani ba? Ko da kana ganin abubuwan da iyayenka suka fuskanta sa’ad da suke matasa ba daya ba ne da abubuwan da ka fuskanta, watakila yadda suka ji a dā daya ne da yadda kake ji yanzu, kuma za su iya taimaka maka.

 KA’IDAR LITTAFI MAI TSARKI: “Hikima . . . tana wurin tsofaffi, a cikin tsawon kwanaki kuma fahimi yake.”​—Ayuba 12:12.

 Abin shi ne: Idan ka gaya wa iyayenka ko wani da ya manyanta, zai ba ka shawarar da za ta iya taimaka maka.

Bakin ciki yana kama da wannan unguwa mai hadari. Idan kana so ka fito lafiya, ka nemi taimako

 Idan ciwo ne da kake bukatar ka ga likita fa?

 Idan kana fama da bakin ciki kowace rana, to, ba mamaki kana bukatar ka ga likita ya ba ka magani, don zai iya zama cutar da ake kira, clinical depression ko kuma major depression (ciwon bakin ciki mai tsanani).

 A wasu lokuta, yadda matasa sukan yi bakin ciki saboda canjin yanayin jikinsu yakan yi kama da cutar clinical depression, amma bambancin shi ne bakin cikin da ake yi saboda cutar ya fi tsanani kuma yana dadewa sosai. Saboda haka, idan kana bakin cikin mai tsanani kuma ka dade kana hakan, ka gaya wa iyayenka cewa a kai ka asibiti don a duba lafiyarka.

 KA’IDAR LITTAFI MAI TSARKI: “Lafiyayyu ba su da bukatar mai magani, sai masu ciwo.”​—Matta 9:12.

 Ba abin kunya ba ne idan aka same ka da wannan cutar. Matasa da yawa suna fama da wannan ciwon kuma akwai maganinsa. Abokanka na kirki ba za su guje ka ko su yi maka ba’a don kana yawan bakin ciki ba.

 Taimako: Ka zama mai hakuri. Ba nan tāke ba ne ake samun sauki daga irin wannan cutar, saboda haka, zai dace ka rika tuna cewa a wasu lokuta abubuwa ba za su tafi sumul ba. *

 Matakan da za ka dauka don ka sami sauki

 Ko da irin bakin ciki da kake yi yana bukatar magani ne ko a’a, akwai abubuwan da za su taimaka maka idan kana fama da bakin ciki. Alal misali, motsa jiki, cin abinci mai gina jiki da kuma samun isasshen barci zai taimaka maka. (Mai-Wa’azi 4:6; 1 Timotawus 4:8) Zai yi kyau ka sami wani littafi da za ka rika rubuta yadda kake ji, da abubuwan da kake so ka yi don ka sami sauki, da wadanda ka cim ma, da wadanda ba ka cim ma ba.

 Ko da cuta ne ke jawo maka bakin ciki ko a’a, zai dace ka tuna wannan: Idan ka yarda a taimaka maka kuma ka dauki matakan da ya kamata ka dauka, za ka iya daina bakin ciki.

 Nassosin da za su taimaka maka

  •  “Ubangiji yana kusa da masu karyayyar zuciya, yana ceton irin wadanda suke da ruhu mai tuba.”​—Zabura 34:18.

  •  “Ka zuba nawayarka bisa Ubangiji, shi kuma za ya taimake ka: Ba za ya yarda a jijjige masu adalci ba.”​—Zabura 55:22.

  •  ‘Ni Ubangiji Allahnka zan rike hannun damanka, in ce maka, kada ka ji tsoro, zan taimake ka.’​—Ishaya 41:13.

  •  “Kada . . . ku yi alhini a kan gobe.”​—Matta 6:34.

  •  “Ku bar roke rokenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku.”​—Filibiyawa 4:​6, 7.

^ Idan kana ji kamar kana so ka kashe kanka, ka gaya wa wani da ya manyanta nan da nan. Don karin bayani, ka dubi talifin nan, “Why Go On?” a cikin Awake! na Afrilu 2014.