Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zai Taimaka Maka Ka Rage Kashe Kudi?

Me Zai Taimaka Maka Ka Rage Kashe Kudi?

 Wani mai suna Colin ya ce: “Kwanan nan, na shiga wani babban shago don in yi kallo. Amma da zan fita, sai ga ni na saya abin da ban shirya saya ba.”

 Colin ya yarda cewa yana da matsala wajen kashe kudi. Kai fa? Kana da irin wannan matsalar? Idan e ce amsarka, to wannan talifin zai taimaka maka.

 Me ya sa zai dace ka rage kashe kudi?

 Karya: Idan ka damu da yadda kake kashe kudi, hakan zai takura maka.

 Gaskiya: Idan ka rage kashe kudi za ka fi samun yanci. Littafin nan I’m Broke! The Money Handbook ya ce: “Da zarar ka san za ka sami kudi, abubuwan da kake so yanzu da kuma nan gaba za su karu.”

 Ka yi la’akari da wannan: Idan ka rage kashe kudi . . .

  •   Ba za ka rasa kudi a lokacin da kake bukatarsa ba. Wata matashiya mai suna Inez ta ce: “Wata rana zan so in je Amurka ta kudu.” Ta dada da cewa: “Hakan ya sa duk lokacin da na yi ajiyar kudi, ina tuna da makasudin da na kafa.”

  •   Ba za a rika binka bashi ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai cin bashi kuma bawa ne ga mai ba da bashi.” (Misalai 22:7) Wata mai suna Anna ta ce: “Cin bashi zai iya sa ka tunani, amma idan ba a bin ka bashi, za ka sami kwanciyar hankali.”

  •   Za ka nuna cewa ka manyanta. Matasan da suke kokarin rage kashe kudi yanzu, za su zama mutanen kirki idan suka girma. Wata mai suna Jean ‘yar shakara 20 ta ce: “Idan ina rage kashe kudi yanzu hakan zai taimaka min lokacin da na bar gida. Kuma idan ina rage kashe kudi yanzu, zai zama min da sauki nan gaba.”

 Gaskiyar al’amarin: Littafi nan The Complete Guide to Personal Finance: For Teenagers and College Students ya ce: “Idan kana iya kashe kudi a hanyar da ta dace yanzu, hakan ya nuna cewa za ka iya zaman kanka a nan gaba.” Ya dada da cewa: “Idan ka san yadda za ka kashe kudi, za ka zama da basirar da za ta taimaka maka sosai.”

 Ka san abin da za ka yi

 Ka san kasawarka. Idan a kullum kana cikin rashin kudi, to ya kamata ka san inda kudin suke shiga. Wasu sun ce saye-saye ne a intane yake cinye kudinsu. Wasu kuma sun ce, kafin wata ya kare, sukan kashe kudin kadan-kadan har ya kare tas!

 Wata mai suna Hailey ta ce: “In ka tara kudin da kake kashewa kullum za ka ga cewa kudin yana yawa. A wata, in ka dan ba da kyauta, ka je cin abinci a waje kuma watakila ka saya wani abin da ba ka shirya saya ba, sai ka ga ka kashe dala dari!”

 Ka zama da tsari. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tunanin mai himma zuwa yalwata kadai suke nufa.” (Misalai 21:5) Idan ka tsara abin da za ka kashe kowane wata, hakan zai sa ka kashe daidai kudin da ka tsara maimakon ka kashe fiye da albashinka.

 Wata mai suna Danielle ta ce: “Idan kana kashe kudi fiye da albashinka, zai dace ka san inda kudin yake shiga kuma ka daina sayan abubuwan da ba ka bukata. Sa’an nan ka ci gaba da rage abubuwan har sai albashinka ya fi abin da kake kashewa a wata.”

 Ka bi tsarin da ka kafa. Akwai abubuwa da dama da za ka yi da su taimaka maka ka daina kashe kudi barkatai. Wasu matasa sun fadi abubuwan da suka taimaka musu. Ga abin da suka fada:

  •  Wani mai suna David ya ce: “Abin da nake yi shi ne, ina tura kudina a banki don na san in sun shiga wurin zai yi wuya in taba su.”

  •  Wata mai suna Ellen ta ce: “Idan zan je sayayya, nakan dauki daidai kudin da nake so in kashe. Hakan ya sa ba na kashe kudi fiye da wanda na tsara.”

  •  Wani mai suna Jesiah ya ce: “Idan ban yi saurin sayan abu ba, hakan na sa in san ko ina bukatar abin ko a’a.”

  •  Wata mai suna Jennifer ta ce: “Ba dole ba ne in je kowane biki! Idan ba ni da kudi, ba laifi ba ne in ki zuwa.”

 Gaskiyar al’amarin: Babban hakki ne mutum ya san yadda zai kashe kudi. Colin da muka ambata dazu ya ce: “Idan ina so in zama magidancin kirki a nan gaba, zai dace in daina kashe kudi barkatai!” Ya dada da cewa: “Idan yanzu da nake matashi ban san yadda zan rika amfani da kudina ba, hakan zai rika sa mu sami sabani da matata a nan gaba ina na yi aure.”

Taimako: Wata mai suna Vanessa ta ce: “Za ka iya gaya wa wani game da yadda kake so ka kashe kudinka, kuma ka ce wa mutumin ya rika tambayarka game da yadda kake kashe kudin. Abu mai kyau ne ka zama da wanda za ku rika lissafi tare!”