Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Guji Kasala?

Ta Yaya Zan Guji Kasala?

 Shin kana ganin za ka kasala saboda aiki? To, wannan talifin zai iya taimaka maka!

 Dalilin da ya sa mutane suke kasala

  •   Yawan aiki. Wata mata mai suna Julie ta ce: “A duk fannonin rayuwa ana gaya mana mu rika kyautata rayuwarmu kuma mu kware a ayyukan da muke yi. Ban da haka ma, mu zama da makasudai kuma mu yi kokari mu cim ma su. Yin hakan a kullum zai iya jawo kasala!”

  •   Fasaha. Da yake muna da wayoyi kala-kala kuma a kullum muna dandalin intane, hakan zai sa mu rika gajiya kuma bayan wani lokaci za mu iya kasala.

  •   Rashin barci. Wata mata mai suna Miranda ta ce: “Da yake matasa sukan je makaranta ko aiki ko wajen da ake nishadi, suna tashiwa da sassafe kuma ba sa barci da wuri. Suna hakan a kullum domin ba su da na ta yi. Hakan zai iya sa su kasala.

 Dalilin da ya sa ya zama batu mai muhimmanci

 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana mu rika aiki da kwazo. (Karin Magana 6:6-8.; Romawa 12:11) Amma hakan ba ya nufin cewa mu rika aiki har mu manta da abubuwan da suka fi muhimmanci ba kamar lafiyar jikinmu.

 Wata mai suna Ashley ta ce : “Akwai wata rana da na wuni ban ci kome ba domin na shagala a yin wasu ayyuka da yawa. Yanzu na gane cewa bai kamata in rika karban duk wani aikin da aka ba ni ba domin yin hakan zai hana ni yin abu buwan da suka fi muhimmanci.”

 Wannan dalilin ne ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwama kare mai rai da mataccen zaki.” (Mai-Wa’azi 9:4) Za ka iya takura wa kanka kana aiki don kana ganin cewa kana da karfi irin na zaki, haka ba zai dade ba domin bayan wani lokaci, hakan zai iya shafi lafiyarka.

 Abin da ya kamata ka yi

  •   Kar ka rika karban kowane aiki. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai sauƙin kai mai hikima ne.” (Karin Magana 11:2) Mutanen da suke da saukin kai sun san kasawarsu kuma ba sa karban ayyukan da suka fi karfinsu.

     Wani matashi mai suna Jordan ya ce: “Mutumin da zai rika fama da kasala shi ne wanda yake amincewa da kome da aka ce ya yi ko da bai da lokacin yin su. Hakan ba ya nuna cewa mutumin yana da saukin kai kuma idan ya ci gaba da yin hakan, zai kasala.”

  •   Samun isashen barci. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma kaɗan a hannu ɗaya cike da kwanciyar rai, da mai yawa a hannu biyu cike da famar aiki, wannan ma ƙoƙarin kamun iska ne.” (Mai-Wa’azi 4:6) An ce barci shi ne “abincin kwakwalwa” amma yawancin matasa ba sa yin barcin awa takwas zuwa goma da suke bukatar su yi.

     Wata matashiya mai suna Brooklyn ta ce: “Ba na samun isashen barci idan ina da ayyukan yi da yawa. Amma idan na yi barci da kyau ina yin ayyuka da yawa kuma in rika farin ciki washegari.”

  •   Ka rika tsara ayyukanka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shirye-shirye na mai ƙwazo lallai sukan kai ga yalwata.” (Karin Magana 21:5) Koyan yadda za ka tsara ayyukanka kuma ka yi amfani da lokacinka da kyau zai taimaka maka a rayuwarka.

     Wata mai suna Vanessa ta ce. “Mutum zai iya guje wa kasala idan ya tsara ayyukansa da kyau. Idan ka rubuta abubuwan da ka ke so ka yi, za ka san ayyukan da ya kamata ka yi da wadanda bai kamata ka yi ba kuma hakan zai taimaka maka kada ka kasala.”