Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Abin da ya Kamata in Sani game da Cin Zarafin Al’umma ta Hanyar Jima’i​—Sashe na 1: Abin da za ka yi don ka guji wannan

Abin da ya Kamata in Sani game da Cin Zarafin Al’umma ta Hanyar Jima’i​—Sashe na 1: Abin da za ka yi don ka guji wannan

 Ta yaya ake cin zarafin al’umma ta hanyar jima’i?

 Ko da yake yadda ake yin hakan ya bambanta a wurare dabam-dabam, ana cin zarafin mutane ta jima’i ba da son su ba. A wani lokaci a kan tilasta musu su yi jima’i. Hakan ya ƙunshi yin lalata da yara da jima’i tsakanin dangi da kuma fyaɗe, kuma a yawancin lokaci mutane da aka amince da su ne ke yin haka, kamar likitoci da malamai ko kuma limamai. Ana yi wa wasu mutane da aka wulaƙanta su ko kuma yi jima’i da su barazana cewa idan suka faɗa, wani abu zai same su.

 Wani bincike da aka yi ya nuna cewa a Amirka kaɗai, a kowace shekara ana cin zarafin mutane kusan dubu ɗari biyu da hamsin ta wurin yin lalata da su. Kusan rabinsu suna tsakanin ’yan shekara 12 da 18.

 Abin da ya kamata ka sani

  •   Littafi Mai Tsarki ya haramta cin zarafin mutum ta jima’i. Littafi Mai Tsarki ya ambata taron ’yan iska da suka nemi su yi wa maza biyu fyaɗe da suka ziyarci birnin Saduma kusan shekaru 4,000 da suka shige. Don wannan ne Jehobah ya halaka birnin. (Farawa 19:4-13) Ƙari ga haka, a Dokar da aka ba Musa shekaru 3,500 da suka wuce, an haramta jima’i tsakanin dangi, har da cin zarafin wani memban iyali ta jima’i.—Levitikus 18:6.

  •   A yawancin lokaci wanda mutum ya sani ne yake cin zarafinsa ta jima’i. Littafin nan Talking Sex With Your Kids ya ce: “A cikin fyaɗe biyu cikin uku da aka yi, mutumin ya san wanda ya yi masa fyaɗe. Ba wani baƙo ba ne da ya fito haka kawai.”

  •   Ana cin zarafin maza da mata. A Amirka, maza sun kai misalin kashi goma cikin ɗari da ake cin zarafinsu ta jima’i da su. Ƙungiyar Rape, Abuse & Incest National Network, ta ce “maza da aka ci zarafinsu suna iya yin fargaba cewa hakan zai sa su zama ’yan daudu ko kuma su riƙa ganin cewa su ba maza ba ne.”

  •   Cin zarafin mutane ta jima’i ba abin mamaki ba ne. Littafi Mai Tsarki ya ce a cikin “kwanaki na ƙarshe” mutane da yawa za su zama “marasa-ƙauna irin na tabi’a” da “masu-zafin hali” da kuma “marasa-kamewa.” (2 Timotawus 3:1-3) Waɗanda suke ƙoƙari su ci zarafin wasu ta jima’i suna nuna irin waɗannan halayen.

  •   Ba laifin wanda aka ci zarafinsa ba ne. Ba wanda ya dace a ci zarafinsa ta jima’i. Wanda ya ci zarafin wani ne yake da laifi. Duk da haka, ya kamata ka ɗauki wasu matakai don ka hana hakan faruwa.

 Abin da za ka yi

  •   Ka kasance a shirye. Ka yi tunanin abin da za ka yi tun da wuri idan wani ko wanda kike fita zance da shi ko dangi ya yi ƙoƙari ya tilasta miki yin jima’i. Wata budurwa mai suna Erin ta ba da shawara cewa don ka kasance a shirye ga kowane irin yanayi na matsi na tsara, kana iya yin kwaikwaiyo wasu yanayi da hakan zai iya faruwa kuma ka yi tunanin abin da za ka yi. Ta ce: “Hakan zai iya zama kamar tsohon yayi, amma zai iya sa ba za a ci zarafinki ba ta jima’i.”

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku duba fa a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; ... tun da yake miyagun kwanaki ne.”—Afisawa 5:15, 16.

     Ka tambayi kanka: ‘Mene ne zan yi idan wani ya taɓa ni a hanyar da ta sa na ji wani iri?’

  •   Ka yi tunanin hanyar da za ka fita. Ƙungiyar Rape, Abuse & Incest National Network ta ce, “ka shirya wata kalmar da abokanka ko kuma iyalinka kaɗai suka sani don ka kira su kuma ka yi magana da su idan ba ka saki jiki a wurin da kake domin kada mutumin ya san cewa kana shirin ficewa. Abokanka ko kuma iyalinka za su zo su tafi da kai ko kuma su ba mutumin wata hujja da zai sa ka bar wajen.” Ba za ka yi baƙin ciki ba ta wajen guje wa irin wannan yanayin da zai sa ka cikin matsala.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai-hankali ya kan hangi masifa, ya ɓuya: Amma wawaye sukan bi ciki, su sha wuya.”—Misalai 22:3.

     Ka tambayi kanka: ‘Wace mafita ce nake da ita?’

    A kowane lokaci ka kasance da mafita

  •   Ka kafa iyaka kuma ka riƙa bin sa. Alal misali, idan kina fita zance da wani, ya kamata ku tattauna irin soyayya da ta dace ku riƙa yi da wadda ba dace ba. Idan abokinki yana ganin hakan bai dace ba, to ki nemi wani wanda zai daraja ra’ayinki.

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙauna ... ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta.”—1 Korintiyawa 13:4, 5.

     Ka tambayi kanka: ‘Mene ne nake so? Wane irin hali ne bai dace ba?’