Koma ka ga abin da ke ciki

Na Ki Jinin Makaranta

Na Ki Jinin Makaranta

Ga abin da kake bukata

 Kasancewa da ra’ayi mai kyau game da koyo. Ka ga abin da ke kunshe ciki. Ba dukan abin da ke cikin tsarin ilimi ke da muhimmanci ba—akalla ba yanzu ba. Duk da haka, samun ilimi a kan abubuwa dabam-dabam zai kyautata fahiminka. Zai taimake ka ka “zama dukan abu ga dukan mutane,” kuma ka kasance da fasahar tattaunawa da mutane daga wurare dabam-dabam. (1 Korintiyawa 9:22) Balle ma, za ka kyautata fahimtar ka—kuma hakan zai taimake ka a nan gaba.

Kammala makaranta yana kama da sare itatuwa a kurmi don ka iya bi, ma’ana, sai idan kana da kayan aiki masu kyau za ka iya cim ma burinka

 Ka kasance da ra’ayi mai kyau game da malaminka. Idan kana jin cewa ba ka son malaminka, ka mai da hankali ga abin da yake koyarwa, ba malamin ba. Ka tuna cewa, malamin nan ya koyar da darussan nan ba sau daya ba amma sau da dama ga wasu ajujuwan. Saboda haka, zai iya kasancewa da wuya ya ci gaba da kasancewa da irin himmar da yake da ita a lokacin da ya fara koyar da darassin.

 Abin taimako: Ka yi rubutu, cikin ladabi ka yi tambaya a kan abin da ba ka gane ba, kuma ka rika sha’awar abin da ake koyarwa. Idan ka yi hakan, hakan zai shafi wasu.

 Ka kasance da ra’ayin da ya dace game da iyawarka. Makaranta za ta iya bayyana baiwar da ba ka san cewa kana da ita ba. Bulus ya rubuta wa Timotawus: “Ka rura baikon Allah, wanda ke cikinka.” (2 Timotawus 1:6) Hakika, Timotawus yana da “baiko” ko kuma baiwa da ya samu ta hanyar ruhu mai tsarki. Amma yana bukatar ya gina baiwar nan don kada ya zama matacce. Babu shakka, ilimin da kake da shi a makaranta ba Allah ne ya saukar maka da shi ba. Duk da haka, baiwar da kake da ita taka ce kawai. Makaranta za ta iya taimaka maka ka san baiwarka kuma ka kyautata iyawarka da ba ka san cewa kana da su ba dā.