Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Zai Dace In Sulhunta da ’Yan’uwana?

Me Ya Sa Zai Dace In Sulhunta da ’Yan’uwana?

 “Abokai masu ban haushi”

 Wasu sukan ce, ’yan’uwa “abokai ne masu ban haushi.” Ma’ana, kana kaunarsu kuma su ma suna kaunarka amma a yawancin lokuta kuna fada. Wata ’yar shekara 18 mai suna Helena ta ce, “Kanina yana yawan ba ni haushi, ya san abin da zai yi da zai bata min rai sosai.”

 Yana yiwuwa a sasanta matsalolin da sukan taso tsakanin ’yan’uwa ta wurin tattaunawa kawai. Alal misali:

  •   Yaya da kani da suke zaune a daki daya za su iya yin fada domin wani yana tsoma baki a sha’anin da bai shafe shi ba. Me ya kamata su yi? Ya kamata su guji nacewa a kan ra’ayinsu kuma su daina shisshigi a batun da bai shafe su ba. Kari ga haka, su bi ka’idar da ke cikin littafin Luka 6:31.

  •   ’Yan’uwa mata biyu za su iya yin “aron” rigunan juna ba tare da neman izinin mai shi ba. Me ya kamata su yi? Ya kamata su tattauna batun da kyau don su san yadda za su rika taba kayan juna kuma su bi ka’idar da ke littafin 2 Timotawus 2:24.

 A wasu lokuta, matsalolin da suke tasowa tsakanin ’yan’uwa suna iya zama da tsanani har su haifar da munanan sakamako. Ga misalai biyu daga Littafi Mai Tsarki:

  •   Maryamu da Haruna sun yi kishin Musa kuma hakan ya jawo musu mummunan sakamako. Ka karanta labarin a Littafin Lissafi 12:1-15. Sa’an nan, ka tambayi kanka: ‘Me zai taimaka min don kada in yi kishin ’yar’uwata ko dan’uwana?’

  •   Kayinu ya ji haushin dan’uwansa Habila har ya kashe shi. Ka karanta labarin a littafin Farawa 4:1-12. Sa’an nan, ka tambayi kanka: ‘Me zai taimaka mini in bi da ’yan’uwana cikin hakuri?’

 Dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta

 Akwai dalilai biyu da suka sa ya kamata ku sulhunta da ’yan’uwanku, ko da yin hakan bai da sauki.

  1.   Hakan zai nuna cewa kun yi girma. Wani mai suna Alex ya ce, “Ina saurin fushi da kannena biyu mata. Amma yanzu na girma shi ya sa ina yawan hakuri da abubuwan da suke yi min.”

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum mai kamewa yana da hikima, amma mai zafin rai yana bayyana wautarsa a fili.”—Misalai 14:29, Littafi Mai Tsarki.

  2.   Hakan zai taimaka muku nan gaba. Idan kuna iya sulhuntawa da ’yan’uwanku a yanzu, a nan gaba zai zama muku da sauki ku sulhunta da abokin aurenku ko abokan aikinku ko ma wasu dabam.

     Gaskiyar lamarin: A gida ne mutum zai iya koyan yadda zai kulla dangantaka mai kyau da mutane kuma hakan zai taimaka masa daga baya in ya girma.

 Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Idan zai yiwu, ku zauna lafiya da dukan mutane.’—Romawa 12:18.

 Idan kuna neman abin da zai taimaka muku ku warware matsaloli tsakaninku da ’yan’uwanku, ku bincika “Abin da tsararku suka ce” da kuma shafin rubutun nan: “Ta Yaya Zan Zauna Lafiya da ’Yan’uwana?”