Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Zai Taimaka Min In Rika Motsa Jiki?

Me Zai Taimaka Min In Rika Motsa Jiki?

 Me ya sa zan rika motsa jiki?

 A wasu kasashe, matasa ba sa motsa jiki, kuma hakan yana sa lafiyar jiki cikin hadari. Don haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Horon jiki yana da dan amfani.” (1 Timoti 4:8) Ka yi la’akari da wannan:

  •   Motsa jiki zai iya sa ka farin ciki. Motsa jiki zai taimaka wa kwakwalwarka ta fitar da sinadarin da ake kira endorphin wanda yake sa mutum farin ciki da kuma wartsakewa. Wasu suka ce motsa jiki ita ce maganin da jikin mutum ke bukata.

     Wata mai suna Regina ta ce: “Idan na fita yin gudu da safe, hakan yana kara mini lafiyar jiki kuma yana sa ni farin ciki.”

  •   Motsa jiki yana sa siffar jikinmu ta yi kyau. Motsa jiki daidai yadda ya kamata zai sa mu kasance da karfin jiki da kuma siffa mai kyau. Hakan zai taimaka mana mu kasance da karfin zuciya.

     Wata mai suna Olivia ta ce: “Ina farin ciki cewa a yanzu ina iya yin irin motsa jiki da nake yi sau goma, a shekarar da ta shige ko guda daya ba na iya yi! Kuma abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa ina kula da lafiyata.”

  •   Motsa jiki zai kara tsawon rayuwarka. Motsa jiki zai taimaki lafiyar zuciyarka da kuma inganta yadda kake numfashi. Kari ga haka, motsa jiki zai taimaka maka ka guji kamuwa da ciwon zuciya wanda yake kashe maza da mata da yawa.

     Wata mai suna Jessica ta ce: “Idan muna motsa jiki a kai a kai, hakan zai nuna cewa muna godiya domin jikin da Allah ya ba mu.”

 Gaskiyar al’amarin: Motsa jiki zai sa ka kasance da koshin lafiya a nan gaba, kuma za ka iya amfana a yanzu. Wata matashiya mai suna Tonya ta ce: “Ba za ka taba cewa da-na-sani da ban je hawan dutse ko gudu ba. A duk lokacin da na kokarta don in motsa jiki ina farin ciki.”

Da shigewar lokaci, motar da ba a kula da ita za ta daina aiki, haka yake da jikinka idan ba ka motsa jiki

 Me ke hana ni motsa jiki?

 Akwai abubuwa da yawa da za su iya hana ka motsa jiki kamar su:

  •   Rashin abin da ke karfafa ka. Wata mai suna Sophia ta ce: “Mutane suna ganin cewa ba su da matsala sa’ad da suke matasa. Yana da wuya mutum ya yi tunanin lokacin da zai soma rashin lafiya. Yana ganin cewa tsofaffi ne suke rashin lafiya.”

  •   Rashin lokaci. Wata mai suna Clarissa ta ce: “Duk da cewa na shagala da aiki ina samun lokacin cin abinci mai kyau da kuma barci, amma samun lokacin motsa jiki yana yi mini wuya sosai.”

  •   Ba ka yi rajista a gidan motsa jiki ba. Wata mai suna Gina ta ce: “Mutum yana bukatar ya kashe kudi don ya kasance da koshin lafiya, kana bukatar ka biya kudi don ka yi rajista a gidan motsa jiki!”

 Ka yi tunani a kan wannan:

 Mene ne ya fi hana ka motsa jiki? Kana bukatar yin aiki tukuru don ka shawo kan wannan matsalar. Amma idan ka yi hakan, za ka amfana sosai.

 Ta yaya zan motsa jiki daidai yadda nake so?

 Ga wasu shawarwari:

  •   Kai za ka dauki matakan da za su taimaka maka ka kasance da koshin lafiya.​—Galatiyawa 6:5.

  •   Ka guji ba da hujjojin kin motsa jiki. (Mai-Wa’azi 11:4) Alal misali, ba ka bukatar ka yi rajista a gidan motsa jiki kafin ka yi hakan. Ka nemi motsa jikin da za ka rika yi da kake jin dadin yi.

  •   Don ka san abin da za ka yi, ka tambayi wasu abin da suke yi don motsa jiki.​—Karin Magana 20:18.

  •   Ka kasance da tsari. Ka kafa makasudai kuma ka rika rubuta ci gaba da kake samu don hakan zai karfafa ka sosai.​—Karin Magana 21:5.

  •   Ka nemi wanda za ku rika motsa jiki tare. Idan kana da abokin da za ku rika motsa jiki tare, hakan zai taimaka maka ka ci gaba da bin tsarin da ka kafa.​—Mai-Wa’azi 4:​9, 10.

  •   A wasu lokuta za ka karaya, idan hakan ya faru, kada ka daina motsa jiki ka yi iya kokarinka don ka ci gaba da yin hakan.​—Karin Magana 24:10.

 Kada ka wuce gona da iri

 Littafi Mai Tsarki ya karfafa maza da mata kada su rika yin abu fiye da kima. (1 Timoti 3:​2, 11) Don haka, kada ka wuce gona da iri a motsa jikinka. Mutanen da ke yin hakan sukan ji wa kansu rauni. Wata matashiya mai suna Julia ta ce: “Bana sha’awar namijin da ya fi mai da hankali ga siffar jikinsa, fiye da samun ilimi.”

 Kari ga haka, ka guji shawarar da mutane ke bayarwa da zai sa ka motsa jiki fiye da kima. Irin wadannan shawarwarin za iya sa ka ji rauni kuma su sa ka kasa mai da hankali ga “abin da ya fi kyau” a rayuwa.​—Filibiyawa 1:10.

 Kari ga haka, abubuwan da mutane ke fada don su karfafa ka ka motsa jiki suna iya sa ka yi sanyin gwiwa. Wata matashiya mai suna Vera ta ce: “’Yan mata da yawa suna ajiye hotunan mutanen da suke so su zama kamar su domin su rika kallon hoton a duk lokacin da suka karaya. A karshe, suna gwada kansu da wadannan mutanen kuma hakan yana iya sa su karaya. Ya fi kyau mu kafa makasudin kasancewa lafiyar jiki ba siffar jikinmu kadai ba.”