Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Abin da Ya Kamata in Sani Game da Tura Hotuna Zuwa Dandalin Yada Zumunta

Abin da Ya Kamata in Sani Game da Tura Hotuna Zuwa Dandalin Yada Zumunta

 Kana son abokanka su san cewa ka ji dadin hutun da ka je! Amma ta yaya za su sani? Shin za ka tura wa

  1.   kowannensu sako ne?

  2.   ko za ka rubuta wa duka abokanka imel?

  3.   ko kuma za ka tura hotunan zuwa dandalin yada zumunta?

 Watakila a lokacin da kakaninka suke matasa, shawara ta “A” ce kadai abin da ake yi.

 Mai yiwuwa a lokacin da iyayenka suke yara ana bin shawara ta “B.”

 A yau matasa da yawa da iyayensu suka yarda su rika tura hotunansu zuwa dandalin yada zumunta suna son yin amfani da shawara ta “C.” Kai kuma fa? Idan kai ma kana son tura hotonka, wannan talifin zai taimaka maka ka guje wa wasu matsaloli.

 Ta yaya za ka amfana?

 Ba a bata lokaci. Melanie ta ce: “A duk lokacin da na yi tafiya ko kuma muka yi wani abu da abokaina, ina tura hotunan nan da nan sa’ad da nake farin ciki game da tafiyar da na yi.”

 Ya fi sauki. Jordan ya ce: “Kalon hotunan da abokaina suka tura a dandalin yada zumunta don in san ko suna nan lafiya ya fi tura musu sakon imel.”

 Yana taimakawa wajen sanin abin da abokanka suke yi. Karen ta ce. “Wasu abokaina da kuma iyalinmu suna zama da nisa. Idan na ga hotunan da suka tura zuwa dandalin yada zumunta yana sa in ji kamar muna tare!”

 Mene ne hadarin?

 Za ka iya sa kanka a cikin hadari. Idan kamaranka yana da abin da yake bayyana wurin da ka dauki hoton, hakan zai iya nuna wa mutane wurin da kake kuma watakila ba ka son hakan. Wani rahoto da Digital Trends ta ba da ya ce: “Tura hoto ko kuma wasu abubuwan da za su nuna inda kake a dandalin yada zumunta zai iya ba wa mugaye damar sanin wurin da kake don su maka illa.”

 Babu shakka, wasu barayi suna son su san inda kake shiga da fita. Digital Trends ta sake ba da rahoto cewa, barayi uku sun shiga gidaje 18 a lokacin da babu kowa a ciki. Amma ta yaya suka san cewa babu kowa a gidajen? Sun je dandalin yada zumunta kuma suka binciko shiga da fitar mutanen, sun saci abubuwan da suka fi dala 100,000.

 Za ka iya ganin abubuwan da ba su dace ba. Wasu mutane ba su da kunya tura abin da bai dace ba zuwa dandalin yada zumunta don kowa ya gani. Wata matashiya mai suna Sarah ta ce: “Za ka iya shiga wahala ko kuma ganin abin da bai dace ba idan ka fara kallon hotunan mutanen da ba ka san su ba. Yana kamar yin tafiya a cikin birnin da ba ka taba zuwa ba babu ja-gora.”

 Za ka bata lokacinka. Yolanda ta ce: “Ba shi da wuya mutum ya rika bata lokaci wurin kallon abin da wasu suka tura da kuma irin kalaman da mutane suke yi, a wasu lokuta za ka iya ma soma duba wayarka kowane sakan don ganin abin da wasu suka saka.”

Kana bukata ka rika kame kanka idan kana da shafin yada zumunta

 Wata matashiya mai suna Samantha ta yarda da hakan, ta ce: “Na rage lokacin da nake yi a dandalin yada zumunta, ban da haka ma, mutum yana bukatar ya rika kame kansa sosai idan yana dandalin yada zumunta.”

 Abin da za ka iya yi

  •   Ka kudiri aniyar cewa ba za kalli abin da bai dace ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ba zan sa wani mummunan al’amari a gaban idanuna ba.”​—Zabura 101:3.

     Steven ya ce: “Nakan duba abin da abokaina a dandalin suke turawa a kai a kai kuma idan na ga cewa abin da suke tura wa bai dace ba, sai in daina abokantaka da su a dandalin.”

  •   Ka daina tarayya da mutanen da ba su san muhimmancin bin ka’idodin Jehobah ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu takan ɓata halaye na kirki.”​—1 Korintiyawa 15:33.

     Jessica ta ce: “Kada ka rika kallon hotunan don mutane da yawa suna son su. A yawanci lokaci ta haka ne mutane suke ganin abubuwan da ba su dace ba kamar su batsa da dai sauransu.”

  •   Ka tsara lokacin da za kana shiga intane da kuma yadda za kana tura hotunanka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku duba fa a hankali yadda kuke yin tafiya, ba kamar marasa-hikima ba, amma kamar masu-hikima; kuna rifta zarafi.”​—Afisawa 5:​15, 16.

     Rebekah ta ce: “Na daina abokantaka da mutanen da suke ‘tura hotuna sosai.’ Alal misali, wani zai iya zuwa kogi yin iyo kuma bayan hakan sai ya tura hotuna guda 20 iri daya. Kuma kallon dukan wadannan hotunan zai dau lokaci.”

  •   Ka mai da hankali don kada hotunan da kake tura ya nuna cewa ka fi damuwa da kanka ne kawai. Bulus wanda ya rubuta wasu littattafai a Littafi Mai Tsarki ya ce: “Nake fāɗa wa kowane mutum wanda ke cikinku, kada shi aza kansa gaba da inda ya kamata.” (Romawa 12:3) Kada ka rika yin tunanin cewa duk hotunan abubuwan da kake yi ne abokanka za su so.

     Allison ta ce: “Wasu mutane suna tura hotuna da yawa wadanda suka dauki kansu. Idan kai abokina ne na san kamaninka, ba ka bukatar ka rika tura hotunan da ka dauki kanka!”