Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Ya Dace In Nemi Gafara?

Me Ya Sa Ya Dace In Nemi Gafara?

 Me za ka yi idan ka sami kanka a daya daga cikin yanayoyi da ke gaba?

  1.   Malaminka ya yi maka horo domin ka yi abin da bai dace ba a aji.

     Za ka ba malaminka hakuri ko da kana ganin ya dau batun da zafi sosai?

  2.   Kawarki ta ji cewa kin yi gulmarta.

     Za ki ba wa kawarki hakuri duk da cewa kina ganin abin da kika fada gaskiya ne?

  3.   Ka yi fushi da mahaifinka kuma ka yi masa bakar magana.

     Za ka ba wa mahaifinka hakuri duk da cewa kana ganin shi ne ya jawo matsalar?

 Amsoshin duka tambayoyin e ce. Amma me ya sa ya kamata ka nemi gafara duk da cewa kana ganin kana da hujjar yin abin da ka yi?

 Me ya sa ya dace ka nemi gafara?

  •   Neman gafara zai nuna cewa ka manyanta. Idan kana amincewa da kurakuren da ka yi kuma ka nemi gafara, hakan zai nuna cewa kana koyan halaye masu kyau da za su taimaka sa’ad da ka yi girma.

     Wata mai suna Rachel ta ce: “Saukin kai da hakuri za su taimaka mana mu nemi gafarar wanda muka yi masa laifi kuma mu saurari shi sa’ad da yake magana.”

  •   Neman gafara zai sa ka sasanta da mutane. Mutanen da suke neman gafara suna nuna cewa sun fi son zaman lafiya maimakon nuna cewa ba su da laifi.

     Wata mai suna Miriam ta ce: “Ko da kana ganin ba kai ne da laifi ba, ya kamata ka yi kokari ka sasanta matsalar. Neman gafara ba wani abu mai wuya ba ne, amma zai iya kyautata dangantakar da ke tsakanin mutane.”

  •   Neman gafara zai kwantar maka da hankali. Idan ka yi ko ka fadi wani abin da ya bata wa mutum rai, hakan zai iya damun ka daga baya. Amma idan ka nemi gafara, zuciyarka za ta kwanta. *

     Wata mai suna Nia ta ce: “Akwai wasu lokuta da na yi wa iyayena rashin kunya. Abin ya dame ni daga baya, amma ya yi min wuya in nemi gafararsu. Amma da na yi hakan, hankalina ya kwanta domin hakan ya kawo zaman lafiya tsakaninmu.”

    Yin da-na-sani yana kama da daukan kaya mai nauyi, amma idan ka nemi gafara, hankalinka zai kwanta

 Yana da sauki mutum ya nemi gafara? A’a! Wata matashiya mai suna Dena da ta nemi gafarar mahaifiyarta sau da yawa domin ta yi mata bakar magana ta ce: “Neman gafara bai da sauki. Nakan ji kamar wani abu ya shake wuyata kuma yana hana ni yin magana!”

 Yadda za ka ba da hakuri

  •   Idan zai yiwu, ka je ka sami mutumin ka ba shi hakuri. Idan ka je ka sami mutumin, hakan zai nuna masa cewa da gaske kake neman gafararsa. Amma idan ka ba da hakuri ta sakon tes, mai yiwuwa mutumin ba zai amince da kai. Ko da ka yi amfani da zanen alamun yanayin mutum (emoji) da ke nuna bakin ciki, mutumin zai iya dauka cewa ba da gaske kake ba.

     Shawara: Idan ba za ka iya zuwa ka sami mutumin ba, ka kira shi ta waya ko kuma ka rubuta masa wasika da hannunka. Ko da wace hanya ce kake so ka bi, ka yi amfani da kalmomin da suka dace.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Zuciyar mai adalci takan yi tunani kafin ta ba da amsa.”​—Karin Magana 15:28.

  •   Kada ka bata lokaci kafin ka nemi gafara. Idan ka dau lokaci kafin ka nemi gafara, matsalar za ta kara muni kuma dangantakarka da mutumin za ta dada lalacewa.

     Shawara: Ka kafa makasudi cewa za ka nemi gafara yau. Ka yi tunanin lokacin da zai fi dacewa ka yi hakan kuma ka yi shi.

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Ka yi sauri ka shirya da shi.”​—Matiyu 5:25.

  •   Ka yi amfani da kalmomin da za su nuna cewa da gaske kake. Kada ka ce: “Ka yi hakuri idan kana ganin na yi maka laifi.” Hakan ba neman gafara ba ne. Wata mai suna Janelle ta ce: “Idan wanda ka yi masa laifi ya ga cewa ka amince da kuskurenka kuma ka nemi gafararsa, zai daraja ka.”

     Shawara: Kada ka ba da sharadi kafin ka nemi gafararsa. “Kada ka ce sai ya ba ni hakuri kafin in ba shi hakuri.”

     Ka’idar Littafi Mai Tsarki: “Bari mu yi iyakacin kokarinmu don mu aikata abin da zai kawo salama.”​—Romawa 14:19.

^ Idan ka batar ko ka lalata abin wani, zai dace bayan ka nemi gafara, ka gaya masa cewa za ka biya abin.