Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Me Ya Sa Koyan Wani Yare Yake da Muhimmanci?

Me Ya Sa Koyan Wani Yare Yake da Muhimmanci?

 Koyan wani yare zai iya sa ka horar da kanka kuma ka zama mai tawali’u. Amma yin hakan yana da wani amfani kuwa? Matasa da yawa za su ce e! A wannan talifin, za a tattauna dalilin da ya sa suke yin hakan.

 Me ya sa ake koyan wani yare?

 Wasu suna koyan wani yare don an bukace su yi hakan a makaranta ne. Wasu kuma suna da ra’ayinsu dabam. Alal misali:

  •   Wata matashiya mai suna Anna da ke zama a Ostereliya ta tsai da shawarar koyan yaren mahaifiyarta, wato yaren Latvia. Ta ce: “Iyalinmu suna shirin zuwa Latvia kuma zan so in yi hira da danginmu a yarensu shi ya sa nake son in koyi yaren.”

  •   Wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Gina da ke Amirka ta koyi Yaren Kurame na Amirka kuma ta kaura zuwa Belize don ta yi wa’azi. Ta ce: “Mutanen da suke yin yaren kurame ba su da yawa, don haka, ba sa samun mutane da yawa da za su yi hira da su. Kuma mutane suna mamaki sa’ad da na gaya musu cewa na koyi yaren kurame ne don in koya wa kurame Littafi Mai Tsarki!”

 Ka sani? Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi wa’azin Mulkin Allah ga “kabila da harshe da al’umma.” (Ru’ya ta Yohanna 14:6) Don su cika wannan annabcin, matasa da yawa da Shaidun Jehobah ne sun koyi wasu harsuna don su yi wa’azi a kasarsu ko kuma su kaura zuwa wata kasa don yin hakan.

 Wadanne kalubale ake fuskanta?

 Koyan wani yare bai da sauki sam. Wata matashiya mai suna Corrina ta ce: “Na aza koyan sabbin kalmomi ne kawai, amma na gano cewa ya kunshi koyan al’adar mutanen ne da yadda suke tunani. Kuma koyan wani yare yana daukan lokaci sosai.”

 Kuma hakan yana bukatar tawali’u. Wani matashi mai suna James da ya koyi Sifanisanci ya ce: “Kana bukatar ka mai da batun abin dariya domin za ka yi kurakurai da dama a lokacin da kake koyon wani yare. Kuma idan ka ci gaba da hakan, za ka koyi yaren.”

 Gaskiyar al’amarin: Idan za ka iya jimre da kalubalen koyan yare har ma da lokacin da ka yi babban kuskure, to za ka iya yin nasara a koyan yaren.

 Shawara: Kada ka yi sanyin gwiwa idan wasu suka iya yaren da sauri fiye da kai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bari kowane mutum shi auna nasa aiki, sa’annan za ya sami fahariyarsa bisa ga zancen kansa kaɗai, ba ga zancen wani ba.”​—Galatiyawa 6:4.

 Wace albarka ake samu don yin hakan?

 Albarkar koyan wani yare suna da yawa. Alal misali, wata matashiya mai suna Olivia ta ce: “Idan ka koyi wani yare, za ka sami abokai da yawa.”

 Wata matashiya kuma mai suna Mary ta gano cewa koyan sabon yare yana sa ta zama mai gaba gadi. Ta ce: “Ba na ganin ina yin abubuwan da suka dace, amma yanzu da nake koyon wani yare ina jin dadi a duk lokacin da na koyi wata kalma. Kuma yanzu ina farin ciki sosai.”

 Gina da aka ambata dazu ta ce koya wa mutane Littafi Mai Tsarki a yaren kurame ya sa tana jin dadin hidimar da take yi. Ta ce: “Ganin yadda mutane suke farin ciki a lokacin da nake yin yarensu albarka ce babba!

 Gaskiyar al’amarin: Koyan wani yare zai taimaka maka ka sami sabbin abokai, ka kasance da gaba gadi, kuma ka ji dadin hidimarka. Ban da haka ma, hanya ce mai muhimmanci na yi wa “dukan kabilai da al’ummai da harsuna” wa’azi.​—Ru’ya ta Yohanna 7:9.