Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Daina Yin Shiririta?

Ta Yaya Zan Daina Yin Shiririta?

Kana yawan gajiya ne da ayyukan gida da na makaranta? Idan haka ne, kana bukatar ka daina yin shiririta! Wannan talifin zai taimake ka ka daina yin shiririta, ko da

Bayan ka karanta wannan talifin,  sai ka yi aikin nan na wasa kwakwalwa.

 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa yin shiririta zai kawo mummunar sakamako. Ya ce: “Shi wanda ya lura da iska ba za ya shuka ba: kuma wanda ya kula da gizagizai ba za ya yi girbi ba.”​—Mai-Wa’azi 11:4.

 Ka yi la’akari da wasu abubuwan da za su iya sa ka yi shiririta da kuma abin da za ka iya yi don ka daina yin hakan.

 Idan aikin ya fi karfinka.

 Gaskiyar ita ce, wasu ayyuka suna da wuya shi ya sa yana da sauki a yi banza da su. Ga wasu shawarwari masu kyau.

  •   Ka rarraba ayyukan kadan kadan. Wata yarinya mai suna Melissa ta ce: “Ko da na makara, nakan yi kokarin gama ayyukana ta wajen yin su bi da bi.”

  •   Ka soma aikin ba tare da bata lokaci ba. Vera ta ce: “Ka fara aikin da zarar an ba ka, ko da hakan yana nufin ka sa shi a rubuce, ko kuma ka rubuta yadda za ka yi aikin a cikin tsarin ayyukanka kafin ka manta.”

  •   Ka nemi shawara daga wurin wasu. Watakila iyayenka da malamanka sun taba fuskantar irin wannan matsalar. Za ka iya amfana daga misalinsu. Za su iya taimakonka ka tsara yadda za ka cim ma aikin.

 Taimako Abbey ta ce: “Ka tsara yadda za ka cim ma aikinka. Hakika, hakan yana nufin ka tsara aikinka kuma ka bi tsarin, za ka cim ma burinka kuma ka gama ayyukanka a kan lokaci.”

 Kai dai ba ka son yin aikin ne.

 A yawancin lokaci, ayyukan da za ka yi sun kunshi abubuwan da ba ka son yi. To, me za ka yi idan ba ka jin dadin aikin? Ka gwada wadannan.

  •   Ka yi tunanin amfanin yin aikin da wuri. Alal misali, ka yi tunanin irin dadin da za ka ji idan ka kammala aikin. Wata yarinya mai suna Amy ta ce: “Ina jin dadi sosai idan na gama aikin da ya kamata na yi a kan lokaci ko kuma kafin lokacin don hakan zai sa hankalina ya kwanta.”

  •   Ka tuna da sakamakon yin shiririta. Idan ka bata lokaci, za ka dada wa kanka ciwon kai kuma da kyar ka yi nasara. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.”​—Galatiyawa 6:​7.

  •   Ka sa ranar da za ka kammala aikin kusa kafin ainihin ranar. Wata yarinya mai suna Alicia ta ce: “Hakan zai sa na dauka cewa ranar kammala aikin ya kai, alhali saura kwana daya ko biyu. Da yake ina da sauran lokaci, hakan zai ba ni damar sake duba aiki.”

 Taimako Alexis ta ce: “Za ka iya iza kanka. Ka yi iyakacin kokarinka babu abin da zai hana ka. Sa’ad da na dage, ba abin da zai hana.”

 Ka takure da aikace-aikace.

 “Mutane suna ce da ni mai shiririta,” in ji wani yaro mai suna Nathan, “amma bai dace ba! Ba su san yadda na takure da aiki ba!” Idan ka ji yadda Nathan ya ji, ka gwada wadannan taimako.

  •   Ka soma da mafi sauki. “Wani ya taba gaya mini cewa idan aiki ba zai kai minti biyar ba a gama shi, yi shi nan da nan,” in ji wata yarinya mai suna Amber. “Wannan ya kunshi ayyuka irinsu shara, shirya riguna, wanke kwanoni, da kuma yin waya.”

  •   Ka jera su bisa muhimmancinsu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwada mafifitan al’amura.” (Filibbiyawa 1:10) Ta yaya za ka yi amfani da wannan a rayuwarka ta yau da kullum? “Nakan jera dukan ayyuka da nake da su bisa kwanan wata,” in ji yarinya mai suna Anna. “Mafi muhimmanci ma, nakan rubuta lokacin da zan yi aikin kuma na gama kowannensu.”

 Wannan yana da wuya ne? To sake dubawa! Batun shi ne, idan ka tsara ayyuka, za ka iya gama a kan shirya lokaci maimakon ka makara. Wannan ba zai sa ka gaji ba. “Shirya abubuwa yana taimaka mini na sami kwanciyar hankali na bi da su daidai,” in ji yarinya mai suna Kelly.

  •   Guje wa abubuwan raba hankali. “Nakan gaya wa kowa a gidanmu zan soma aikina,” in ji Jennifer. “Idan akwai abin da suke son na yi nakan ce su gaya mini na gama shi kafin na soma nawa aikin. Nakan kashe wayana da kuma karar shigowar i-mel di na.”

 Taimako Jordan ya ce: “Duk abin da kake da shi na yi, ka yi shi ka huta. Maimakon ka bar aiki yana jiranka, ka gama shi ka huta. Ta haka ne za ka huta.”.