Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?

Ta Yaya Zan Iya Mai da Hankali Sosai ga Abin da Nake Yi?

 Me ke raba hankalina?

 Wata mai suna Elaine ta ce: “A dā, nakan karanta littattafai da dama amma yanzu yana min wuya in yi hakan. Ko da sakin layi daya ne, idan ya yi tsawo, ba na so in karanta shi.”

 Miranda kuma ta ce: “Nakan kara saurin bidiyon da nake kallo idan na ga kamar yana bata min lokaci.”

 Jane ta ce: “Ko da abu mai muhimmanci ne nake yi, idan wayata ta yi kara, nan da nan sai in soma tunani, ‘Wa ya tura min sako?’ ”

 Shin, na’urorin zamani za su iya hana mutum natsuwa? Wasu sun ce kwarai kuwa. Wani marubuci mai ba da shawara mai suna Nicholas Carr ya ce: “Idan muna amfani da intane da yawa, hakan zai sa hankalinmu ya rika saurin rabuwa. Kwakwalwarmu za ta saba da yin tunani da wuri ba tare da mun mai da hankali ga bin da muke yi ba.” *

 Ga fannoni uku da na’urori za su iya hana ka natsuwa.

  •   Sa’ad da kake magana. Wata matashiya mai suna Maria ta ce: “Ko da mutane suna tattaunawa ido-da-ido ne, wasu sukan ci gaba da tura sakonni, ko buga game ko kuma duba dandalin sada zumunta, maimakon su mai da hankali ga wanda suke magana da shi.”

  •   Sa’ad da kake aji. Wani littafi mai suna Digital Kids ya ce: “Yawancin dalibai sun ce sukan yi amfani da wayoyinsu wajen tura sakonni, ko neman abubuwa a intane ko su shiga kallon bidiyoyin da ba su shafi abin da suke koya a makaranta ba.”

  •   Sa’ad da kake nazari ko karatu. Wani dan shekara 22 mai suna Chris ya ce: “Wani abin da yake min wuya shi ne in guji duba wayata a duk lokacin da ya yi kara.” Idan kai dalibi ne, kuma an ba ka aiki a makaranta ka yi a gida, kila aikin na awa daya ne, amma za ka iya yin awa uku ko fiye da hakan idan na’urorinka suna raba hankalinka.

 Gaskiyar batun: Zai yi maka wuya ka natsu idan na’urorinka ne ka sa a gaba kuma kana barin su su raba hankalinka.

Idan tunaninka yana yawo nan da can, yana kama da dokin da yake gudu da kai kuma ka kasa yi masa ja-gora

 Abin da zai taimake ka ka mai ga hankali ga abin da kake yi

  •   Sa’ad da kake magana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku kula da kanku kadai, amma ku kula da wadansu kuma.” (Filibiyawa 2:⁠4) Ka nuna wa mutane cewa ka damu da su ta wurin sauraronsu da kyau. Ka kalle su sa’ad da suke magana kuma kar ka bar na’urorinka su janye hankalinka.

     Wani mai suna Thomas ya ce, “Idan kana magana da mutane, kada ka rika duba wayarka. Ka daraja wanda kake magana da shi ta wurin ba shi hankalinka.”

     ABIN DA ZAI TAIMAKA: Idan kana magana da wani, za ka iya ajiye wayarka a inda ba za ka gani ba. Masu bincike sun ce ganin wayarka kawai ma zai iya hana ka mai da hankali ga abin da kake yi, don zai rika tuna maka cewa wayar za ta yi kara nan ba da dadewa ba.

  •   Sa’ad da kake aji. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi hankali fa da yadda kuke [sauraro].” (Luka 8:18) Bisa ga wannan abin da Littafi Mai Tsarki ya fada, kar ka rika karanta sakonni ko buga game ko ka rika tura sakonni a aji, ko da akwai sabis na intane a ajinku. Maimakon haka, ka dinga mai da hankali ga abin da ake koyarwa.

     Wata mai suna Karen ta ce: “Ka yi kokari ka saurari abin da ake koyarwa da kyau. Ka rubuta muhimman darussa da malaminku yake koyarwa. Idan zai yiwu ka zauna a kujerar da ke gaba don kar wani abu ya dauke hankalinka.”

     ABIN DA ZAI TAIMAKA: Ka dinga rubutu da hannunka maimakon ka yi amfani da kwamfuta. Masu bincike sun gano cewa hakan zai taimaka maka ka natsu kuma ka tuna abin da ka koya.

  •   Sa’ad da kake nazari ko karatu. Littafi Mai Tsarki ya ce mu kokarta mu ‘sami hikima da ganewa.’ (Karin Magana 4:⁠5) Hakan yana bukatar yin tunani sosai a kan abin da kake karantawa, ba yin karatu sama-sama don ka ci jarrabawa kawai ba.

     Wani mai suna Chris ya ce: “Idan ina nazari, nakan saita wayata yadda kira ko sakonni ba za su shigo ba kuma in mai da hankali ga abin da nake yi. Ba na dauka wayata ko da ta yi wata kara. Idan na tuna wani abin da ba na so in manta, nakan rubuta shi.”

     ABIN DA ZAI TAIMAKA: Ka kawar da duk wani abin da zai raba hankalinka a inda kake karatu. Wurin ya zama da tsabta kuma a shirye.

^ Daga littafin nan, The Shallows​—⁠What the Internet Is Doing to Our Brains.