Koma ka ga abin da ke ciki

Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane

Rayuwa Mai Ma'ana

Na Sami Arziki na Kwarai

Ta yaya wani ɗan kasuwa mai arziki ya sami abin da ya fi kuɗi daraja?

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Amsa Tambayoyina Ya Burge Ni

Ernest Loedi ya sami amsoshin tambayoyi masu muhimmanci game da rayuwa. Amsoshin da ya samu daga Littafi Mai Tsarki sun sa ya kasance da bege.

A Dā Ina Tsoron Mutuwa!

Yvonne Quarrie ta ce, “Me ya sa aka halicce ni?” Amsar da ta samu ta canja rayuwarta.

Jehobah Ya Taimaka Mini Sosai

Wace koyarwa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaki Crystal, wata da aka ci zarafinta ta yin jima’i da ita sa’ad da take karama, ta kulla dangantaka da Allah kuma ta yin rayuwa mai ma’ana?

Yanzu Na Daina Raina Kaina

Ka karanta labarin Israel Martínez, wanda ya daina raina kansa.

Na Sasanta da Mahaifina

Ka koyi abin da ya sa Renée ya soma shan kwayoyi da shan giya har ya bugu da kuma abin da ya taimaka masa ya daina wadannan halayen.

Yanzu Na San Zan Iya Taimaka wa Mutane

Julio Corio ya makanta kuma ya dauka Allah bai damu da shi ba. Nassin da ke Fitowa 3:7 ya taimaka masa ya canja ra’ayinsa.

Na So Na Yaki Rashin Adalci

Rafika ta hada kai da ’yan tawaye don su yaki rashin adalci. Amma yanzu ta gaskata da alkawarin da Allah ya yi a Littafi Mai Tsarki na salama da adalci a karkashin Mulkinsa.

“Na Daina Dauka Cewa Zan Iya Gyara Duniya”

Ta yaya nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa mai fafutikar kāre hakkin ’yan Adam ya fahimci ainihin abin da zai kawo karshen matsalolin ’yan Adam?

Na Bar Aikin Soja

Ka ga yadda sakon da ke cikin Littafi Mai Tsarki mai karfafa mutane ya taimaka wa Cindy ta canja halinta.

A Dā, Ban Yi Imani da Wanzuwar Allah Ba

Ta yaya wani mutum da tun yana yaro bai amince da wanzuwar Allah ba ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki?

Canja Imani

“Akwai Abubuwa da Dama da Na So In Sani”

Me ya tabbatar wa wani fasto a dā mai suna Mario cewa abin da Shaidun Jehobah suke koyarwa gaskiya ne?

Koyarwar Littafi Mai Tsarki Ta Gamsar da Ni

Mayli Gündel ta daina yin imani da Allah bayan rasuwar mahaifinta. Me ya sa daga baya ta sake imani da Allah kuma ta sami kwanciyar rai?

Kwaya da Giya

“Na Daina Zalunci”

A rana ta farko a wurin aikinsa, an yi wa Michael Kuenzle tambaya cewa, “Kana ganin cewa Allah ne yake jawo matsalolin da mutane ke fuskanta a duniya?” Wannan tambaya ta sa ya soma tunanin canja rayuwarsa.

Rayuwata Tana Ta Lalacewa

Solomone ya kaura zuwa Amirka, ko zai sami rayuwa mai inganci. Maimakon haka, ya soma shan miyagun kwayoyi kuma hakan ya sa an daure shi a kurkuku. Me ya taimaka masa ya canja?

Ina Kwana A Titi

Abubuwa da suka faru a rayuwar Antonio sa’ad da yake shaye-shaye da fada sun sa ya ga cewa rayuwa ba ta da wata ma’ana. Me ya taimaka masa ya canja tunaninsa?

Na Koya Mutunta Kaina da Kuma Mata

Joseph Ehrenbogen ya karanta wani abu a Littafi Mai Tsarki da ya taimaka masa ya gyara rayuwarsa.

Na Gaji da Salon Rayuwata

Dmitry Korshunov mashayi ne, amma ya soma karanta Littafi Mai Tsarki kullum. Mene ne ya motsa shi ya yi canji a rayuwarsa kuma ya yi farin ciki na gaske?

“Yanzu Na Sami ’Yanci na Ƙwarai”

Ka karanta yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa wani matashi ya daina shan taba da ƙwaya kuma ya daina maye.

Mugunta da Aikata Laifi

“Aikata Laifi da Son Kudi Sun Cutar da Ni”

Bayan an saki Artan daga kurkuku, ya gano cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da son kudi gaskiya ne.

“A Dā Ina Haka Kabarina”

Me ya sa wannan dan daba daga El Salvador ya canja salon rayuwarsa?

Yanzu Ina Daraja Mutane

Sobantu ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki, ya daina yin zalunci kuma yanzu yana koyar da makwabtansa cewa a nan gaba, mugunta da ’yan daba ba za su kara kasancewa ba.

Ni Mai Zafin Rai Ne a Dā

Wani dan daba ya gaskata cewa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka masa ya canja rayuwarsa kuma ya zama irin mutumin da yake yanzu. A yau yana farin ciki don yana da dangantaka da Allah.

Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada

Mene ne ya taimaki wani dan Meziko mai son fada sosai ya canja salon rayuwarsa?

Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Dā

Stephen McDowell yana da zafin rai a dā, amma wani kisan da ba shi ya yi ba ya sa ya yanke shawarar canja salon rayuwarsa.

Na Koyi Cewa Jehobah Mai Jinkai Ne da Kuma Gafartawa

Yin zamba ya zama jikin Normand Pelletier. Amma ayar da ya karanta a cikin Littafi Mai Tsarki ta sa ya zub da hawaye.

Wasanni, Waka, da Nishadi

Kamar Dai Ina da Kome da Nake So

Stéphane wani mawaki ne da ya shahara sosai. Ko da yake yana ganin yana da kome da yake so, ba ya farin ciki. Mene ne ya taimaka masa ya soma farin ciki da kuma yi rayuwa mai ma’ana?

Lambar Girma Mafi Tamani da Na Samu

Abin da ya sa wani wanda gwani ne cikin wasan tanis ya zama mai wa’azi

“Ina Son Fada Sosai”

Erwin Lamsfus ya taba tambayar abokinsa cewa, “Ka taba yin tunanin ko mece ce manufar rayuwa?” Amsar da ya ba ni ta canja rayuwata.

Na Ji Jiki Sosai Kafin Na Yi Nasara

Ta yaya Josef ya daina kallon hotunan batsa kuma ya kasance da kwanciyar hankali?

Bauta wa Jehobah Ne Yake Sa Mutum Karfi

Wata aya a Littafi Mai Tsarki ta tabbatar wa Hércules cewa zai iya canja halinsa na saurin fushi kuma ya kasance da sabon hali kamar kamewa da kuma kauna.

Ina Son Kwallon Baseball Fiye da Kome!

A dā, Samuel Hamilton yana son kwallo sosai, amma wani raunin da ya ji ya canja rayuwarsa.