Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Amsa Tambayoyina Ya Burge Ni

Yadda Littafi Mai Tsarki Ya Amsa Tambayoyina Ya Burge Ni
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1948

  • KASAR HAIHUWA: HUNGARY

  • TARIHI: YA SO YA SAN AMSOSHIN TAMBAYOYI MASU MUHIMMANCI GAME DA RAYUWA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a birnin Székesfehérvár a kasar Hungary kuma birnin yana da tarihi sosai na fiye da shekara 1,000. Abin bakin ciki shi ne, har yanzu ina tuna yadda yakin duniya na biyu ya yi barna sosai a kasar.

Na yi zama da kakannina sa’ad da nake yaro. Na ji dadin zama da su, musamman kakata Elisabeth. Ta koya min yadda zan yi imani da Allah. Da na kai shekara uku, mun soma yin Addu’ar Ubangiji kowace yamma. Amma sai da na kai kusan shekara 30 ne na fahimci ainihin ma’anar addu’ar.

Kakannina ne suka yi ta kula da ni sa’ad da nake yaro domin iyayena sukan yi aiki dare da rana don su tara kudin da za su sayo mana gida mai kyau. Amma bayan kowane sati biyu, mukan hadu don mu ci abinci tare. Na so wadannan lokutan da muke cin abinci tare.

Abin da iyayena suke nema ya samu a shekara ta 1958, sun iya sayan gida da dukanmu uku za mu iya zama a ciki. A karshe, na soma zama da iyayena kuma na yi farin ciki ba kadan ba! Amma bayan wata shida, wani abin bakin ciki ya faru. Mahaifina ya rasu sanadiyyar cutar kansa.

Mutuwar mahaifina ya bata min rai sosai. Na tuna da addu’ar da na yi cewa: “Ya Allah na roke ka ka ceci mahaifina domin ina bukatar sa. Me ya sa ba ka amsa addu’o’ina ba?” Na so in san wurin da mahaifina yake. Na yi ta tunani: ‘Shin ya je sama ne? Ko kuma ya hallaka kwata-kwata?’ Nakan yi bakin ciki idan na ga wasu yara tare da iyayensu.

Kuma na yi shekaru da yawa ina zuwa makabarta kowace rana, in tsuguna a gaban kabarin babana ina addu’a cewa: “Ya Allah, ka nuna min inda mahaifina yake.” Na kuma roke shi ya sa in fahimci dalilin da ya sa muke rayuwa.

Da na kai shekara 13, sai na soma koyan yaren Jamus. Na yi tsammanin cewa da yake akwai littattafan harshen Jamus da yawa da suka bayyana batutuwa da dama, watakila zan iya samun amsoshin tambayoyina idan na karanta su. A shekara ta 1967, na soma karatu a birnin Jena, da ke kasar Jamus ta Gabas a lokacin. Na karanta littattafan da masanan Jamus suka rubuta, musamman wadanda suka yi bayani a kan wanzuwar mutane. Ko da yake na sami bayanai da yawa a ciki, amma ban gamsu ba. Don haka, na ci gaba da rokon Allah ya taimaka min.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Na koma kasar Hungary a shekara ta 1970 kuma a wurin ne na hadu da matata Rose. A lokacin, kasar Hungary tana karkashin mulkin kwaminisanci. Jim kadan bayan aurenmu, sai muka gudu zuwa Ostiriya. Burinmu shi ne daga baya mu kaura zuwa birnin Sydney a kasar Ostireliya inda kawuna yake.

Na sami aiki a Ostiriya. Wata rana sai abokin aikina ya gaya min cewa zan iya samun amsoshin dukan tambayoyina a Littafi Mai Tsarki. Ya ba ni wasu littattafai da suka tattauna Littafi Mai Tsarki. Na karanta su ba tare da bata lokaci ba kuma na nemi samun karin bayani. Sai na rubuta wa Shaidun Jehobah, mawallafan littattafan wasika don su turo min wasu littattafai.

Wani Mashaidi dan Ostiriya ya ziyarce mu a lokacin da muke bikin cika shekara daya da aure. Ya kawo littattafan da na ce a turo min. Kuma ya ce zai so ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, sai na amince. Mun yi nazarin sau biyu a mako don na yi marmarin sanin Littafi Mai Tsarki. Kuma a kowane lokaci, mukan yi awoyi hudu muna nazari!

Na ji dadin abin da Shaidun suka koya min daga Littafi Mai Tsarki. Na yi mamaki sosai da suka nuna min sunan Jehobah a cikin littafina na yaren Hungary. Na yi shekara 27 ina zuwa coci, amma ban taba jin an ambata sunan Allah ko sau daya ba. Yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyina dalla-dalla ya burge ni sosai. Alal misali, na koya cewa matattu ba su san kome ba, kamar suna barci mai zurfi ne. (Mai-Wa’azi 9:​5, 10; Yohanna 11:​11-15) Ban da haka ma, na koya game da alkawarin Allah na sabuwar duniya inda ba za a sake “mutuwa” ba. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4) Ina marmarin ganin mahaifina a wannan sabuwar duniya, inda “za a tā da matattu.”​—Ayyukan Manzanni 24:15.

Matata Rose ta sa kai a nazarin da muke yi. Mun samu ci gaba sosai kuma muka karasa nazarin littafin da muke amfani da shi a cikin wata biyu! Mun halarci kowane taro da Shaidu suke yi a Majami’ar Mulki. Yadda Shaidun Jehobah suke kauna da taimaka wa juna da kuma hadin kansu ya burge mu sosai.​—Yohanna 13:​34, 35.

A shekara ta 1976, an ba ni da matata bisa na shiga kasar Ostireliya. Nan da nan muka nemi Shaidun Jehobah da suke zama a wurin. Shaidun Jehobah da suke wurin sun taimaka mana sosai don mu ji dadin zama. Mun zama Shaidun Jehobah a shekara ta 1978.

YADDA NA AMFANA:

A karshe na sami amsoshin tambayoyi da suka dade suna damu na. Yanzu da na kusaci Jehobah, na sami Mahaifi da babu kamarsa. (Yakub 4:8) Kuma a kullum, ina dokin ganin mahaifina da ya rasu a sabuwar duniya.​—Yohanna 5:​28, 29.

A shekara ta 1989, ni da matata mun tsai da shawara mu koma kasarmu Hungary don mu koya wa abokanmu da danginmu da kuma duk wani da zai so abubuwan da muka koya daga Littafi Mai Tsarki. Mun sami damar koyar da mutane da yawa. Fiye da mutane 70 daga cikinsu sun fara bauta wa Jehobah, har da mahaifiyata.

Na yi shekaru 17 ina addu’a don in sami amsar tambayoyina. Har bayan shekaru 39 kuma, ban daina addu’a ba. Amma yanzu ne zan iya cewa, “Na gode Ubana da ke sama, da ka amsa addu’ar da na yi ta yi tun ina yaro.”