Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Ina Son Fada Sosai”

“Ina Son Fada Sosai”
  • Shekarar Haihuwa: 1962

  • Kasar Haihuwa: Amirka

  • Tarihi: Na sa yin fada a kan gaba a rayuwata

RAYUWATA A DĀ

 Raunin da abokin fadana ya ji ya yi tsanani sosai, fiye da yadda na yi tsammani. Ba da son raina ba na buge shi a hanci. Hakan ya sa ni damuwa, kuma na soma tunani ko zan daina yin fada. Me ya sa wannan kuskuren ya sa ni tunanin daina wasan da na yi shekaru ina jin dadinsa? Da farko, bari in bayyana yadda na soma yin wannan wasan.

 Na girma a kusa da garin Buffalo da ke jihar New York a Amirka, iyayena suna zuwa cocin Katolika. Na je makarantar ’yan Katolika kuma na yi hidima a matsayin yaron da ke taimaka wa firist. Iyayenmu suna so ni da ’yar’uwata mu yi nasara a rayuwa. Saboda haka, iyayena sun yarda in rika wasa bayan mun tashi makaranta ko in yi aiki na dan lokaci, muddin na ci jarrabawa ta a makaranta. Hakan ya sa na koyi tsara abubuwa tun ina karami.

 A lokacin da nake shekara 17, na soma koyan fada. Na yi shekaru da yawa ina karbar horarwa na awa uku kowace rana sau shida a mako. A kowane mako, ina daukan lokaci da yawa ina yin tunanin dabarun da zan rika amfani da su har da kallon bidiyoyi don in inganta yadda zan rika fada. Na ji dadin koyan fada idanuna a rufe har ma a lokacin da nake amfani da makamai. Nakan karya katako ko kuma fasa bulo da bugu daya. Na zama gwani kuma na sami lambobin yabo da yawa a gasa. Yin fada ya zama abu mafi muhimmanci a rayuwata.

 Na dauka na yi nasara a rayuwa. Na ci jarrabawar kammala makarantar jami’a sosai. Na yi aiki da wani babban kamfani a matsayin injiniya mai gyara kwamfuta. Na sami gida na kaina da kuma budurwa. Wasu sun dauka kamar ina jin dadin rayuwa, amma hakan ba gaskiya ba ne domin akwai tambayoyi game da rayuwa da ban sami amsoshinsu ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Garin neman amsoshin tambayoyina, na soma zuwa coci sau biyu a mako da kuma yin addu’a ga Allah ya taimake ni. Wata rana, abin da na tattauna da wani abokina ya canja rayuwata. Na tambaye shi cewa: “Ka taba yin tunanin ko mece ce manufar rayuwa?” Sai na dada da cewa: “Idan ka duba dama da hagu, za ka ga matsaloli da kuma rashin adalci sun cika ko’ina!” Ya gaya mini cewa shi ma ya yi irin wadannan tambayoyin kuma ya sami amsoshi masu gamsarwa a Littafi Mai Tsarki. Sai ya ba ni wani littafi mai jigo Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya. * Ya gaya mini cewa yana yin nazari da Shaidun Jehobah. Da farko na ki in karba domin ba na so in karbi littafin da ba addinina ne suka rubuta ba. Amma da yake ina so in sami amsoshin tambayoyina, sai na ce zan ga ko abin da Shaidun Jehobah suka rubuta gaskiya ne.

 Na yi mamaki sosai da koyi abin da Littafi Mai Tsarki yake fadi. Na koyi cewa nufin Allah tun farko shi ne mutane su yi rayuwa har abada a cikin aljanna a duniya, kuma har yanzu Allah bai canja nufinsa ba. (Farawa 1:28) Na yi mamaki sosai da na ga sunan Jehobah a cikin nawa juyin Littafi Mai Tsarki, wato King James, da kuma cewa sunan da nake addu’a a kai ke nan a duk lokacin da na yi Addu’ar Ubangiji. (Zabura 83:18; Matiyu 6:⁠9) Kari ga haka, na fahimci dalilin da ya sa Allah yake kyale ’yan Adam su sha wahala. Na gamsu sosai da duk abubuwan da na koya!

 Ba zan taba manta da yadda na ji ba sa’ad da na soma halartan taron Shaidun Jehobah. Sun marabce ni da kyau kuma sun tambaye ni sunana. A taro na farko da na halarta, an ba da jawabi game da addu’o’i da Allah yake ji. Na ji dadin jawabin domin na jima ina addu’a ga Allah ya taimake ni. Daga baya, na halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu. A wadannan tarukan, na yi mamaki da na ga cewa har yara ma suna bude Littafi Mai Tsarki da kansu. Da farko, ban san yadda ake neman ayoyi a Littafi Mai Tsarki ba, amma Shaidun Jehobah sun taimaka mini in iya yin hakan.

 Da na ci gaba da halartan taro, sai na dada daraja Shaidun Jehobah don yadda suke koyarwa. Na koyi abubuwa da yawa a kowane taro da na halarta, kuma na gamsu sosai. Sai wani Mashaidi ya ce zai yi nazari da ni.

 Abubuwan da Shaidun Jehobah suke yi ya bambanta sosai da na cocinmu. Na ga cewa Shaidun Jehobah suna da hadin kai kuma suna iya kokarinsu domin su faranta wa Allah rai. Na kasance da tabbaci cewa suna kaunar juna sosai, kuma abin da Yesu ya ce zai sa a san Kiristoci na gaskiya ke nan.​—⁠Yohanna 13:⁠35.

 Da na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na soma canja salon rayuwata. Amma ya yi mini wuya in daina wasan dambe. Ina son yin horo da kuma gasa sosai. Da na gaya wa dan’uwan da yake nazari da ni, sai ya karfafa ni, ya ce: “Ka ci gaba da yin nazari, na tabbata cewa za ka yanke shawara mai kyau.” Abin da nake so in ji ke nan. Da na ci gaba da yin nazari, sai na soma so in faranta wa Jehobah rai.

 Abin da ya sa na canja ra’ayina shi ne abin da na ambata dazu, wato raunin da na ji wa abokin fadana a lokacin da na buge shi a hanci a cikin kuskure. Abin da ya faru ya sa na soma tunanin ko idan na ci gaba da yin wasan dambe zan zama mabiyin Kiristi mai son zaman lafiya. Na koya a Ishaya 2:​3, 4 cewa wadanda suke bin ka’idodin Jehobah “ba za su kara koyon dabarar yaki kuma ba.” Kuma Yesu ya koya wa mabiyansa cewa kada su rama idan an ci zalinsu. (Matiyu 26:52) Saboda haka, na daina yin wasan da nake so sosai.

 Bayan haka, na bi shawarar Littafi Mai Tsarki cewa in ‘horar da kaina cikin hali irin na Allah.’ (1 Timoti 4:⁠7) A maimakon in rika bad da lokaci wajen yin wasan dambe, na soma amfani da lokacin don yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. Budurwata ba ta amince da abubuwan da nake koya daga Littafi Mai Tsarki ba, sai muka rabu. Na yi baftisma don in zama Mashaidin Jehobah a ranar 24 ga Janairu, 1987. Bayan dan lokaci, sai na soma hidima ta cikakken lokaci. Na ci gaba da yin hidimar nan har wa yau, na ma dan yi hidima a ofishinmu da ke jihar New York a Amirka.

YADDA NA AMFANA

 Yanzun da na san gaskiya game da Allah, rayuwata ta kasance da ma’ana. Ina da bege mai kyau game da nan gaba kuma ina farin ciki sosai. Har yanzu ina jin dadin motsa jiki a kai a kai, amma hakan ba shi ne ya fi muhimmanci a rayuwata ba. Abin da ya fi muhimmanci a rayuwata shi ne in bauta wa Jehobah.

 A lokacin da nake wasan dambe, a kullum ina cikin fargaba, domin ina tunanin yadda zan kāre kaina idan wani ya kawo mini hari. A yau, ina mai da hankali don in taimaka wa mutane. Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in zama mai bayarwa hannu sake, da kuma miji nagari ga matata mai suna Brenda.

 A dā ina son wasan dambe sosai. Amma yanzu, na sauya shi da abu mafi kyau. Littafi Mai Tsarki ya bayyana hakan a hanyar da ta fi dacewa, cewa: “Ko da yake horon jiki yana da dan amfani, amma dai kasancewa da hali irin na Allah ya fi amfani a ta kowace hanya, gama yana jawo albarka ga rayuwar nan ta yanzu da kuma rayuwa mai zuwa.”​—⁠1 Timoti 4:⁠8.

^ sakin layi na 5 Shaidun Jehobah ne suka wallafa amma yanzu an daina bugawa.