Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“A Dā Ina Haƙa Kabarina”

“A Dā Ina Haƙa Kabarina”
  • Shekarar Haihuwa: 1978

  • Kasar Haihuwa: El Salvador

  • Tarihi: Dan Daba

RAYUWATA TA DĀ

 “Idan kana so ka san Allah, ka ci gaba da yin cudanya da Shaidun Jehobah.” Wannan furucin ya ban mamaki sosai. A lokacin da na ji wannan furucin, bai dade da na soma nazari da Shaidun Jehobah ba. Don ku fahimci dalilin da ya sa wannan furucin ya ba ni mamaki, bari in ba ku labarina.

 An haife ni a garin Quezeltepeque, a kasar El Salador. Ni ne na 6 a cikin yara 15 da iyayena suka haifa. Iyayena sun yi kokarin koya mana fadin gaskiya da kuma bin doka. Ban da haka, Leonardo da kuma wasu Shaidun Jehobah suna zuwa gidanmu don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mu. Amma na yi watsi da abin da aka koya mini, kuma hakan ya sa na yanke shawarwarin da ba su dace ba. Sa’ad da nake dan shekara 14, sai na fara shan giya da kwayoyi tare da abokaina a makaranta. Dukan abokaina sun bar makaranta suka shiga kungiyar ’yan daba, sai ni ma na bi su. A kan titi muke zama muna yi wa mutane kwace da kuma sata don biyan bukatunmu.

 ’Yan kungiyar sun zama iyalina, kuma a ganina dole ne in nuna musu aminci. Alal misali, wata rana, wani dan kungiyarmu ya sha kwaya ya bugu, sai ya kai ma makwabcina hari. A lokacin da suke fadan, makwabcina ya sha karfin abokina kuma sai ya kira ’yan sanda. Hakan ya bata mini rai kuma na dauki katon kulki na fara farfasa gilashin motar makwabcina don ya saki abokina. Mutumin ya roke ni in daina, amma na ki ji kuma na ci gaba da farfasa wundon motar.

 A lokacin da na kai shekara 18, kungiyarmu ta yi arangama da ’yan sanda. Sa’ad da nake kokarin jefa wa ’yan sandan bam, sai ya fashe a hannuna, ban san yadda hakan ya faru ba. Na dai ga hannu na a farfashe sai na suma. Da na farfardo a asibiti sai aka ce mini, an yanke hannuna na dama, ba zan rika ji da kunnena na dama ba kuma ba zan rika gani sosai da idon dama ba.

 Duk da wadannan munana raunuka, da na fito daga asibiti na sake koma kungiyar. Ba da dadewa ba bayan haka, ’yan sanda sun kama ni kuma aka saka ni a kurkuku. A kurkukun, dangantakata da ’yan kungiyar ta dada karfi. A kowace rana muna yin kome tare, daga cin abincin safe sai mu shiga shan tabar aljanu, har barci.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWA TA

 A lokacin da nake kurkuku, Leonardo ya ziyarce ni. Da muke magana, sai ya yi nuni ga jarfar da ke hannuna na dama kuma ya ce: “Ka san abin da jarfar nan uku suke nufi?” Sai na ce: “Kwarai kuwa, na sani, suna nufin jima’i da kwayoyi da kuma cashewa.” Amma Leonardo ya ce: “A ganina suna nufin asibiti da kurkuku da kuma mutuwa. Ka je asibiti, yanzu kana kurkuku kuma ka san abin da zai biyo baya.”

 Abin da Leonardo ya ce ya ba ni mamaki. Abin da ya fada gaskiya ne. Ashe salon rayuwata tana kama da haka kabari. Leonardo ya ce mini mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki, sai na amince. Abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki ya motsa ni na canja rayuwata. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zama da mugaye yakan bata halayen kirki.” (1 Korintiyawa 15:33) Don haka, abu na farko da na bukaci yi shi ne canja mutanen da nake yin abokantaka da su. Sai na daina halartan taron kungiyar ’yan daba da muke yi a kurkuku, kuma na soma halartan taron Shaidun Jehobah da suke yi a kurkukun. A taron, na hadu da wani fursuna mai suna Andrés wanda an riga an yi masa baftisma a kurkukun, kuma ya zama Mashaidin Jehobah. Ya gayyace ni cin abincin safe da shi, daga wannan lokacin na daina shan wi-wi da safe. A maimakon haka, ni da Andrés mukan tattauna aya guda a kowace safiya.

 Nan da nan ’yan kungiyar suka gano cewa na soma canja salon rayuwata, hakan ya sa daya cikin shugabannin ’yan daban ya ce yana so ya yi magana da ni. Hakan ya tsorata ni. Ban san abin da zai yi mini ba idan ya ji cewa ina so in bar kungiyar domin barin kungiyar ’yan daba yana da wuya sosai. Ya ce: “Mun lura cewa ba ka zuwa taronmu, a maimakon hakan, kana zuwa taron Shaidun Jehobah. Me kake kokarin yi?” Na gaya masa cewa ina so in ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki kuma in canja salon rayuwata. Na yi mamaki da ya gaya mini cewa ’yan kungiyar ba za su yi mini kome ba idan na tabbata cewa na zama Mashaidin Jehobah. Sai ya ce: “Idan kana so ka san Allah, ka ci gaba da yin cudanya da Shaidun Jehobah. Muna sa rai za ka daina yin munana abubuwa. Ina taya ka murna domin kana hanyar gaskiya. Shaidun Jehobah za su taimaka maka. Ni ma na yi nazari da su a kasar Amirka, wasu membobin iyalina ma Shaidun Jehobah ne. Kada ka ji tsoro.” Duk da haka, na tsorata, amma na yi farin ciki. Sai na gode wa Jehobah a zuciyata. Kuma na ji kamar tsuntsun da aka sake shi daga keji, hakan ya sa na fahimci abin da Yesu ya fada: Ya ce: “Za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za ta ba ku ’yanci.”​—Yohanna 8:32.

 Duk da haka, wasu abokaina na dā, sun jarraba ni ta wajen ba ni kwayoyi. Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta nakan karba. Amma da shigewar lokaci, bayan addu’a mai tsanani, na kubuta daga wannan munana abubuwan.​—Zabura 51:​10, 11.

 Bayan an sake ni daga kurkuku, mutane da yawa gani suke zan koma gidan jiya, amma ban koma ba. A maimakon haka, nakan je kurkuku a kai a kai don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da fursunoni. Daga baya, abokaina na dā sun ga cewa da gaske na canja salon rayuwata. Amma abokan gāban kungiyar ’yan daba da nake a dā ba su san hakan ba.

 Wata rana da muka fita yin wa’azi da wani dan’uwa, sai abokan gāban kungiyar ’yan daba da nake a dā suka kewaye mu da makamai suna so su kashe ni. Sai dan’uwan ya bayyana musu cewa ni ba dan daba ba ne kuma. Ni kuwa na natsu. Bayan sun yi mini dūka, sai suka yi mini kashedi kada in sake zuwa wannan unguwar. Sai suka mayar da makamansu, suka ce mana mu tafi. A gaskiya, Littafi Mai Tsarki ya canja rayuwata. Da a ce dā ne, da na yi kokarin daukar fansa. Amma na bi shawarar da ke Littafin 1 Tasalonikawa 5:15 da ya ce: “Ku kula fa kada kowa ya rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi kokarin yin abin da yake nagari wa junanku da kuma sauran mutane.”

 Tun da na zama Mashaidi, ina yin iya kokarina in kasance mutum mai gaskiya. Yin hakan bai da sauki. Amma da taimakon Jehobah da bin shawarwarin Littafi Mai Tsarki, da kuma taimakon ’yan’uwa, na yi nasara. Ba na so in sake komawa salon rayuwata ta dā.​—2 Bitrus 2:22.

YADDA NA AMFANA

 A dā ni mutum ne mai cin zali da kuma saurin fushi. Na tabbata cewa da a ce na ci gaba da bin salon rayuwata ta dā, da yanzu na mutu. Abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki ya canja ni. Na soma zaman lafiya da makiyana. (Luka 6:27) Yanzu ina da abokai da suke taimaka mini in kasance da halaye masu kyau. (Karin Magana 13:20) A yanzu, ina yin rayuwa mai ma’ana kuma ina jin dadin bauta wa Allah wanda yake a shirye ya gafarta mini duk laifofina.​—Ishaya 1:18.

 A shekara ta 2006, na halarci makaranta na musamman na koyar da Shaidun Jehobah marasa aure. Bayan ’yan shekaru, sai na yi aure kuma ni da matata muka yi rainon ’yarmu. Yanzu ina amfani da lokacina don koyar da mutane ka’idodin Littafi Mai Tsarki da suka taimaka mini. Kari ga haka, yanzu ni dattijo ne a ikilisiya, kuma ina yin iya kokarina don in taimaka wa yara da matasa su guji yin irin kuskuren da na yi a lokacin da nake matashi. A yanzu, maimakon haka kabarina, ina kokarin samun rai na har abada wanda Allah ya yi mana alkawarinsa a Littafi Mai Tsarki.