Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Lambar Girma Mafi Tamani da Na Samu

Lambar Girma Mafi Tamani da Na Samu
  • SHEKARAR HAIHUWA 1967

  • KASAR HAIHUWA FINLAND

  • TARIHI GWANI A WASAN TANIS

RAYUWATA TA DĀ

 Na yi girma a wani kauyen da ke kusa da birnin Tampere, a Finland. Iyalina ba su damu da zancen addini ba amma suna daukaka samun ilimin duniya da kuma tarbiyya mai kyau. Lokacin da nake yaro, nakan je hutu wurin kakannina a Yammacin Jamus domin mamata ’yar Jamus ce.

 Tun ina yaro ina son yin wasanni. Da farko dai, ina wasanni dabam-dabam, amma sa’ad da na kai shekara 14, sai na mai da hankali na ga wasan tanis. Lokacin da na ke shekara 16, sai na soma zuwa koyan wasan tanis sau biyu ko uku a rana. Wani da ya gwanince a wasan tanis yana horar da ni sau biyu a rana sai ni kuma in gwada yin wasan da kaina da yamma. Fannoni dabam-dabam na wasan yana burge ni kuma yin wasan tanis hanya ce da zan horar da kaina. Ko da yake nakan ji dadin fita da abokaina mu dan sha giya a wasu lokatai, ba a taba kama ni wai na bugu ko kuma na sha kwaya ba. Na fi ba wasan tanis fifiko a rayuwata.

 A lokacin da na kai shekara 17 * sai na soma gāsa cikin wasannin da ake kira ATP. Bayan da na ci gāsa dabam-dabam, sai sunana ya bazu cikin kasar. Da na kai shekara 22, sunana yana cikin sunayen mutane 50 da suka gwanince cikin wasan tanis a duk fadin duniya.

 Na yi shekaru da yawa ina zuwa kasashe dabam-dabam a duniya ina wasan tanis. Na ga wurare masu ban sha’awa, amma kuma na lura cewa duniya tana fuskantar matsaloli dabam-dabam, kamar aikata laifi da shan mugun kwayoyi da kuma rashin tsabtace mahalli. Alal misali, lokacin da muke kasar Amirka, an ce mana kada mu je wasu wurare a cikin birnin domin yawan aikata laifi da ake yi a wurin. Duk irin wadannan abubuwan sun daga mini hankali. Ko da yake ina yin abin da nake jin dadinsa, amma a karshe, ba na samun gamsarwa.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Budurwata mai suna Sanna, ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Yadda ta soma son zancen addini ya dan ban mamaki, amma ban damu da nazarin da take yi ba. Mun yi aure a shekara ta 1990, ta yi baftisma kuma zama daya cikin Shaidun Jehobah a 1991. Ko da yake na gaskata cewa akwai Allah, amma ban dauki addini da wani muhimmanci ba. Na tuna cewa kakata wadda ’yar Jamus ce tana son karanta Littafi Mai Tsarki sosai, har ma ta koya min yin addu’a.

 Wata rana da muka ziyarci wasu Shaidu ma’aurata, sai mijin, wanda sunansa Kari ya nuna min annabcin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da “kwanaki na karshe.” (2 Timoti 3:1-5) Wannan ya burge ni kwarai da gaske, domin yanzu na fahimci dalilin da ya sa abubuwa suka dagule haka a duniya. Ba mu yi zance akan addini sosai ba a ranar. Amma kuma, daga ranar sai na soma yin zance game da Littafi Mai Tsarki tare da Kari, kuma duk abubuwan da na ke koya sun gamsar da ni. Yawan tafiye-tafiye da na ke yi da kuma rashin lokaci, ya sa ba mu cika haduwa da Kari, amma hakan bai sa shi sanyin gwiwa ba. Ya kan mayar da amsoshin tambayoyin da na yi a lokacin nazarinmu cikin wasika. Na sami amsar tambayoyi masu wuya game da yanayin rayuwa cikin Littafi Mai Tsarki, kuma a hankali sai na gane jigon da Littafi Mai Tsarki ke dauke da shi, wato cewa Mulkin Allah zai cimma nufin Allah a duniya. Koya cewa sunan Allah, Jehobah ne, kuma ganin dukan abubuwan da ya yi mana ya burge ni kwarai da gaske. (Zabura 83:18) Abin da ya fi burge ni shine tanadin fansa da ya yi, ba kwasam kawai ya yi wannan shirin, ko bi wani tsarin doka ba, amma ya nuna mana cewa yana kaunar mu ne. (Yohanna 3:16) Na kuma koya cewa zan iya zama aminin Allah kuma in rayu har abada a cikin salama a al’janna. (Yakub 4:8) Sai na soma tambayar kaina cewa, “Ta wace hanya ce zan nuna godiya ga wannan tanadin?”

 Hakan ya sa na dubi yanayin rayuwata. Abin da na ke koya daga Littafi Mai Tsarki shine cewa mutum zai fi samun farin ciki idan yana bayarwa, sai na ji sha’awar gaya wa wasu game da imani na. (Ayyukan Manzanni 20:35) A cikin shekara daya na kan yi kwana 165 kawai a gida tare da iyalina, domin ni gwani ne a wasan tanis kuma hakan na bukatar in yi tafiye-tafiye da yawa ina gāsa. Yanzu na gane cewa ya kamata in yi wani abu don in taimaka wa iyalina, domin aiki da wasanni da na ke yi suna daukan lokaci na sosai.

 Na sani cewa mutane da yawa ba za su gane dalilin da ya sa zan bar aiki mai ni’ima domin ina son in yi ayyukan addini ba. Amma zarafin sanin Jehobah da na samu da kuma begen yin rayuwa na har abada ya fi duk wani lambar girma da zan ci a wasan tanis, saboda haka na tsai da shawara daina wasanni. Matakin da na dauka ba ta zama mini da wuya ba, domin na kudura cewa ba zan damu da abin da mutane za su ce ba. Wata aya cikin Littafi Mai Tsarki da ta karfafa ni sosai ita ce Zabura 118:6 wadda ta ce: “Ubangiji yana wajena; ba zan ji tsoro ba: Ina abin da mutum za ya yi mani?”

 A wannan lokacin ne wasu mutane suka ba ni wani aikin da zai sa in zama cikin gwanin dan wasan tanis, kuma hakan zai sa in yi arziki. Amma na riga na yanke shawarata, saboda haka ban karba aikin ba kuma daga baya ma na daina yin wasan. Na ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma aka yi mini baftisma na zama daya daga cikin Shaidun Jehobah ranar 2 ga Yuli 1994.

YADDA NA AMFANA

 Ba wai sanda wani bala’i ya fado mini kafin na sani cewa akwai Allah ba. Ba kuma cewa ina neman sanin addini na gaske ba. Ni dai ina jin kamar ba ni da wata damuwa a rayuwa, na gamsu da yanayi na. Kwasam kawai, kamar dama gaskiyar da ke cikin Littafi Tsarki na jira in samo ta, na gano cewa ashe rayuwa tana da ma’ana sosai fiye da yadda na sani, kuma yanzu rayuwata ta fi kyau fiye da dā sosai! Kaunar da ke cikin iyalinmu ta kara danko kuma mun fi kusa da juna yanzu. Ina farin ciki cewa yara na maza uku sun bi gurbi na, sun zama Kiristoci na gaske, ba ’yan wasa ba.

 Har yanzu ina jin dadin wasan tanis. Yanzu ina samun na biyan bukata ta wurin koya wa mutane wasan tanis kuma ni manaja ne a wani filin wasan Tanis. Amma rayuwata ba ta dangana ga yin wasanni ba. A dā, ina bata lokaci sosai wurin yin wasan tanis domin ina son in zama gwani cikin wasan. Yanzu ni mai wa’azin bishara na cikakken lokaci ne, ina jin dadin yin amfani da lokacin da nake da shi don in taimaka wa mutane su koyi kuma yi amfani da ka’idodin Littafi Mai Tsarki wanda ya canja rayuwata. Ina bala’in jin dadin lokacin da nake bayarwa wajen kyautata dangantakata da Jehobah da kuma gaya wa wasu bege mai kyau da nake da shi. 1 Timoti 6:19.

^ sakin layi na 3 Ma’anar ATP shi ne Association of Tennis Professionals. Wannan shi ne kungiyar maza da suka gwanince a wasan tanis. ATP sukan yi zagaya, gwanaye suna gāsa a lokacin zagayar kuma ana cin digo a kowane wasa kuma ana ba wadanda suka ci gāsar kyautar kudi. Kafin sunan mutum ya shiga cikin sunayen mutanen da suka gwanince a duniya, hakan ya dangana ga yawan digon da mutum ya samu a lokacin gāsar.