Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

”Ni Mai Zafin Rai Ne a Dā”

”Ni Mai Zafin Rai Ne a Dā”
  • Shekarar Haihuwa: 1975

  • Kasar Haihuwa: Meziko

  • Tarihi: Dan fursuna mai zafin rai

RAYUWATA A DĀ

 An haife ni a San Juan Chancalaito, wani karamin gari a jihar Chiapas da ke kasar Mexico. Iyalinmu mutanen Chol ne, kuma sun fito ne daga kabilar Maya. Iyayena sun haifi ’ya’ya 12 kuma ni ne na biyar a cikinsu. A Lokacin da nake yaro, Shaidun Jehobah sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni da kuma ’yan’uwana. Abin bakin ciki shi ne, a lokacin ban bi shawarar Littafi Mai Tsarki ba.

 Sa’ad da na cika shekara 13, na soma shan kwayoyi da yin sata har na bar gida kuma na fara yawace-yawace. Da na kai shekara 16, na fara aiki a wata gonar da ake noman wi-wi. Na yi kusan shekara daya ina aiki a wurin, sai wata rana daddare yayin da muke kokarin mu kai wi-wi mai yawa da kwalekwale, wasu mutane da makamai daga rukunin abokan gābanmu masu sana’ar sayar da kwayoyi suka kawo mana hari. Na tsira daga harbin da suka yi domin na fada cikin kogin kuma na yi iyo zuwa tsallaken kogin. Bayan haka, sai na gudu zuwa Amirka.

 A Amirka, na ci gaba da sana’ar sayar da kwayoyi kuma hakan ya kara sa ni cikin matsala. Da na cika shekara 19, an kama ni kuma aka sa ni a kurkuku da zargin yin fashi da kuma niyyar yin kisan kai. A kurkuku, na shiga kungiyar ’yan daba kuma na ci gaba da yin mugunta. Hakan ya sa hukuma ta kai ni wani kurkukun da aka tsare sosai a Lewisburg da ke jihar Pennsylvania.

 A cikin kurkukun Lewisburg, hali na sai dada bacewa yake yi. Da yake ina da jarfa a jikina, ya yi mini sauki in sake shiga ƙungiyar ’yan daba da ke wannan kurkuku. Na dada zama mugu sosai kuma ina yawan fada da mutane. Akwai wata rana da muka yi fada a filin da ke kurkukun. Mun yi kazamar fada har da sanduna da karafuna. Domin su raba wannan fada, masu tsaron kurkuku suka wasa barkonon tsohuwa. Bayan haka, sai hukumar kurkukun suka saka ni a wani wuri na musamman a kurkukun da aka yi don ’yan fursuna masu mugunta sosai. Ina da zafin rai sosai kuma ina zage-zage. Ba ya yi mini wuya na dūki mutum kuma ina ma jin dadin hakan. Ban yi da-na-sani don halina ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWA TA

 A wurin da aka yi don ’yan fursuna masu mugunta sosai, an rufe ni a wani daki kuma a yawancin lokaci ba na iya fita waje, sai na fara karanta Littafi Mai Tsarki domin ban da abin da zan yi. Bayan haka, wani mai gadi ya ba ni littafin nan Zaka Iya Rayuwa Har Abada a Aljanna a duniya. * Yayin da nake karanta wannan littafin, na tuna abubuwa da yawa da na koya a lokacin da nake karami sa’ad da Shaidun Jehobah suke nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Bayan haka, na soma tunani a kan yadda rayuwa ta lalace sosai domin mugun halina. Ban da haka, na yi tunani game da iyalina. Da yake ’yan’uwana mata biyu sun riga sun zama Shaidun Jehobah, sai na soma tunanin cewa, ‘Za su rayu har abada.’ Sai na tambayi kaina, ‘Me zai hana ni yin rayuwa har abada?’ Daga nan ne na yanke shawarar cewa zan canja salon rayuwata.

 Amma na san cewa ina bukatar taimako domin na canja salon rayuwata. Da farko, na yi addu’a ga Allah Jehobah ya taimake ni. Bayan haka, na rubuta wasika zuwa ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka cewa ina bukatar a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Sai suka shirya da wata ikilisiya da ke kusa da inda nake domin a yi nazari da ni. A wannan lokacin, ba a yarda mutanen da ba iyalina ba su ziyarce ni, sai wani Mashaidi daga wannan ikilisiyar ya fara aiko mini wasiku da littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, kuma wadannan littattafan sun dada motsa ni na so canja rayuwata.

 Na dauki matakin barin kungiyar ’yan daba da na yi shekaru da yawa a ciki. Shugaban kungiyar ’yan daban shi ma yana wurin da aka yi don ’yan fursuna masu mugunta sosai. Na same shi a lokacin da muke fita shakatawa kuma na gaya masa cewa ina so in zama Mashaidin Jehobah. Na yi mamaki sosai da ya ce: “Idan da gaske kake, ka yi hakan, ba zan hana ka yin aikin Allah ba. Amma idan kana son barin kungiyarmu ne kawai, ka san sakamakon yin hakan.”

 Bayan shekaru biyu, ma’aikatan kurkukun sun ga canji a halayena. Hakan ya sa sun soma mutunta ni. Alal misali, masu gadin su fara kai ni wurin wanka ba tare da saka mini sarka ba. Daya daga cikin masu gadin ya same ni kuma ya karfafa ni cewa in ci gaba da yin canje-canjen da nake yi. Kari ga haka, hukumar kurkukun sun komar da ni wata karamar kurkuku da ba a tsaro sosai da ke kusa da kurkukun da nake a shekara ta karshe da zan yi a kurkuku. Bayan na yi shekaru goma a kurkuku, an sake ni a shekara ta 2004 kuma aka dauke ni a motar gidan yari aka mayar da ni Meziko.

 Nan da nan da muka iso Meziko, sai na nemi inda Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah take. Da inifam na fursunoni na halarci tarona na farko domin shi ne kadai kaya mai kyau da nake da shi. Shaidun sun marabce ni duk da cewa kayan ’yan fursuna na saka. Yadda suka nuna mini alheri ya sa na ji cewa ina tsakanin Kiristoci na gaskiya. (Yohanna 13:15) A wannan taron, dattawan ikilisiyar suka shirya domin a fara nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Bayan shekara daya, na yi baftisma a ranar 3 ga Satumba, 2005.

 Na soma hidimar majagaba na cikakken lokaci, a watan Janairu 2007, kuma ina daukan sa’o’i 70 a kowace wata ina yin wa’azi. A shekara ta 2011, na gama Makarantar Littafi Mai Tsarki don ’Yan’uwa Maza Marasa Aure (wanda yanzu ake kira Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki). Wannan makarantar ta taimaka mini sosai don yin hidimomi a ikilisiya.

Yanzu ina jin dadin koyar da wasu su zama masu salama.

 A 2013, na auri mata ta Pilar. Takan gaya mini da wasa cewa yana yi mata wuya ta yarda da dukan abubuwan da nake gaya mata game da yadda rayuwata take a dā. Ban sake komawa rayuwata ta dā ba. Ni da matata mun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka mini in canja rayuwata kuma na zama irin mutumin da nake yanzu.

YADDA NA AMFANA

 Ina gani cewa kalmomin Yesu da ke a Luka 19:10 ya shafe ni. A wurin ya ce: ‘[Na] zo ne musamman neman abin da ya bata, na cece shi kuma.’ Ban sake jin na bace a rayuwa ba. Ba na kuma cin mutuncin mutane. Ina godiya ga littafi Mai Tsarki, yanzu rayuwata ta kasance da ma’ana, ina zaman lumana da mutane, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, ina da dangantaka mai kyau da Mahaliccina, Jehobah.

[KARIN BAYANI]

^ sakin layi na 5 Shaidun Jehobah ne suka wallafa wannan littafin amma an daina bugawa. A yanzu littafin da suke amfani da shi don koyarwa shi ne Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?