Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Yanzu Na San Zan Iya Taimaka wa Mutane

Yanzu Na San Zan Iya Taimaka wa Mutane
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1981

  • KASAR HAIHUWA: GUATEMALA

  • TARIHI: YA SHA WUYA SA’AD DA YAKE GIRMA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a wani gari mai suna Acul, garin yana a kan tuddan da ke yammacin kasar Guatemala. Mu mutanen Ixil ne daga kabilar Maya. Ina yarenmu da kuma Sifanisanci. An haife ni a lokacin da ake yakin basasa a Guatemala. An yi shekaru 36 ana yakin kuma an kashe mutanen Ixil da yawa.

Da na kai shekara hudu, dan’uwana wanda shekarunsa bakwai a lokacin, ya dauki gurnati yana wasa da shi, kuma abin ya fashe a hannunsa. Gurnatin ya kashe shi kuma ya makantar da ni. Daga baya an kai ni makarantar makafi a birnin Guatemala City, inda na koyi karatun makafi. Malaman makarantar sun hana ni magana da sauran ’yan makarantar kuma ’yan makarantar da kansu ma sun guje ni. Ban san abin da ya sa suka yi haka ba. Na kadaita sosai, kuma a kullum ina alla-alla a ba mu hutun wata biyu da ake ba mu kowace shekara, don in je in ga mahaifiyata da take nuna min kauna sosai. Abin bakin cikin shi ne, ta rasu a lokacin da na kai shekara goma. Rasuwarta ya jijjiga ni sosai domin ita ce kadai take kauna ta.

Da na kai shekara 11, sai na koma garinmu inda na zauna da yayana da iyalinsa. Sun kula da bukatuna amma ba wanda ya iya kwantar min da hankali. A wasu lokuta, nakan yi kuka kuma in tambayi Allah cewa: “Don me mahaifiyata ta rasu? Don me na makance?” Mutane sukan gaya min cewa haka Allah ya so. Hakan ya sa na dauka cewa Allah marar tausayi ne kuma mai rashin adalci ne. Da na san yadda zan kashe kaina, da na yi hakan.

Da yake ni makaho ne, yana da sauki mutane su ci zarafina. An yi min fyade sau da yawa sa’ad da nake yaro. Ban gaya wa kowa ba domin ina ganin ba wanda ya damu da ni. Mutane ba sa yawan min magana kuma ni ma ba na magana da kowa. Na shiga bakin ciki sosai kuma ba na sake jiki da mutane don ban yarda da kowa ba.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

A lokacin da nake shekara 13, wani Mashaidin Jehobah da matarsa sun zo sun yi mini wa’azi a makaranta a lokacin shan iska. Ashe wata malama ce ta tura su wurina domin tana tausaya min. Sun gaya min cewa Littafi Mai Tsarki ya ce wata rana Allah zai ta da matattu kuma zai bude idanun makafi. (Ishaya 35:5; Yohanna 5:​28, 29) Na ji dadin abin da suka gaya min amma yin magana da su ya min wuya domin ban saba yin magana da mutane ba. Duk da cewa ban saki jiki da su ba, sun yi hakuri da ni kuma sun yi min alheri. Sun ci gaba da zuwa don su koya min abin da ke Littafi Mai Tsarki. Sukan yi tafiya fiye da kilomita 10 ta kan tuddai kafin su iso garinmu.

Dan’uwana ya ce min suna yin ado mai kyau amma su ba masu kudi ba ne. Duk da haka sun nuna min kauna kuma sukan kawo min tsaraba. Sadaukarwar da suke yi ta sa na gane cewa lallai mutanen nan Kiristoci na gaskiya ne.

Na yi amfani da littattafan makafi sa’ad da suke nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Ko da yake na fahimci abin da suka koya min, ya dan min wuya in amince da wasu abubuwan. Alal misali, ya min wuya in yarda cewa Allah ya damu da ni, kuma cewa akwai mutanen da suka damu da ni. Na fahimci abin da ya sa Allah ya kyale munanan abubuwa su faru, amma ya min wuya in yarda cewa Allah Uba ne mai kauna. *

A hankali, abubuwan da na koya daga Littafi Mai Tsarki sun sa na canja ra’ayina. Alal misali, na koyi cewa Allah yana tausaya wa mutanen da suke shan wahala. Da ya ga ana wulakanta bayinsa, Allah ya ce: “Na ga azabar da jama’ata suke sha . . . Hakika, na san dukan wahalarsu.” (Fitowa 3:7) Da na gane irin halaye masu kyau da Jehobah yake da su, na yi alkawari cewa zan bauta masa. A 1998, na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

Ni da dan’uwan da iyalinsa suka karbe ni a gidansu

Wajen shekara daya bayan na yi baftisma, na je wata makarantar makafi da ke kusa da birnin Escuintla. A Escuintla, wani dattijo ya ji irin famar da nake yi kafin in je taro sa’ad da nake zama a garinmu. Ikilisiya mafi kusa da kauyenmu yana inda Shaidun da suka yi nazari da ni suke, kuma sai na bi ta kan tuddai kafin in isa wurin. Hakan bai yi mini sauki ba. Da dattijon ya ji hakan, sai ya yi magana da wani Mashaidi da ke Escuintla, kuma iyalinsa sun amince in zauna da su don in rika zuwa taro cikin sauki. Har wa yau, su suke kula da ni. Sun mai da ni dansu.

Akwai lokuta da yawa da ’yan’uwa a ikilisiya suka nuna min kauna. Alherin da suka yi ta nuna mini ya tabbatar mini cewa addinin da nake bi addini na gaskiya ne.​—Yohanna 13:​34, 35.

YADDA NA AMFANA:

Yanzu na san cewa Allah yana kauna ta kuma ina da begen yin rayuwa har abada. Ba na tunani cewa rayuwata ba ta da amfani. Ina amfani da yawancin lokacina wajen koya wa mutane Littafi Mai Tsarki, kuma hakan yana taimaka min in rage yawan tunani a kan yanayina. Kari ga haka, ni dattijo ne kuma ina yin jawabai a ikilisiyoyi da dama. Na ma sami damar ba da jawabai a taron yanki inda dubban mutane suke halarta.

Ina ba da jawabi kuma ina amfani da Littafi Mai Tsarki na makafi

A 2010, na sauke karatu a Makarantar Koyar da Masu Hidima (wadda ake kira Makarantar Masu Yada Bisharar Mulki yanzu) da aka yi a El Salvador. Koyarwar da na samu ta taimaka min in yi ayyukan da aka ba ni a ikilisiya da kyau. Koyarwar ta sa na ga cewa Jehobah yana kauna ta sosai, kuma zai iya sa dukanmu mu kware a yin aikin da ya ba mu.

Yesu ya ce: “Ya fi albarka [‘sa farin ciki,’ NW ] a bayar da a karba.” (Ayyukan Manzanni 20:35) A yau, da dukan zuciyata zan iya ce ina farin ciki kuma yanzu na san zan iya taimaka wa mutane. Ban taba tsammani zan iya yin hakan ba.

^ sakin layi na 13 Don karin bayani game da abin da ya sa Allah ya kyale munanan abubuwa suna faruwa, ka duba babi na 11 na littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.