Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada

Dā Ni Mugu Ne da Kuma Mai Son Yin Fada
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1974

  • ƘASAR HAIHUWA: MEZIKO

  • TARIHI: MAI SON YIN FAƊA

RAYUWATA A DĀ:

An haife ni a wani yanki mai kyau a jihar Tamaulipas da ake kira Ciudad Mante, a Meziko. A taƙaice dai, mazaunan birnin suna da kirki kuma masu karimci ne. Amma abin baƙin ciki, yawan zalunci ya sa zama a wurin yana da haɗari.

Ni ne na biyu cikin yara huɗu da iyayenmu suka haifa. Mu mabiyan Cocin Katolika ne kuma daga baya na zama ɗaya daga cikin mawaƙan cocin. Ina son in bauta wa Allah domin ba na son a shari’anta ni kuma a ƙone ni cikin wuta har abada.

Mahaifinmu ya yi watsi da mu sa’ad da na kai shekara biyar. Kuma hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Ban fahimci dalilin da ya sa ya yi watsi da mu ba. Mahaifiyata tana aiki na sa’o’i da yawa don ta biya bukatunmu.

Yanayin da muke ciki ya sa na bar zuwa makaranta kuma na soma tarayya da ‘yan iska da suka girme ni. Sun koya mini ashar da shan taba da sata da kuma yin faɗa. Da yake ni mai nuna ƙarfi ne, na koyi dambe da kokuwa kuma na horar da kaina a yin faɗa da kuma yin amfani da makamai. Na zama mai son yin faɗa sosai. Sau da yawa ina faɗa da bindiga kuma sai a raunata ni sosai har a yar da ni a kan titi ana zaton na mutu. Mahaifiyata tana baƙin ciki sosai a duk lokacin da ta same ni a wannan yanayin kuma tana kai ni asibiti!

A lokacin da na kai shekara 16, wani abokinmu mai suna Jorge ya ziyarce mu. Ya gaya mana cewa shi Mashaidin Jehobah ne kuma yana son ya ba mu wani albishiri. Sai ya soma yin amfani da Littafi Mai Tsarki don ya gaya mana abin da ya yi imani da shi. Ban taɓa karanta Littafi Mai Tsarki ba kuma na yi farin ciki sa’ad da na koyi sunan Allah, wato Jehobah da kuma nufinsa ga duniya. Jorge ya ce zai so ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mu kuma mun amince da hakan.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Da na koya cewa Littafi Mai Tsarki bai ce Allah zai ƙone mutane cikin wuta ba, sai hankalina ya kwanta. (Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5) Sa’ad da na koyi hakan, sai na daina tsoro cewa Allah zai ƙona ni cikin wuta. Bayan haka, sai na soma ganinsa a matsayin Uba mai ƙauna da yake son yaransa su ji daɗin rayuwa.

Sa’ad da na ci gaba da koyon Littafi Mai Tsarki, na fahimci cewa ina bukatar yin wasu canje-canje a halayena. Ina bukatar kasancewa da tawali’u kuma in daina yin faɗa. Shawarar da ke 1 Korintiyawa 15:33 ta taimaka mini. Ayar ta ce: “Zama da miyagu takan ɓata halaye na kirki.” Na gane cewa ina bukatar daina tarayya da ‘yan iska idan har ina so in gyara halina. Sai na soma yin abokai da ‘yan’uwa a ikilisiya waɗanda ba sa yin faɗa don su warware matsaloli amma suna amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

Wani nassi kuma da ya taimaka mini shi ne Romawa 12:​17-19. Ayoyin sun ce: “Kada ku sāka wa kowane mutum mugunta da mugunta. . . . Idan ya yiwu, ku zama lafiya da dukan mutane, gwargwadon iyawarku. Kada ku ɗauka wa kanku fansa, . . . gama an rubuta, ɗaukar fansa tawa ce; ni zan yi sakamako, in ji Ubangiji.” Na yarda cewa Jehobah zai magance rashin adalci a lokacin da ya ayyana. Kuma a hankali, na daina yin faɗa.

Ba zan taɓa manta da wani abin da ya faru wata rana sa’ad da nake dawowa gida ba. Wasu ‘yan iska da suke gāba da rukunin da nake a dā sun tare ni kuma shugabansu ya buge ni a baya sai ya ce, “Ka ceci kanka mana!” Nan da nan sai na yi addu’a ga Jehobah kuma na gaya masa ya taimake ni in jimre wannan gwajin. Ko da yake na ji haushi kuma na so in rama, amma ban rama ba. Washegari, sai na sake haɗuwa da shugabansu shi kaɗai. Sai na cika da fushi sosai, amma na sake yin addu’a ga Jehobah ya taimake ni in kame kaina. Da shugaban ya gan ni, sai ya zo wurina ya ce: “Ka gafarce ni don abin da na yi maka jiya. A gaskiya, ni ma ina son in zama kamar kai kuma ina son in koya Littafi Mai Tsarki.” Hakan ya ba ni mamaki sosai. Na yi farin ciki cewa na iya kame kaina! Kuma daga baya, sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi.

Amma abin baƙin ciki shi ne, mahaifiyata da ‘yan’uwa ba su ci gaba da nazarin ba. Duk da haka, na tsai da shawara cewa zan ci gaba da nazarin kuma ba zan bar kome ya hana ni yin hakan ba. Na san cewa yin tarayya da mutanen Allah zai kyautata rayuwata sosai ya kuma sa in kasance da ‘yan’uwa da suke ƙaunata. Na ci gaba da koyo kuma a shekara ta 1991, na yi baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah.

YADDA NA AMFANA:

A dā ni mugu ne da kuma mai son yin faɗa. Amma Kalmar Allah ta canja rayuwata. Yanzu ina wa duk wanda zai saurara wa’azin salama. Na yi shekaru 23 ina hidima na cikakken lokaci.

Na taɓa yin hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke Meziko. A wurin ne na haɗu wata ‘yar’uwa mai kirki da ake kira Claudia kuma mun yi aure a shekara ta 1999. Na gode wa Jehobah da ya ba ni wannan mata mai hankali!

Muna hidima a ikilisiyar da ake Yaren Kurame a ƙasar Meziko don mu taimaka wa kurame su san Jehobah. Daga baya, an tura mu zuwa ƙasar Belize don mu koya wa mutanen da ke wurin Littafi Mai Tsarki. Muna da duk abubuwan da muke bukata don mu kasance da farin ciki ko da yake mun sauƙaƙa rayuwarmu a nan. Ba ma yin da-na-sa-ni sam.

Daga baya, mahaifiyata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta yi baftisma. Ban da haka ma, yayana da matarsa da yaransu sun zama Shaidun Jehobah. Wasu cikin abokaina a dā waɗanda na koya musu Littafi Mai Tsarki ma suna bauta wa Jehobah yanzu.

Amma wasu cikin ‘yan’uwana sun mutu domin sun ƙi canja halayensu. Wataƙila da na mutu da a ce ban daina tarayya da su ba. Ina godiya ga Jehobah don ya jawo ni wurinsa kuma ya sa na san ƙungiyarsa. Ina kuma godiya ga bayinsa da suka yi haƙuri da ni yayin da suke koya mini in riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.