Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Yanzu Na Daina Raina Kaina”

“Yanzu Na Daina Raina Kaina”
  • Shekarar Haihuwa: 1963

  • Kasar Haihuwa: Meziko

  • Tarihi: Yaro mai kwana a titi; yana rena kansa

RAYUWATA A DĀ

 An haife ni a Ciudad Obregón a arewacin Meziko, ni ne na biyar a cikin yara tara da mahaifiyata ta haifa. Muna zama a gefen gari kuma mahaifina yana noma da kuma kiwon dabbobi. Mun ji dadin zama a wurin kuma a lokacin iyalinmu tana zaman lafiya da hadin kai. Abin bakin ciki shi ne, da nake dan shekara biyar, wata mahaukaciyar guguwa ta zo ta yi rugu-rugu da gonarmu. Hakan ya sa mun kaura zuwa wani gari.

 A wurin ne mahaifina ya soma samun kudi. Amma sai ya zama mashayi. Hakan ya shafi mu yara da kuma dangantakarsa da mahaifiyarmu. Mukan saci sigarinsa mu sha. Lokacin da nake shekara shida ne na soma buguwa da giya. Daga baya, iyayena sun rabu, kuma hakan ya sa yanayina ya dada muni.

 Mahaifiyata ta soma zama da wani mutum kuma ta kwashe mu zuwa gidansa. Mutumin ba ya ciyar da mu kuma mahaifiyarmu ba ta samun isashen kudi. Hakan ya sa ni da ’yan’uwana muka soma aiki, duk da haka kudin da muke samu ba ya isan mu. Nakan yi aikin shushaina, a wasu lokuta kuma, ina tallan burodi, da jaridu, da cingam, da dai sauransu. Nakan zagaya gari ina neman abinci a kwandon bolar masu kudi.

 Sa’ad da na kai shekara goma, sai wani mutum ya ce in zo mu rika aiki tare a bolar birnin. Na yarda kuma na bar makaranta da kuma gida. Abin da yake biya na a rana bai kai dala daya (dala daya a lokacin bai kai naira daya ba), amma yana ba ni abincin da muke samuwa a bolar. Kayan bolar ne na tattara na yi bukkar da nake kwana a ciki. Mutanen da suke zama a bolar suna yawan bakar magana kuma fasikai ne. Da yawa a cikinsu ’yan kwaya ne da mashaya. A wurin ne rayuwata ta tabarbare gaba daya, hakan ya sa na yi ta kuka kowace dare, kuma kullum ina cikin tsoro. Talauci da kuma rashin karatu ya sa na soma raina kaina. Na zauna a bolar har tsawon shekara uku, sa’an nan na kaura zuwa wata jiha a Meziko. A wurin na yi aiki a gonaki. Aikin ya kunshi tsinka furanni da kuma auduga, da tattara rake da kuma girbin dankali.

A irin wannan bolar ne na zauna har shekara uku

 Shekara hudu bayan haka sai na koma Ciudad Obregón. Wata antina da take bokanci ta ba ni daki a gidanta. A wurin, na soma munanan mafarkai da dare kuma hakan ya sa na yi bakin ciki sosai har ma na soma tunanin kashe kaina. Wata rana da dare na yi wa Allah addu’a kuma na ce: “Ubangiji, idan kana wanzuwa, ina so in san ka kuma in bauta maka har abada. Idan akwai addini na gaskiya, zan so in san addinin.”

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Ni mai son ibada ne sosai. Ko a lokacin da nake dan yaro, nakan je coci-coci, amma ban gamsu da abin da suke koyarwa ba. Babu ko daya a cikinsu da ya taimaka min in fahimci abin da ke Littafi Mai Tsarki. Wasu a cikinsu sun fi mai da hankali ga neman kudi ne kawai. Wasu shugabannin addinan kuma fasikai ne.

 Sa’ad da na kai shekara 19, maigidan yayata ya gaya min cewa Shaidun Jehobah sun nuna masa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da yin amfani da sifofi. Ya karanta min Fitowa 20:​4, 5. Wurin ya ce kar mu sassaka wani gunki. Aya ta 5 ta ce: “Ba za ka rusuna musu ba, ko ka yi musu sujada, gama ni Yahweh Allahnka, Allah ne mai bukatar cikakkiyar kaunarka.” Sai maigidan yayata ya tambaye ni ya ce: “Da a ce Allah yana mu’ujiza ta wurin gumakai ko yana so mu bauta masa ta wurin su, da zai ce kar mu sassaka su?” Tambayar ta sa na soma tunani. Daga baya, mun tattauna wasu batutuwa daga Littafi Mai Tsarki kuma na ji dadin tattaunawar da muke yi sosai.

 Wata rana sai ya kai ni taron Shaidun Jehobah. Na ji dadin abin da na gani da kuma ji a taron. Na ga cewa yara a wurin suna da ilimi sosai kuma suna magana ba tsoro a gaban jama’a! Sai na ce, ‘Ba karamin ilimi mutane suke kwasa a nan ba!’ Duk da cewa ba na aski a lokacin kuma adona a birkice yake, Shaidun sun marabce ni. Har wasu sun gayyace ni in zo in ci abinci a gidansu bayan taron!

 Sa’ad da nake nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah, na koyi cewa Jehobah, Allah ne mai kauna kuma ya damu da mu, ko da yaya yanayinmu yake. Ba ya nuna bambanci. (Ayyukan Manzanni 10:​34, 35) Hakan ya ba ni damar sanin Allah sosai, kuma na daina bakin ciki kamar dā.

YADDA NA AMFANA

 Rayuwata gaba daya ta soma canjawa. Na daina shan taba da giya kuma na daina bakar magana. Haushin da nake rike da shi a zuciyata tun ina dan yaro ya soma warwarewa kuma na daina yin munanan mafarkai. Yanzu na daina raina kaina kamar yadda nake yi a dā sakamakon irin wahalar da na sha sa’ad da nake karami, da kuma makarantar da ban yi sosai ba.

 Na auri matar da take kaunar Jehobah, kuma tana ba ni karfin gwiwa sosai. Yanzu ni mai kula da wani da’ira na Shaidun Jehobah ne. Aikina ya kunshi ziyartar wasu ikilisiyoyi don in karfafa da kuma koyar da ’yan’uwana Shaidun Jehobah. Na gode wa Allah sosai da ya koyar da ni ta wurin Littafi Mai Tsarki ya kuma taimaka min in kyautata rayuwata. Hakika, yanzu ba na daukan kaina a matsayin marar daraja.

Yanzu ni da matata muna taimaka wa mutane kamar yadda aka taimaka min