Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

Na Sami Arziki na Kwarai

Na Sami Arziki na Kwarai
  • Shekarar Haihuwa: 1968

  • Kasar Haihuwa: Amirka

  • Tarihi: Wani dan kasuwa da ya roki Allah ya ba shi arziki

RAYUWATA A DĀ

 An haife ni a birnin Rochester da ke jihar New York kuma ni dan Katolika ne a dā. Iyayena sun rabu a lokacin da nake shekara takwas. Saboda haka, daga Litinin zuwa Jumma’a nakan zauna da mahaifiyata a wata unguwar talakawa, sa’an nan in je wurin mahaifina a unguwar masu kudi ranar Asabar da Lahadi. Da na ga yadda mahaifiyata take shan wahala don ta kula da mu shida, na ce sai na yi kudi don in taimaka wa iyalinmu.

 Da yake mahaifina yana so in yi kudi, sai ya saka ni a makarantar da ake koyan yadda ake tafiyar da sana’ar otal. Na so hakan, kuma na dauka cewa Allah ya amsa addu’ata na yin arziki da kuma farin ciki. Na koyi tafiyar da sana’ar otal, kuma na yi shekara biyar ina koyan yadda ake tafiyar da kudaden kamfani sa’ad da nake aiki a wani otal na gidan caca a birnin Las Vegas a jihar Nevada.

Aikina ya kunshi kula da masu kudi da suke yin caca

 Sa’ad da nake dan shekara 22, an nada ni mataimakin shugaban otal na wani gidan caca. Mutane suna dauka na a matsayin mai arziki, nakan ci abinci mafi kyau kuma in sha giya mafi tsada. Abokaina da muke sana’a tare sukan ce mini, “Ka tuna cewa kudi shi ne abin da ya fi muhimmanci a duniya.” A ra’ayinsu, kudi ne yake sa mutum farin ciki.

 Aikina ya kunshi kula da masu kudi da suke zuwa yin caca a birnin Las Vegas. Duk da cewa suna da arziki sosai, da alama ba sa farin ciki. Ni ma na soma bakin ciki. Gaskiyar ita ce, yayin da nake dada yin kudi, sai na soma damuwa kuma ba na iya barci da kyau. Sai na soma tunanin kashe kaina. Sa’ad da na kasa samun gamsuwa a rayuwa, sai na roki Allah ya nuna mini wurin da zan sami farin ciki na gaskiya.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 A lokacin, ’yan’uwana mata biyu da suka zama Shaidun Jehobah sun kaura zuwa birnin Las Vegas. Ko da yake na ki karban littattafansu, na amince cewa zan rika karanta Littafi Mai Tsarki nawa tare da su. A cikin Littafi Mai Tsarki da nake da shi, an rubuta kalmomin Yesu da jar kala. ’Yan’uwana sun yi ta amfani da kalmomin Yesu suna yi mini wa’azi domin sun san cewa na amince da kome game da shi. Kari ga haka, na karanta Littafi Mai Tsarki da kaina.

 Da yawa daga cikin abubuwan da na karanta sun ba ni mamaki. Alal misali, Yesu ya ce: “Garin yin addu’a kuma kada ku yi ta maimaitawa ta banza, kamar yadda arna suke yi: gama suna tsammani bisa ga yawan maganarsu za a amsa masu.” (Matiyu 6:​7, Tsohuwar Hausa a Saukake) Kafin lokacin, wani firist ya ba ni hoton Yesu kuma ya ce mini idan na yi addu’o’i ga hoton, Allah zai ba ni duk kudin da nake so. Amma na fahimci cewa yin wannan addu’ar a kai a kai daya ne da maimaitawar banza da Littafi Mai Tsarki ya ambata. Kari ga haka, na karanta abin da Yesu ya fada, cewa: “Kada ku ce da kowane mutum a duniya ubanku: gama ɗaya ne Ubanku, shi na sama.” (Matiyu 23:9) Sai na soma tunani, ‘Me ya sa ni da sauran ’yan Katolika muke kiran firistocinmu “Fāda,” wanda ke nufin “Uba”?’

 Bayan da na karanta littafin Yakub ne na soma tunani sosai game da rayuwata. A sura 4, Yakub ya ce: “Ba ku sani ba cewa zaman abokin duniya yana daidai da zaman gāba da Allah? Gama duk mai kaunar duniya, ya mai da kansa mai gāba da Allah ke nan.” (Yakub 4:4) Aya ta 17 ce ma ta fi ba ni mamaki, ta ce: “Wanda ya san abin da ya kamata ya yi amma ya ki yi, ya yi zunubi ke nan.” Sai na kira ’yan’uwana kuma na gaya musu cewa zan bar aikin da nake yi domin yana sa ni yin abin da Littafi Mai Tsarki ya haramta, abubuwa kamar caca da hadama.

“Bayan da na karanta littafin Yakub ne na soma tunani sosai game da rayuwata”

 Na so in kyautata dangantakata da Allah da iyayena da kuma ’yan’uwana. Saboda haka, na yanke shawarar saukaka salon rayuwata. Amma bai yi mini sauki in yi wadannan canje-canjen ba. Alal misali, an gaya mini cewa za a kara mini matsayi kuma a ninka albashina sau biyu ko uku idan na ci gaba da yin aikin. Amma da na yi addu’a game da batun, sai na yanke shawara cewa ba zan ci gaba da yin irin wannan rayuwar ba. Na yi murabus kuma na gina wurin kwana da kuma wurin aiki a inda mahaifiyata take faka mota. Sai na soma sana’ar laminetin takardar abinci wa gidajen abinci.

 Duk da cewa Littafi Mai Tsarki ya taimaka mini in yanke shawarwari masu kyau a rayuwata, ban yarda in soma halartan taron Shaidun Jehobah ba. ’Yan’uwana sun tambaye ni ko akwai dalilin da ya sa ba na son Shaidun Jehobah. Sai na ce: “Domin Allahnku Jehobah yana raba kan iyali. Ranakun da zan iya kasancewa tare da ku su ne ranar bikin Kirsimati da ranar tuna haihuwa. Amma ba ku yin wadannan bukukuwa.” Sai daya daga cikinsu ta soma kuka kuma ta tambaye ni: “Me ya sa ba za ka kasance tare da mu a sauran ranaku a shekara ba? Muna so mu kasance tare da kai a koyaushe. Amma sai a ranakun nan ne kake so ka zo domin kana tunanin cewa ya zama maka dole.” Kalmominta sun ratsa zuciyata, sai ni ma na soma kuka.

 A lokacin ne na fahimci cewa na yi kuskure, domin Shaidun Jehobah suna kaunar iyalinsu. Sai na yanke shawarar halartan taronsu a Majami’ar Mulki. A wurin na hadu da wani dan’uwa da ya kware a koyar da Littafi Mai Tsarki mai suna Kevin kuma ya soma nazari da ni.

 Kevin da matarsa sun saukaka rayuwarsu don su sami damar koya wa mutane abin da ke Littafi Mai Tsarki. Sun tara kudi da zai ishe su yin tafiya zuwa Afirka da Amirka ta tsakiya domin su taimaka da aikin gina ofisoshin Shaidun Jehobah. Suna farin ciki sosai kuma suna kaunar juna. Sai na ce, ‘Irin rayuwar da nake so ke nan.’

 Kevin ya nuna mini wani bidiyo game da yadda yin hidima a wata kasa take sa mutum farin ciki, sai na yanke shawara cewa abin da zan yi ke nan. A 1995, bayan da na yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai na tsawon watanni shida, sai aka yi mini baftisma a matsayin Mashaidin Jehobah. Maimakon in roki Allah ya ba ni arziki, sai na soma rokon sa cewa: “Kada ka ba ni talauci ko dukiya.”​—Karin Magana 30:8.

YADDA NA AMFANA

 Yanzu ni mai arziki ne. Wannan arzikin ba don kudi ba ne amma don dangantakata da Allah da kuma irin rayuwa mai kyau da nake yi. Na auri wata ’yar’uwa mai hankali mai suna Nuria a kasar Honduras. Kuma tare mun yi hidima a kasar Panama amma yanzu muna hidima a kasar Meziko. Abin da Littafi Mai Tsarki ya fada cewa, “albarkar Ubangiji takan kawo wadata, ba ya kan hada ta da bakin ciki ba,” gaskiya ne.​—Karin Magana 10:​22, Tsohuwar Hausa a Saukake.