Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Aikata Laifi da Son Kudi Sun Cutar da Ni”

“Aikata Laifi da Son Kudi Sun Cutar da Ni”
  • Shekarar Haihuwa: 1974

  • Kasar Haihuwa: Albania

  • Tarihi: Barawo, mai sayar da kwayoyi, dan fursuna

RAYUWATA A DĀ

 An haife ni a Tiranë, babban birnin kasar Albania. Mahaifina mutumin kirki ne kuma yakan yi aiki na dogon lokaci don ya sami abin kula da mu. Amma ba ya samun kudin da zai ishe mu. A lokacin da nake karami, ganin talaucinmu yakan sa ni bakin ciki sosai. A lokacin da nake yaro, a yawancin lokuta ba na samun takalmi kuma ba na samun isasshen abinci.

 Na soma sata sa’ad da nake karami. Na dauka cewa ina taimaka wa iyalinmu yin tanadin abin da suke bukata ne. A karshe, ’yan sanda sun kama ni. A shekara ta 1988 a lokacin da nake dan shekara 14, mahaifina ya tura ni zuwa makarantar da ake gyara halayen yara. Na yi shekaru biyu a wurin kuma na koyi aikin walda. Da na bar makarantar, na so in yi rayuwa yadda ya kamata kuma in daina yin mugayen abubuwa, amma ban sami aiki ba. Yawancin mutane ba su da aikin yi a lokacin domin kasar Albania tana fama da matsalolin siyasa. Hakan ya sa ni bakin ciki sai na soma cudanya da abokaina na dā kuma na koma yin sata. A karshe, an kama ni da abokaina kuma aka yanke mana hukuncin yin shekara uku a kurkuku.

 Bayan an sake ni daga kurkuku, na ci gaba da aikata laifi. Tattalin arzikin kasar Albania ya rugurguge gaba daya kuma kasar ta kasance a cikin tashin hankali. A wannan lokacin, na samu kudi sosai ta wajen yin mugayen abubuwa. Bayan wani fashi da muka yi da aka kama abokaina biyu, na gudu na bar kasar domin kada a kama ni a saka ni a kurkuku na dogon lokaci. A lokacin, na riga na auri matata Julinda kuma mun haifi da.

 Mun tsinci kanmu a Ingila. Na so in soma sabon rayuwa da matata da dana, amma ya yi mini wuya in canja halayena. Sai na koma aikata laifi, na soma sayar da mugayen kwayoyi kuma hakan ya sa na soma samun kudi sosai.

 Mene ne ra’ayin Julinda game da sana’ata na sayar da mugayen kwayoyi a lokacin? Bari ta gaya muku: “A lokacin da nake girma a kasar Albania, nakan yi tunanin ranar da zan fita daga talauci. Na kasance a shirye in yi kome don in sami rayuwa mai inganci. Na dauka cewa kudi zai inganta rayuwarmu, don haka na goyi bayan Artan sa’ad da yake karyace-karyace da sata da kuma sayar da mugayen kwayoyi, duk dai abin da zai yi don ya sami kudi.”

“Na goyi bayan Artan sa’ad da yake karyace-karyace da sata da kuma sayar da mugayen kwayoyi.”—Julinda

 A shekara ta 2002 rayuwarmu ta canja farat daya, kuma shirin da muke yi na samun kudi ya lalace. An kama ni dauke da mugayen kwayoyi sai aka sake kai ni kurkuku.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA

 Littafi Mai Tsarki ya soma yin tasiri a kaina ba da sani na ba. A farkon shekara ta 2000, Julinda ta hadu da Shaidun Jehobah kuma ta soma nazari da su. Ban so in tattauna Littafi Mai Tsarki da kowa ba domin na dauka cewa ba zan ji dadin yin hakan ba. Amma matata ta ji dadin yin hakan. Ta ce: “Iyalina masu ibada ne sosai, kuma tun ina karama ina son Littafi Mai Tsarki kuma ina daraja shi. Na dade ina so in san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, kuma na yi farin cikin yin nazari da Shaidun Jehobah. Koyarwar Littafi Mai Tsarki da yawa sun burge ni. Abubuwan da na koya sun taimaka mini in yi wasu gyara a rayuwata. Duk da haka, na ci gaba da tunanin cewa kudi ne zai sa mu farin ciki, har sai da aka kama Artan. Hakan ya sa na canja ra’ayina gabaki daya. A lokacin ne na gane cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da kudi gaskiya ne. Mun yi iya kokarinmu don mu yi kudi, amma duk da haka ba mu yi farin ciki ba. Sai na gano cewa ina bukatar in bi dukan ka’idodin Allah.”

 A shekara ta 2004, an sake ni daga kurkuku, kuma jim kadan bayan haka, sai na yi kokari in koma sana’ar sayar da mugayen kwayoyi. Amma ra’ayin matata ya riga ya canja, kuma abin da ta gaya mini ya sa ni tunani. Ta ce: “Ba na son kudinka kuma ba. Ina so ka kasance tare da ni kuma ina so yarana ma su kasance da babansu.” Abin da ta fada ya ba ni mamaki, amma na san cewa gaskiya ne ta fada. Na yi shekaru da yawa ba na tare da iyalina. Na yi tunanin dukan wahalolin da na sha domin ina neman kudi ta mummunar hanya. Don haka, na yanke shawarar canja rayuwata kuma na daina tarayya da abokaina na dā.

 Abin da ya fi sa ni yin tunanin canja rayuwata shi ne lokacin da na halarci taron Shaidun Jehobah tare da matata da yaranmu biyu. Yadda mutane a wurin suka marabce ni da zuciya daya ya burge ni sosai. Sai na soma nazarin Littafi Mai Tsarki.

A dā na dauka cewa idan mun yi kudi sosai, za mu yi farin ciki

 A Littafi Mai Tsarki, na koyi cewa ‘kaunar kudi ita ce tushen kowace irin mugunta. A cikin marmarin yin arziki da sauri, wadansu sun . . . jawo wa kansu bakin ciki iri-iri masu zafi.’ (1 Timoti 6:9, 10) Abubuwan da na fuskanta sun tabbatar mini cewa abin da wannan ayar ta fada gaskiya ne! Na yi da-na-sani domin irin rayuwar da na yi a dā da kuma irin bakin ciki da na jawo wa kaina da kuma iyalina. (Galatiyawa 6:7) Da na gano yadda Jehobah da Dansa Yesu Kristi suke kaunar mu, sai na soma canja halayena. Na daina mai da hankali ga kaina kuma na soma saka bukatun wasu a kan gaba maimakon nawa. Hakan ya sa na soma zama tare da iyalina sosai.

YADDA NA AMFANA

 Na amfana sosai daga bin wannan shawarar Littafi Mai Tsarki cewa: “Ku yi nesa da halin son kudi, ku kuma [gamsu] da abin da kuke da shi.” (Ibraniyawa 13:5) Yanzu ina da kwanciyar hankali kuma zuciyata ta daina damu na. Hakan ya sa ni farin cikin da ban taba yi ba. Dangantakata da matata ta dada danko kuma mun dada kusantar juna a iyalinmu.

 A dā na dauka cewa idan mun yi kudi sosai, za mu yi farin ciki. Yanzu na ga yadda aikata laifi da son kudi suka cutar da ni. Mu ba masu kudi ba ne yanzu, amma muna da abin da ya fi kudi daraja, wato dangantaka mai kyau da Jehobah. Bauta wa Jehobah tare da iyalina yana sa mu farin ciki.

Ni da iyalina a wani taron yanki na Shaidun Jehobah