Koma ka ga abin da ke ciki

LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE

“Na Daina Dauka Cewa Zan Iya Gyara Duniya”

“Na Daina Dauka Cewa Zan Iya Gyara Duniya”
  • SHEKARAR HAIHUWA: 1966

  • KASAR HAIHUWA: FINLAND

  • TARIHI: MAI FAFUTIKAR KĀRE HAKKIN ’YAN ADAM

RAYUWATA A DĀ:

Ni mai son halittun Allah ne tun ina karami. Dukanmu a gidanmu mukan so zuwa yawo a daji da kuma tafkuna masu kyaun gani da suka kewaye garinmu, wato Jyväskylä, a Yankin Finland ta Tsakiya. Kari ga haka, ina son dabbobi sosai. Da nake karami, nakan ji kamar in rungumi kowane kule da kare da na gani! Da na yi girma, na ga cewa mutane suna wulakanta dabbobi, kuma abin ya dame ni. Da shigewar lokaci, na shiga wata kungiya da ke kāre hakkin dabbobi, a wurin na hadu na masu irin ra’ayina.

Mun yi ta kokarin sa a daina wulakanta dabbobi. Mun yi ta fadakar da mutane, mun yi zanga-zanga kuma mun nuna rashin yardar mu da masu sayar da fatar dabbobi da wadanda suke amfani da dabbobi wajen yin gwaje-gwaje. Har mun kafa kungiyar kāre dabbobi. Amma mun yi ta samun matsala da jami’an tsaro domin wasu matakan da muka dauka suna ta da hankalin jama’a. Hakan ya sa an kama ni sau da yawa kuma aka kai ni kotu.

Amma ba dabbobi ne kadai na damu da su ba, na kuma damu da wasu matsalolin da nake gane a duniya. Don haka, na shiga wasu kungiyoyin kāre hakkin dan Adam da mahalli kamar su Amnesty International da Greenpeace. Na yi amfani da dukkan karfina wajen tallafa wa kungiyoyin nan. Na yi kokarin kāre hakkin talakawa, da masu fama da yunwa, da kuma wadanda ba su da mai taimako.

Amma da shigewar lokaci, na gane cewa ba zan iya gyara duniyar nan ba. Ko da yake kungiyoyin nan sukan yi kokari wajen magance wasu kananan matsaloli, manyan matsalolin sai dada karuwa suke yi. Sai na ga kamar akwai wani mugun ruhun da yake iko da duniyar nan, ga shi ba wanda ya damu da abin da ke faruwa. Abin ya fi karfina.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:

Da na ga cewa ba zan iya gyara kome ba, sai na soma bakin ciki kuma na soma tunani game da Allah da kuma Littafi Mai Tsarki. Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a dā. Na san Shaidun Jehobah mutanen kirki ne domin sun nuna min kauna, amma ni ne ban so in canja halina a lokacin ba. Yanzu kam na canja ra’ayina.

Na soma karanta Littafi Mai Tsarki. Kuma hakan ya taimaka min sosai. Na ga nassosi da dama da suka umurce mu mu kula da dabbobi. Alal misali, Karin Magana 12:10 ta ce: “Mai adalci yana kula da lafiyar dabbobinsa.” Kuma na gano cewa ba Allah ba ne yake jawo matsalolin da ke duniya. A maimakon haka, rashin bin umurnin Allah ne yake sa matsaloli su yi ta karuwa a duniya. Da na ga cewa Allah mai kauna ne da kuma hakuri, hakan ya ratsa zuciyata.​—Zabura 103:​8-14.

A daidai wannan lokacin ne na aika a turo min littafin nan, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Ba da dadewa ba, sai wasu ma’aurata Shaidun Jehobah suka zo gidana kuma suka ce za su so su soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Na amince kuma na soma zuwa taro a Majami’ar Mulki. Hakan ya sa na soma jin dadin abubuwan da nake koya.

Littafi Mai Tsarki ne ya taimaka min na canja halina sosai. Na daina shan taba sigari da buguwa da giya. Na soma ado da kyau kuma na daina yi wa mutane bakar magana. Na kuma soma yi wa hukumomi biyayya. (Romawa 13:1) Sa’an nan na daina yin fasikanci duk da cewa na saba yin hakan.

Abin da ya fi min wuya in bari shi ne, goyon bayan kungiyoyin da suke kokarin kāre hakkin ’yan Adam da dabbobi. Bai kasance min da sauki ba don ina ganin idan na bar kungiyoyin nan zai zama kamar na ci amanarsu. Amma a hankali na gane cewa Mulkin Allah ne kadai zai magance matsalolin duniyar nan. Don hakan, na tsai da shawarar goyon bayan Mulkin Allah da dukan zuciyata da kuma koya wa mutane game da shi.​—Matiyu 6:33.

YADDA NA AMFANA:

A lokacin da nake yunkurin kāre hakkin ’yan Adam, nakan yi wa mutane kallon masu kirki ko mugaye, kuma nakan yaki wadanda na dauke su a matsayin mugaye. Amma yanzu, Littafi Mai Tsarki ya sa ba na tsanan mutane. A maimakon hakan, ina kokari in kaunace kowa. (Matiyu 5:44) Wata hanyar da nake nuna wa mutane wannan kaunar ita ce ta wajen koya musu game da Mulkin Allah. Ina farin cikin ganin yadda wannan aikin alherin yake sa mutane su zauna lafiya da juna, su yi farin ciki, kuma su kasance da bege.

Barin kome a hannun Jehobah, ya sa na sami kwanciyar hankali. Na san cewa, Mahaliccinmu, ba zai bari a ci gaba da wulakanta mutane da dabbobi har abada ba, kuma ba zai bar mutane su hallaka duniyar nan ba. A maimakon haka, nan ba da dadewa ba, zai yi amfani da Mulkinsa wajen gyara duk barnar da aka yi a duniya. (Ishaya 11:​1-9) Sanin hakan da kuma taimaka wa mutane su yi imani da wannan gaskiya yana sa ni farin ciki sosai. Na daina dauka cewa zan iya gyara duniya.