Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA HUƊU

Ya Koyi Nuna Jin Ƙai

Ya Koyi Nuna Jin Ƙai

1. Wace irin tafiya ce Yunana zai yi, kuma yaya ya ji game da birnin da za shi?

YUNANA yana da doguwar tafiya da zai yi kuma hakan za ta ba shi zarafin yin tunani sosai. Zai yi tafiyar da ta fi nisan mil 500 da ƙafa kuma hakan zai ɗauke shi wajen wata ɗaya ko fiye da hakan. Idan ya bi yanke zai fuskanci haɗarurruka, amma idan ya bi doguwar hanya, zai sha tafiya kuma zai ƙetare ƙwari da tuddai masu yawa. Wataƙila zai bi ta Hamadar Suriya kuma ya haye kogin Yufiretis, sai ya nemi masauki a garuruwa da ƙauyukan da bai saba zama ba da ke Suriya da Mesopotamiya da kuma Assuriya. Da shigewar kwanaki, Yunana ya yi alhini sosai yayin da yake kusantar birnin Nineba da ya ji tsoron zuwa a dā.

2. Ta yaya Jehobah ya sa Yunana ya yi aikin da ya ba shi?

2 Yunana ya san cewa wajibi ne ya yi wannan aikin. Ya yi ƙoƙari ya gudu a dā, amma hakan bai yiwu ba. Kamar yadda aka ambata a babin da ya gabata, Jehobah ya koya wa Yunana darasi ta hanyar hadari a teku da kuma yadda ya cece shi daga cikin babban kifi. Bayan kwanaki uku, kifin ya yi aman Yunana a bakin teku. A yanzu, yana a shirye ya yi biyayya ga Jehobah domin ya ga abubuwan ban al’ajabi da suka faru.—Yunana, surori na 1 da 2.

3. Wane hali ne Jehobah ya nuna wa Yunana, kuma hakan ya sa a yi wace tambaya?

3 Sa’ad da Jehobah ya umurci Yunana ya je Nineba a wannan karin, annabin ya yi biyayya kuma ya bi ta gabas. (Karanta Yunana 3:1-3.) Shin horon da Jehobah ya yi masa ya canja halinsa kuwa? Alal misali, Jehobah ya yi masa jin ƙai ta wurin hana ruwa ya cinye shi, bai hukunta shi ba don tawayen da ya yi kuma ya sake ba shi zarafin yin wannan aikin. Shin dukan waɗannan abubuwa sun sa Yunana ya zama mai jin ƙai? Yana yi wa ’yan Adam ajizai wuya su zama masu jin ƙai. Bari mu ga abin da za mu iya koya daga Yunana.

Saƙon Hukunci da Kuma Sakamako da Bai Zata Ba

4, 5. Me ya sa Jehobah ya kira Nineba “babban birni,” kuma mene ne hakan ya koya mana game da shi?

4 Yunana bai fahimci dalilin da ya sa birnin Nineba yake da muhimmanci ga Jehobah ba. A cikin littafin Yunana, Jehobah ya kira Nineba “babban birni” har sau uku. (Yun. 1:2; 3:2; 4:11) Me ya sa wannan birnin yake da muhimmanci ga Jehobah?

5 Nineba yana cikin birane na farko da Nimrod ya kafa bayan Rigyawar. Babban birni ne da ke da wasu birane a ciki kuma mutum zai yi tafiyar kwana uku kafin ya kai ƙarshensa. (Far. 10:11; Yun. 3:3) Nineba yana da manyan haikalai da garu da kuma gidaje masu kyau. Amma, mutanen birnin ne suka fi muhimmanci ga Jehobah, ba waɗannan abubuwa ba. Nineba ya fi sauran birane na lokacin jama’a. Duk da muguntar mutanen, Jehobah ya damu da su. Yana ƙaunar kowane ɗan Adam, kuma yana so su tuba su yi abin da ya dace.

Yunana ya lura cewa Nineba babban birni ne da ake yawan miyagun ayyuka

6. (a) Me ya sa wataƙila birnin Nineba ya tsoratar da Yunana? (Ka kuma duba hasiya.) (b) Wane misali ne Yunana ya kafa mana ta yadda ya yi wa’azi?

6 Yunana ya ƙara tsorata sa’ad da ya shiga birnin Nineba domin mutane fiye da 120,000 ne suke ciki. * Ya yi tafiya na kwana ɗaya har ya kai sashen da mutane suka fi yawa a birnin, wataƙila domin ya samu wurin da ya dace don idar da saƙonsa. Ta yaya zai yi wa waɗannan mutanen magana? Shin ya koyi yaren Assuriyawa ne? Ko kuma Jehobah ya sa ya yi hakan ta mu’ujiza? Ba mu sani ba. Wataƙila Yunana ya yi wa’azi da Ibrananci kuma wani yana fassara wa mutanen Nineba. Ko ta yaya dai, saƙonsa yana da sauƙi kuma mai yiwuwa mutane ba za su so saƙon ba, don ya ce: ‘Da sauran kwana arba’in tukuna, kāna a kaɓantar da Nineba.’ (Yun. 3:4) Yunana ya yi maganar da gaba gaɗi kuma ya yi ta maimaitawa. Ta yin hakan, ya nuna cewa yana da ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya sosai. A yau, Kiristoci suna bukatar su kasance da waɗannan halayen fiye da dā.

7, 8. (a) Mene ne mutanen Nineba suka yi sa’ad da suka ji saƙon Yunana? (b) Mene ne sarkin Nineba ya yi sa’ad da ya ji saƙon Yunana?

7 Wataƙila Yunana yana ganin cewa mutanen za su yi fushi kuma su yi faɗa da shi. Amma, wani abin mamaki ya faru. Mutanen sun saurare shi! Saƙonsa ya yaɗu kamar wutar daji. Ba da daɗewa ba, dukan mutanen birnin suna magana game da saƙon hukunci da Yunana ya idar. (Karanta Yunana 3:5.) Masu arziki da talakawa da ƙaƙƙarfa da raunanu da yara da kuma manya da ke birnin sun tuba. Dukansu sun yi azumi. Ba da daɗewa ba, sarkin ya ji abin da yake faruwa.

Yunana yana bukatar gaba gaɗi da bangaskiya don ya yi wa’azi a birnin Nineba

8 Sarkin ma ya tuba sa’ad da ya ji shelar Yunana. Don ya ji tsoron Allah, sai ya tashi daga karagarsa kuma ya tuɓe alkyabbarsa, ya saka tsummokara, “ya zauna cikin toka.” Sarkin da kuma “hakimansa” suka sa aka yi shelar azumi. Ya ba da umurni cewa kowa ya saka tsumma, har da dabbobi. * Sarkin ya amince cewa mutanensa azzalumai ne. Ya yi bege cewa Allah na gaskiya zai ji ƙansu tun da ya ga cewa sun tuba, ya ce: “Allah za ya juya, . . . ya bar zafin fushinsa, kada mu lalace.”—Yun. 3:6-9.

9. Mene ne masu sūka suka ce game da mutanen Nineba, amma yaya muka san cewa hakan ba daidai ba ne?

9 Wasu masu sūkar Littafi Mai Tsarki sun yi shakkar cewa mutanen Nineba sun tuba nan da nan. Amma, wasu masanan Littafi Mai Tsarki sun ce mutanen dā masu camfi da kuma saurin canja halinsu suna iya yin hakan. Buga da ƙari, mun san cewa masu sūka sun yi kuskure, domin daga baya Yesu Kristi ya ambata yadda mutanen Nineba suka tuba. (Karanta Matta 12:41.) Yesu ya san abin da yake faɗi, gama yana sama kuma ya ga sa’ad da waɗannan abubuwan suke faruwa. (Yoh. 8:57, 58) A gaskiya, bai kamata mu zata cewa mutane ba za su iya tuba ba, ko da wane irin mugunta ne suke yi. Jehobah ne kaɗai ya san zuciyar mutum.

Jin Ƙan Allah da Hukuncin ’Yan Adam

10, 11. (a) Mene ne Jehobah ya yi sa’ad da mutanen Nineba suka tuba? (b) Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah bai yi kuskure a shawarar da ya yanke ba?

10 Mene ne Jehobah ya yi sa’ad da mutanen Nineba suka tuba? Daga baya Yunana ya ce: “Allah kuwa ya ga ayyukansu, da suka juya ga barin mugun tafarkinsu; Allah kuwa ya tuba ga barin masifar da ya ce za ya yi masu; ba ya kuwa aikata ba.”—Yun. 3:10.

11 Shin hakan yana nufin cewa Jehobah ya yi kuskure da ya ce zai hukunta mutanen Nineba? A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce shari’unsa daidai ne. (Karanta Kubawar Shari’a 32:4.) Jehobah ya daina fushi da mutanen Nineba domin ya ga cewa sun tuba kuma bai dace ya hukunta su ba. Ya tsai da shawara cewa zai yi musu jin ƙai.

12, 13. (a) Ta yaya Jehobah ya nuna cewa yana da sauƙin hali, yana canja ra’ayinsa dangane da irin yanayin kuma shi mai jin ƙai ne? (b) Me ya sa annabcin Yunana ba ƙarya ba ce?

12 Jehobah ba azzalumi ba ne da ba ya damuwa da mutane kamar yadda shugabannan addinai suke koyarwa. Akasi, yana da sauƙin hali da daidaita a kowane irin yanayi kuma shi mai jin ƙai ne. Kafin ya hukunta miyagu, yakan aiki bayinsa su gargaɗar da su, domin yana ɗokin ganin sun tuba kuma sun canja tafarkinsu kamar mutanen Nineba. (Ezek. 33:11) Jehobah ya gaya wa annabi Irmiya: “Kadan na yi shawara a kan wata al’umma, ko kuwa a kan wani mulki, a tumɓuke, a rushe, a hallaka; idan a loton nan wannan al’umma, wadda na ambace ta, ta juya ga barin muguntarsu, ni ma in tuba ga barin aikin masifa da na ƙudurta musu.”—Irm. 18:7, 8.

13 Shin Yunana ya yi ƙaryan annabci ne? A’a, domin ya gargaɗar da mutanen game da abin da zai faru idan ba su tuba ba. An ba da wannan gargaɗin domin mugun tafarkin mutanen Nineba kuma sun tuba daga baya. Idan mutanen Nineba suka koma gidan jiya, Allah zai hukunta su kamar yadda ya ce kuma abin da aka yi musu ke nan daga baya.—Zaf. 2:13-15.

14. Mene ne Yunana ya yi sa’ad da Jehobah ya yi wa mutanen Nineba jin ƙai?

14 Mene ne Yunana ya yi sa’ad da ba a hukunta mutanen Nineba a lokacin da yake sa rai ba? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abin ya ɓata zuciyar Yunana ƙwarai, har ya yi fushi.” (Yun. 4:1) Yunana ya yi addu’a kamar yana tsauta wa Allah Maɗaukaki! Ya ce da ya sani da bai je aikan ba. Ya yi da’awa cewa ya san Jehobah ba zai hukunta mutanen Nineba ba, shi ya sa ya yi niyyar gudu zuwa Tarshish. Sai ya ce ya fi masa ya mutu maimakon ya kasance da rai.—Karanta Yunana 4:2, 3.

15. (a) Mene ne wataƙila ya sa Yunana fushi sosai? (b) Yaya Jehobah ya bi da annabinsa da ke baƙin ciki?

15 Mene ne yake damun Yunana? Ba mu san zuciyarsa ba, amma mun san cewa ya yi wa mutanen Nineba shelar hukunci. Kuma sun gaskata cewa abin da ya faɗa zai faru, amma hakan bai faru ba. Shin ya ji tsoro cewa za su yi masa ba’a ko kuma su ce shi annabin ƙarya ne? Yunana bai yi farin ciki ba don mutanen sun tuba ko kuma don Jehobah ya yi musu jin ƙai. Maimakon haka, kamar ya ƙara yin fushi, ya tausaya wa kansa kuma ya damu cewa an ɓata sunansa. Duk da haka, Allah mai jin ƙai ya ga cewa wannan annabinsa da ke baƙin ciki yana da halin kirki. Maimakon Jehobah ya hukunta Yunana, ya yi masa wata tambaya da za ta sa shi tunani. Ya ce: “Daidai ne ka yi fushi?” (Yun. 4:4, Littafi Mai Tsarki) Shin Yunana ya amsa ne? Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba.

16. Ta yaya wasu mutane suke ƙi da shawarar Allah, kuma mene ne muka koya daga misalin Yunana?

16 Yana da sauƙi mu ce abin da Yunana ya yi bai dace ba, amma ya kamata mu tuna cewa ’yan Adam ajizai suna yawan ƙi da shawarar da Allah ya yanke. Wasu sun ce ya kamata Jehobah ya hana wani tsautsayi faruwa ko ya hukunta mugaye nan da nan ko kuma ya kawo ƙarshen wannan duniyar tun da daɗewa. Amma, misalin Yunana ya koya mana cewa Jehobah ba ya yin kuskure kuma duk sa’ad da muka ƙi da shawararsa, mu ne muke bukatar mu daidaita ra’ayinmu, ba shi ba.

Jehobah Ya Koya wa Yunana Darasi

17, 18. (a) Mene ne Yunana ya yi bayan ya bar birnin Nineba? (b) Ta yaya mu’ujizar da Jehobah ya yi ta shafi Yunana?

17 Sa’ad da annabin nan mai baƙin ciki ya bar Nineba, bai koma gida ba, amma ya haura tuddai da ke gabashin yankin. Sai ya yi ɗan rumfa da zai zauna a ciki ya ga abin da zai faru da birnin Nineba. Wataƙila yana ganin cewa har ila za a halaka birnin. Ta yaya Jehobah zai koya wa wannan mutumin da ba ya gafartawa muhimmancin nuna jin ƙai?

18 Jehobah ya sa itacen duma ya tsiro farat ɗaya kuma ya yi ganyaye sosai. Washegari, Yunana ya ga cewa wannan itacen ya fi rumfarsa inuwa, sai “ya yi murna ƙwarai,” wataƙila yana zato wannan mu’ujizar alama ce cewa Allah ya amince da shi kuma ya albarkace shi. Jehobah ya tanadar wa Yunana rumfa da ta kāre shi daga zafin rana, ya kuma sa ya daina fushi amma ba shi ke nan ba, yana son ya koya masa wani darasi na musamman. Tun da yake Allah yana so ya sa Yunana ya yi tunani, sai ya sake yin wasu mu’ujizai. Jehobah ya sa tsutsa ta cinye itacen duman har ya yi yaushi, sai ya sa “iskan gabas mai-ƙuna” ya huro, har Yunana ya kusan “suma” don zafi. Ya fusata sosai har ya so ya mutu.—Yun. 4:6-8.

19, 20. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da itacen duma don ya koya wa Yunana darasi?

19 Jehobah ya sake tambayar Yunana ko fushin da yake yi don itacen duman da ya mutu ya dace. Maimakon ya tuba, Yunana ya ba da hujja, ya ce: “Ya yi kyau na yi fushi har mutuwa.” Yanzu lokaci ya yi da Jehobah zai bayyana darasin dalla-dalla.—Yun. 4:9.

Allah ya yi amfani da itacen duma don ya koya wa Yunana nuna jin ƙai

20 Allah ya taimaka wa Yunana ya yi tunani. Ya ce masa ya ji tausayin itacen duma da ya yi girma farat ɗaya kawai, wanda bai shuka ba kuma bai sa ya tsira ba. Sai Allah ya daɗa cewa: “Ni kuwa ba zan ji tausayin [Nineba], babban birnin nan ba, wadda mutum da ke cikinta sun fi zambar ɗari da ashirin waɗanda ba su iya rarrabe hannun damansu da hagu ba; da kuwa dabbobi dayawa?”—Yun. 4:10, 11. *

21. (a) Wane darasi ne Jehobah ya koya wa Yunana? (b) Ta yaya labarin Yunana zai taimaka mana mu bincika kanmu?

21 Ka fahimci abin da Jehobah yake nufi da wannan misalin kuwa? Yunana bai yi kome ba don ya kula da wannan itacen duma. Amma, Jehobah ne ya halicci mutanen Nineba kuma ya kula da su kamar yadda yake wa dukan halittunsa a duniya. Yaya Yunana zai daraja itacen duma fiye da ’yan Adam 120,000 da dukan dabbobinsu? Shin hakan ba son kai ba ne? Ya ji tausayin itacen duma don ya amfane shi. Shin ba son kai ba ne ya sa ya fusata don yana ganin cewa yadda aka nuna wa mutanen Nineba jin ƙai zai ɓata sunansa? Labarin Yunana zai taimaka mana mu bincika halinmu. Waye ne cikinmu zai ce bai taɓa son kai ba? Ya kamata mu yi hamdala cewa Jehobah yana koyar da mu cikin haƙuri don mu daɗa zama masu tausayi da jin ƙai kamar sa.

22. (a) Ta yaya gargaɗin da Jehobah ya yi wa Yunana game da nuna jin ƙai ya shafe shi? (b) Wane darasi ne dukanmu muke bukatar mu koya?

22 Shin Yunana ya koyi darasin kuwa? Da tambayar da Jehobah ya yi ne aka kammala littafin Yunana. Saboda haka, wasu masu sūka suna iya cewa Yunana bai ba da amsar ba. Amma da yake Yunana ne ya rubuta wannan littafin da kansa, za mu iya cewa ya ba da amsar. Ka kwatanta a zuci yadda wannan annabin da ya riga ya koma ƙasarsu yake rubuta wannan labarin. Ka kuma kwatanta a zuci yadda wannan dattijo mai hikima da tawali’u yake kaɗa kansa, yayin da yake rubutu game da kurakuransa da tawayensa da kuma yadda ya ƙi nuna jin ƙai. Hakika, Yunana ya koyi darasi mai muhimmanci daga gargaɗin Jehobah. Ya koyi nuna jin ƙai. Shin za ka yi koyi da shi kuwa?—Karanta Matta 5:7.

^ sakin layi na 6 An kimanta cewa Samariya babban birnin ƙabila goma na Isra’ila yana da mazauna 20,000 zuwa 30,000 a zamanin Yunana. Hakan bai kai rabin-rabi na mutanen da ke Nineba ba. A zamanin Yunana, wataƙila Nineba ne birni mafi girma a duniya.

^ sakin layi na 8 Mutane suna iya ganin cewa hakan ba zai iya faruwa ba, amma ya taɓa faruwa a zamanin dā. Herodotus, ɗan tarihi Bahelani ya ce mutanen Fasiya na dā da dabbobinsu sun yi makokin wani sanannen janar.

^ sakin layi na 20 Sa’ad da Allah ya ce mutanen Nineba ba su iya rarrabe tsakanin hannun damansu da hagu ba, yana nufin cewa ba su san mizanansa ba.

Ko da yake saƙon Yunana ba irin wanda mutane za su so ji ba, amma yana da sauƙin fahimta

Allah yana ɗokin ganin miyagu sun tuba kamar mutanen Nineba