Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA TAKWAS

Ya Jimre da Yanayin da Bai Yi Tsammani Ba

Ya Jimre da Yanayin da Bai Yi Tsammani Ba

1. Me ya sa ake makoki a Shiloh?

SAMA’ILA ya ga mutane da yawa a Shiloh suna ta makoki. Mata da yara nawa ne suke kuka domin sun samu labari cewa mazansu da ’ya’yansu da kuma ’yan’uwansu ba za su sake dawowa gida ba? Ba mu san amsar dalla-dalla ba. Amma mun san cewa Filistiyawa sun kashe sojojin Isra’ila guda dubu huɗu a yaƙi, kuma daga baya sun ƙara kashe sojoji dubu talatin.—1 Sam. 4:1, 2, 10.

2, 3. Waɗanne bala’i ne suka jawo wa Shiloh kunya da kuma rashin ɗaukaka?

2 Wannan dai ɗaya ne cikin bala’in da suka fuskanta. Miyagun ’ya’yan Eli Babban Firist, Hophni da Finehas sun fita da sanduƙin alkawari daga Shiloh. Ana ajiye wannan Sanduƙin a cikin wuri mafi tsarki a mazaunin, kuma hakan alama ce cewa Allah yana tare da su. Amma mutanen suka kai Sanduƙin bakin dāga domin suna ganin zai kāre su kuma ya sa su yi nasara. Sai Filistiyawa suka kwace Sanduƙin kuma suka kashe Hophni da Finehas.—1 Sam. 4:3-11.

3 An yi shekaru da yawa ana daraja mazaunin da ke Shiloh sosai saboda Sanduƙin da ke cikinsa. Amma, yanzu Sanduƙin ya bi ruwa. Sa’ad da aka gaya wa Eli wanda ɗan shekara 98 ne a lokacin wannan labarin, sai ya faɗo daga kujerarsa ta baya ya mutu. A ranar kuma, matar Finehas ta rasu sanadin haihuwa. Kafin ta rasu, ta ce: “Ɗaukaka ta rabu da Isra’ila.” Hakika, Shiloh ba zai ƙara kasancewa kamar dā ba.—1 Sam. 4:12-22.

4. Mene ne za mu tattauna a wannan babin?

4 Yaya Sama’ila zai jimre da waɗannan abubuwan da suke faruwa ba zato ba tsammani? Shin zai kasance da bangaskiya sosai har ya iya taimaka wa mutanen da suka rasa tagomashin Jehobah da kuma kāriyarsa? Dukanmu a yau muna fuskantar mawuyancin yanayi da kuma abubuwan da ba mu yi tsammani ba a kai a kai. Babu shakka, waɗannan abubuwan barazana ne ga bangaskiyarmu. Saboda haka, bari mu ga ƙarin darussan da za mu iya koya daga Sama’ila.

Ya ‘Aikata Adalci’

5, 6. Wane labari ne aka mai da wa hankali cikin shekaru 20 da aka ƙwace Sanduƙin, kuma mene ne Sama’ila yake yi a lokacin?

5 Labarin dai yanzu ya koma kan Sanduƙi mai tsarki da kuma yadda Filisitiyawa suka ji jiki sanadin ɗaukan sa, har hakan ya sa suka maido da shi. Sai bayan shekara ashirin ne aka sake ambata Sama’ila. (1 Sam. 7:2) Me Sama’ila yake yi a cikin waɗannan shekarun? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar.

A wace hanya ce Sama’ila ya taimaki mutanensa su jimre da rashi da kuma takaici?

6 Kafin wannan lokacin, mun karanta cewa: “Maganar Sama’ila kuma ta zo wurin dukan Isra’ila.” (1 Sam. 4:1) Bayan waɗannan shekarun, labarin ya nuna cewa Sama’ila yakan ziyarci birane uku a Isra’ila, har sai ya kewaye su duk shekara yana daidaita matsaloli da kuma amsa wasu tambayoyi. Bayan haka, sai ya koma garinsu, wato Ramah. (1 Sam. 7:15-17) Hakika, Sama’ila ya shagala da aiki a waɗannan shekarun.

Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ambata Sama’ila ba sai bayan shekara 20, amma babu shakka, ya ci gaba da yin hidimar Jehobah

7, 8. (a) Wane saƙo ne Sama’ila ya idar bayan shekara ashirin da ya yi yana aiki tuƙuru? (b) Shin mutanen sun saurare shi kuwa? Ka bayyana.

7 ’Ya’yan Eli sun gurɓata bangaskiyar mutane ta wajen halayensu na lalata da kuma ɓatanci. Wataƙila hakan ya sa mutane da yawa su soma bautar gumaka. Bayan shekara ashirin da Sama’ila ya yi yana shan aiki, sai ya idar da wannan saƙon ga Isra’ilawa: “Idan kun juyo wurin Ubangiji da dukan zuciyarku, sai ku rabu da baƙin alloli da Ashtaroth, ku nufa zuciyarku zuwa wurin Ubangiji, ku bauta masa shi kaɗai: shi kuma za ya fishe ku daga hannun Filistiyawa.”—1 Sam. 7:3.

8 Filistiyawa sun ba Isra’ilawa kashi sosai. Da yake sun ci su a yaƙi sau da sau, sai suka ji cewa za su iya matsa musu yadda suka ga dama. Amma Sama’ila ya gaya wa Isra’ilawa cewa reshe zai juye da mujiya idan suka komo ga Jehobah. Shin sun yarda su yi hakan kuwa? Sama’ila ya yi farin ciki sa’ad da mutanen suka rabu da gumakansu kuma suka soma “bauta wa Ubangiji shi kaɗai.” Sai Sama’ila ya ce su taru a Mizpah, wata ƙasa da ke arewacin Urushalima. Mutanen suka taru, suka yi azumi kuma suka daina bauta wa gumaka.—Karanta 1 Sama’ila 7:4-6.

Filistiyawa sun ɗauka cewa taron da bayin Jehobah da suka tuba suke yi dama ce na kai musu hari

9. Wane zarafi ne Filistiyawa suka samu, kuma wane mataki ne bayin Allah suka ɗauka?

9 Amma, sa’ad da Filistiyawa suka sami labari cewa Isra’ilawa suna son su yi babban taro, sai suka ɗauki hakan a matsayin zarafin kai musu hari. Sun tura rundunarsu zuwa Mizpah don su halaka waɗannan bayin Jehobah. Sai Isra’ilawa suka sami labarin wannan harin da ke tafe. Yaya suka ji? Sun tsorota sosai har suka ce Sama’ila ya yi addu’a a madadinsu. Sama’ila ya yi hakan, har ma ya miƙa hadaya ga Jehobah. Yayin da Isra’ilawa suke wannan taro mai tsarki, sai Filistiyawa suka kawo musu hari a Mizpah. Shin Jehobah ya amsa addu’ar da Sama’ila ya yi a madadin mutanen kuwa? Ƙwarai kuwa. A sakamako, Jehobah ya gana musu azaba. Ya “yi tsawa da tsawa mai-girma a ran nan a kan Filistiyawa.”—1 Sam. 7:7-10.

10, 11. (a) Me ya sa tsawar da Jehobah ya saukar wa rundunar Filistiyawa ba gama gari ba ne? (b) Mene ne sakamakon yaƙin da aka yi a Mizpah?

10 Shin waɗannan Filistiyawa suna kamar ƙananan yara ne da suke ɓoyewa a bayan mahaifiyarsu sa’ad da suka ji ƙarar tsawa? Ko kaɗan. Su ƙwararrun runduna ne. Babu shakka, ba su taɓa jin irin wannan tsawar ba. Shin ƙarar ce ta rikitar da su? An yi hadari kafin tsawar ta soma ko kuwa ƙarar tsawar tana tasowa ne daga bayan manya-manyan duwatsu? Ba mu san ainihin amsoshin waɗannan tambayoyin ba. Amma, mun san cewa tsawar ta yi matuƙar birkitar da Filistiyawa. Sai Isra’ilawa suka yi jerin gwano, suka yi musu tis kuma suka kori sauran Filisitiyawa har kudu matso yamma na Urushalima.—1 Sam. 7:11.

11 Wannan yaƙin yana da muhimmanci sosai ga Isra’ilawa. Sun ci gaba da yin nasara a kan Filistiyawa a zamanin da Sama’ila yake musu ja-gora kuma sun ci birane da yawa.—1 Sam. 7:13, 14.

12. Mene ne furucin nan Sama’ila ya aikata “adalci” yake nufi, kuma me ya sa ya yi nasara?

12 Shekaru da yawa bayan haka, manzo Bulus ya ambata Sama’ila cikin alƙalawa da annabawa masu aminci da suka aikata “adalci.” (Ibran. 11:32, 33) Babu shakka, Sama’ila ya ƙarfafa Isra’ilawa su kasance da aminci ga Allah. Ya yi nasara domin ya dogara ga Jehobah kuma bai daina aikinsa ba duk da abubuwan da suka faru da bai yi tsammani ba. Sama’ila ya kuma yi hamdala. Bayan sun yi nasara a Mizpah, Sama’ila ya sa a kafa wata alama da za ta riƙa tunasar musu yadda Jehobah ya taimaka musu.—1 Sam. 7:12.

13. (a) Waɗanne halaye ne ya kamata mu kasance da su idan muna son mu yi koyi da Sama’ila? (b) A wane lokaci ne ya fi dacewa mu kasance da irin halayen Sama’ila?

13 Shin kana son ka aikata “adalci” kuwa? Idan haka ne, to ka yi koyi da tawali’un Sama’ila da yadda ya yi haƙuri kuma ya yi hamdala. (Karanta 1 Bitrus 5:6.) Dukanmu muna bukatar mu kasance da waɗannan halayen. Ya dace da Sama’ila ya koyi waɗannan halayen sa’ad da yake ƙarami, domin daga baya, sun taimaka masa ya jimre da abubuwan da bai yi tsammani za su faru ba.

“’Ya’yanka Ba Su Bi Tafarkinka Ba”

14, 15. (a) Wane abin baƙin ciki ne Sama’ila ya fuskanta sa’ad da “ya tsufa”? (b) Shin Sama’ila ya ƙi ya yi wa yaransa horo kamar Eli ne? Ka bayyana.

14 Sama’ila ya riga “ya tsufa” kafin mu sake jin wani labari game da shi. A wannan lokacin, yana da ’ya’ya biyu da suka yi girma. Sunayensu Joel da Abijah ne, kuma ya naɗa su su riƙa taimaka masa a matsayin alƙalawa. Amma abin baƙin ciki, yaran ba su aikata yadda ya kamata ba. Sama’ila mutum ne mai gaskiya da kuma adalci, amma ’ya’yansa sun yi amfani da matsayinsu don su amfane kansu ta wajen aikata rashin adalci da kuma cin hanci.—1 Sam. 8:1-3.

15 Wata rana, sai dattawan Isra’ila suka kai ƙara wurin Sama’ila, suka ce masa: “’Ya’yanka ba su bi tafarkinka ba.” (1 Sam. 8:4, 5) Shin Sama’ila ya san da hakan kuwa? Ba za mu iya ce e ko a’a ba. Akasin Eli, Sama’ila yana horon ’ya’yansa. Jehobah ya hukunta Eli domin bai sa ’ya’yansa su daina yin mugunta ba, kuma ya daraja su fiye da Allah. (1 Sam. 2:27-29) Amma Sama’ila bai yi irin wannan laifi ga Jehobah ba.

Ta yaya Sama’ila ya jimre da takaicin da ’ya’yansa masu rashin aminci suka jawo masa?

16. Yaya iyaye suke ji sa’ad da ’ya’yansu suka yi musu tawaye, kuma ta yaya misalin Sama’ila zai iya taimaka da kuma ƙarfafa su?

16 A labarin, ba a ambata yadda Sama’ila ya ji sa’ad da aka gaya masa yadda ’ya’yansa suke aikata mugunta ba. Iyaye da yawa za su fi fahimtar yadda Sama’ila ya ji. A wannan zamanin, tawaye ga iyaye ya zama ruwan dare. (Karanta 2 Timotawus 3:1-5.) Iyaye da ke cikin irin wannan yanayin za su iya yin koyi da misalin Sama’ila kuma hakan zai iya ƙarfafa su. Halayen Joel da Abijah ba su sa Sama’ila sanyi gwiwa ba. Misalin iyaye ya fi taimaka wa yara, ko da sun ƙi jin magana da kuma gargaɗinsu. Iyaye kuma suna da zarafin faranta wa Jehobah rai, kamar yadda Sama’ila ya yi.

‘Ka Naɗa Mana Sarki’

17. Mene ne dattawan Isra’ila suka ce Sama’ila ya yi, kuma yaya ya ji?

17 ’Ya’yan Sama’ila ba su san cewa halayensu za su shafi mutane sosai ba. Sai dattawan Isra’ilawa suka ce wa Sama’ila: “Yanzu kuwa sai ka yi mana sarki wanda za ya hukunta mu kamar dukan al’ummai.” Shin hakan ya sa Sama’ila ya ji cewa sun ƙi shi ne a matsayin alƙalinsu? Jehobah ya daɗe yana amfani da shi a wannan matsayin, amma yanzu suna son sarki ne ya zama alƙalinsu, ba annabi kamar Sama’ila ba. Al’ummai da ke kewaye da Isra’ilawa suna da sarakuna, kuma su ma suna so a naɗa musu sarki. Yaya Sama’ila ya ji? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Al’amarin nan ya ɓata zuciyar Sama’ila.”—1 Sam. 8:5, 6.

18. Ta yaya Jehobah ya ƙarfafa Sama’ila, kuma yaya ya bayyana tsananin zunubin Isra’ilawa?

18 Sa’ad da Sama’ila ya yi addu’a game da batun, Allah ya ce masa: “Sai ka saurari muryar jama’a a cikin dukan abin da suka faɗa maka: gama ba kai suka ƙi ba, ni ne suka ƙi, kada in yi sarki a bisansu.” Ko da yake hakan ya ƙarfafa Sama’ila, amma rashin kunya ce ga Allah Maɗaukaki. Jehobah ya ce wa annabinsa ya gaya musu sakamakon kasancewa da sarki ɗan Adam. Sa’ad da Sama’ila ya yi hakan, sai suka ta da muryarsu suna cewa: “A’a, sai dai mu sami sarki a bisanmu.” Tun da yake Sama’ila yana biyayya ga Allahnsa, sai ya je ya naɗa musu sarkin da Jehobah ya zaɓa.—1 Sam. 8:7-19.

19, 20. (a) Ta yaya Sama’ila ya yi biyayya ga umurnin da Jehobah ya ba shi cewa ya naɗa Saul a matsayin sarki? (b) Ta yaya Sama’ila ya ci gaba da taimaka wa bayin Jehobah?

19 Shin Sama’ila ya yi biyayya? Ko kuwa ya yi fushi? Mutane da yawa za su iya yin fushi, amma ba abin da Sama’ila ya yi ke nan ba. Ya shafe Saul kuma ya ce shi ne mutumin da Jehobah ya zaɓa. Ya yi masa sumba kuma hakan alama ce cewa ya marabce shi a matsayin sabon sarkin Isra’ila. Sai ya ce wa mutanen: “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa, babu kininsa a cikin dukan jama’a?”—1 Sam. 10:1, 24.

20 Sama’ila bai mai da hankali ga kurakuran Saul ba, amma ya mai da hankali ga halayensa masu kyau. Bai kuma mai da hankali ga yadda mutanen suka ƙi shi ba, amma ga yadda ya daɗe yana bauta wa Allah da aminci. (1 Sam. 12:1-4) Ya ci gaba da yin hidimarsa na yi wa bayin Allah gargaɗi a kan abin da zai iya raunana dangatakarsu da shi kuma ya ƙarfafa su su kasance da aminci ga Jehobah. Gargaɗin da Sama’ila ya yi musu ya shige su sosai, har suka roƙe shi ya yi addu’a a madadinsu. Mene ne Sama’ila ya ce musu? Ya ce: “Allah shi tsare ni, kada in yi wa Ubangiji zunubi, in daina yi muku addu’a: amma zan riƙa koya muku a hanya mai-gaskiya mai-kyau.”—1 Sam. 12:21-24.

Misalin Sama’ila ya tuna mana cewa kada mu taɓa kuskura mu ƙyale kishi da haushi ya mamaye mu

21. Ta yaya misalin Sama’ila zai iya taimaka maka idan ka taɓa yin sanyin gwiwa domin an danƙa wa wani gata maimakon kai?

21 Shin ka san da wani da aka taɓa danƙa wa gata maimakon kai? Yaya ka ji? Misalin Sama’ila ya koya mana cewa kada mu taɓa kuskura mu ƙyale kishi da fushi su shawo kanmu. (Karanta Misalai 14:30.) Jehobah yana da ayyuka masu ɗimbin yawa ga kowane amintaccen bawansa kuma suna sa mu farin ciki.

“Har Yaushe Za Ka Yi Makoki Domin Saul?”

22. Me ya sa ra’ayin Sama’ila game da Saul da farko ba laifi ba ne?

22 Saul mutum ne tubarkalla kuma ya dace da Sama’ila ya ɗauke shi hakan! Saul yana da tsayi da kyaun siffa da gaba gaɗi da kuma dabara. Yana da filako da kuma tawali’u. (1 Sam. 10:22, 23, 27) Ƙari ga hakan, yana da ’yancin zaɓar abin da yake so. (K. Sha 30:19) Shin ya yi amfani da wannan baiwar yadda ya dace kuwa?

23. Wane hali mai kyau ne Saul ya daina nunawa, kuma yaya hakan ya ci gaba da yin muni?

23 Abin baƙin ciki, muddin ka danƙa wa mutum maƙami, yana kasance masa da wuya sosai ya ci gaba da nuna tawali’u. Kafin a ce kwabo, sai Saul ya soma girman kai. Ya ƙi bin umurnin da Jehobah ya ce Sama’ila ya ba shi. Akwai ma lokacin da Saul ya miƙa hadaya maimakon ya jira Sama’ila. A sakamako, Sama’ila ya tsauta masa kuma ya gaya masa cewa zai ƙwace gadon sarauta daga iyalinsa. Saul ya ƙi yin gyara, maimakon haka, ya yi wasu abubuwa da suka fi hakan muni.—1 Sam. 13:8, 9, 13, 14.

24. (a) Ta yaya Saul ya yi rashin biyayya sa’ad da Allah ya ce ya yi yaƙi da Amalekawa? (b) Mene ne Saul ya yi sa’ad da aka yi masa gyara, kuma me Jehobah ya ce?

24 Jehobah ya tura Sama’ila ya gaya wa Saul cewa ya je ya yi yaƙi da Amalekawa. Jehobah ya ce ya kashe sarkinsu mai suna Agag. Amma, Saul ya kāre Agag da kuma wasu abubuwan da aka ce ya halaka. Sa’ad da Sama’ila ya gargaɗe shi, ya ƙi ya saurara, amma ya soma neman hujja don ya kāre kansa. Mene ne Sama’ila ya yi sa’ad da Saul ya yi hakan? Ya ce: “Ka lura, biyayya ta fi hadaya.” Sama’ila ya yi gaba gaɗi sosai kuma ya tsauta wa Saul ƙwarai. Ya gaya masa cewa Jehobah ya ƙwace sarauta daga hannunsa kuma zai ba wani da ya fi shi. *1 Sam. 15:1-33.

25, 26. (a) Me ya sa Sama’ila ya yi makoki domin Saul, kuma ta yaya Jehobah ya yi masa gyara? (b) Wane darasi ne Sama’ila ya koya sa’ad da ya je gidan Jesse?

25 Abin da Saul ya yi ya ɓata wa Sama’ila rai sosai. Ya yi ta kuka ga Jehobah daddaren. Ya ma soma makoki domin Saul. Sama’ila ya ga cewa Saul yana da halaye masu kyau, amma yanzu duk sun bi ruwa. Saul ya canja baƙi ɗaya, kuma ya juya bayansa ga Jehobah. Sama’ila ya ƙi ya sake ganin Saul. Daga baya Jehobah ya daidaita ra’ayin Sama’ila, ya ce masa: “Har yaushe za ka yi makoki domin Saul, da shi ke na ƙi shi da zaman sarki bisa Isra’ila? ka cika ƙahonka da mai, ka tafi, in aike ka wurin Jesse mutumin Bai’talahmi: gama daga cikin ’ya’yansa na zaɓo sarki.”—1 Sam. 15:34, 35; 16:1.

26 Rashin amincin ’yan Adam ajizai ba zai hana Jehobah ya cika nufinsa ba. Idan mutum ya yi rashin aminci, Jehobah zai zaɓa wani ya ɗauki matsayinsa. Sai Sama’ila ya daina makoki domin Saul. Ya yi biyayya ga umurnin Jehobah, ya tafi gidan Jesse a Bai’talami inda ya haɗu da ’ya’yansa masu kyaun gaske. Da farko, Jehobah ya tuna masa cewa kada ya mai da hankali ga siffarsu. (Karanta 1 Sama’ila 16:7.) Daga baya, Sama’ila ya haɗu da autansu mai suna Dauda kuma shi ne Jehobah ya zaɓa!

27. (a) Me ya taimaki Sama’ila ya ci gaba da kasancewa da bangaskiya? (b) Mene ne ra’ayinka game da gurbin da Sama’ila ya kafa?

27 Da shigewar lokaci, Sama’ila ya fahimci cewa ya dace da Jehobah ya sauya Saul da Dauda. Saul ya soma kishi da ridda kuma ya nemi ya kashe Dauda. Amma, Dauda ya kasance da gaba gaɗi da nagarta da bangaskiya da kuma aminci. Sa’ad da Sama’ila ya kusan mutuwa, ya yi imani sosai ga Jehobah. Ya ankara cewa babu takaicin da ya fi ƙarfin Jehobah, kuma zai iya mai da shi albarka. Daga baya, sai Sama’ila ya rasu. Ya kafa gurbi mai kyau kuma ya rayu kusan shekara 100. Dukan Isra’ilawa sun yi makoki ƙwarai saboda rasuwar wannan mutum mai aminci! Ya kamata bayin Jehobah a yau su tambaye kansu, ‘Shin zan yi koyi da bangaskiyar Sama’ila kuwa?’

Sama’ila ya ankara cewa babu takaicin da ya fi ƙarfin Jehobah, kuma zai iya mai da shi albarka

^ sakin layi na 24 Sama’ila ya kashe Agag da kansa. Wannan mugun sarkin da iyalinsa ba su cancanci rangwame ba. Babu shakka, “Haman Ba-agagi” wanda ya nemi ya halaka dukan bayin Allah dangin Agag ne.—Esther 8:3, ka duba Babi na 15 da 16 na wannan littafin.