Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA ASHIRIN

‘Na Riga Na Ba da Gaskiya’”

‘Na Riga Na Ba da Gaskiya’”

1. Me ya sa Martha take baƙin ciki?

MARTHA ba za ta iya manta da kabarin ɗan’uwanta ba, wato wani kogo da aka rufe bakin da dutse. Tana baƙin ciki sosai. Tana ji kamar mutuwar ɗan’uwanta Li’azaru mafarki ne. Tun bayan kwanaki huɗu da ya mutu, gidan yana cike da mutane masu makoki da kuma masu ta’aziyya.

2, 3. (a) Yaya Martha ta ji sa’ad da ta ga Yesu? (b) Mene ne kalamin Martha ya nuna game da ita?

2 Ga shi kuma, aminin Li’azaru yana tare da Martha. Sa’ad da ta ga Yesu, wataƙila ta daɗa baƙin ciki, domin da shi kaɗai ne zai iya ceton ɗan’uwanta. Duk da haka, kasancewa tare da Yesu a tudun ƙauyen Bait’anya ya ƙarfafa Martha sosai. Alheri da tausayin da Yesu ya nuna mata sun ta’azantar da kuma ƙarfafa ta. Yesu ya yi mata tambayoyi da suka taimaka mata ta mai da hankali ga bangaskiya da kuma begenta game da tashin matattu. Tattaunawar da suka yi ta sa Martha ta furta wani kalami mafi muhimmanci da ta taɓa yi. Ta ce: “Na rigaya na ba da gaskiya kai ne Kristi, Ɗan Allah, shi wanda yake zuwa cikin duniya.”—Yoh. 11:27.

3 Wannan kalamin ya nuna cewa Martha tana da bangaskiya sosai. Mun koyi darussa da za su taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu a ɗan bayanin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da ita. Bari mu tattauna labari na farko game da Martha da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

“Kin Damu, Kina Wahala”

4. Iyalin su Martha ta haɗa da waye kuma wace dangantaka suke da shi da Yesu?

4 A watannin baya, Li’azaru yana da rai da kuma koshin lafiya. Yesu Kristi yana so ya ziyarce su a gidansu da ke ƙauyen Bait’anya kuma ba su taɓa yin baƙo irinsa ba. Li’azaru da Martha da kuma Maryamu ’yan’uwa ne da ke zama tare. Wasu masu bincike sun ce wataƙila Martha ce babba, da yake ita ce mai karɓan baƙi kuma akan fara ambata sunanta a wasu lokatai. (Yoh. 11:5) Ba wanda ya san ko wani cikinsu ya taɓa yin aure, amma mun dai san cewa sun zama aminan Yesu. A lokacin da Yesu yake hidima a yankin Yahuda, inda ya fuskanci hamayya da kuma ƙiyayya, ya zauna a gidansu. Ba shakka cewa ya ji daɗin zama da su cikin salama kuma ya yi hamdala don yadda suka taimaka masa.

5, 6. (a) Me ya sa Martha ta fi shagala da aiki a lokacin da Yesu ya ziyarce su? (b) Mene ne Maryamu ta yi sa’ad da Yesu ya kawo musu ziyara?

5 Martha ta taimaka sosai wajen sa gidan ya kasance da lumana kuma tana da karimci. Ta saba da yin aiki tuƙuru kuma ta shagala da aiki a lokacin da Yesu yake so ya ziyarce su. Martha ta yi girki na musamman don wannan baƙon da wataƙila ke tare da tawagarsa. Mutane suna karɓan baƙi da kyau a zamaninsu. Sa’ad da baƙo ya iso, za a yi masa sumba, a cire takalmansa, a wanke sawunsa kuma a shafa masa mān ƙamshi a kai. (Karanta Luka 7:44-47.) Akan shirya masa wurin kwanciya kuma a ciyar da shi da kyau.

6 Martha da Maryamu sun shagala da aiki sosai. Da farko, Maryamu wadda ake ganin ta fi ’yar’uwarta mai da hankali da kuma natsuwa ta taimaka mata da aikace-aikacen. Amma sa’ad da Yesu ya iso, ya mai da hankali ga wani abu dabam. Ya yi amfani da wannan zarafin wajen koyar da waɗanda suke wurin. Shugabannin addini a lokacin ba sa daraja mata, amma Yesu bai yi hakan ba. Maimako, ya koya musu game da batu mafi muhimmanci a hidimarsa, wato Mulkin Allah. Maryamu ta ji daɗin wannan damar ƙwarai kuma ta zauna kusa da sawunsa tana sauraro da kyau.

7, 8. Me ya sa Martha ta damu kuma ta yaya ta furta abin da ke ci mata rai?

7 Ka yi tunanin yadda Martha ta damu ƙwarai sa’ad da take aiki wurjanjan. Shirye-shiryen da take yi don ta kula da kuma ciyar da baƙinta ya raba hankalinta kuma ya sa ta alhini. Shin Martha ta ɗaura fuska ne ko ta ja tsaki yayin da take kai da kawowa kuma ta ga ’yar’uwarta zaune kawai maimakon ta taimaka mata? Ko da ma ta yi hakan, ba abin mamaki ba ne domin aikin ya fi ƙarfinta.

8 A ƙarshe, Martha ba ta iya jimre da yadda take ji ba. Sai ta katse wa Yesu magana da cewa: “Ubangiji, ko ba ka kula ba ’yar’uwata ta bar ni in yi hidima ni kaɗai? Sai ka ce mata ta taimake ni.” (Luk 10:40) Kalaminta ya nuna cewa abin ya dame ta sosai. Sai ta ce Yesu ya tsauta wa Maryamu kuma ya umurce ta ta koma bakin aiki.

9, 10. (a) Wace amsa ce Yesu ya ba Martha? (b) Me ya sa za a ce Yesu bai tsauta wa Martha ba don ta shagala da aiki?

9 Wataƙila amsar da Yesu ya ba Martha ya ba ta mamaki ƙwarai, kamar yadda mutane da yawa suke mamaki sa’ad da suka karanta labarin. Mene ne Yesu ya ce mata? Ya gaya mata a hankali cewa: “Martha, Martha, kin damu, kina wahala kuma a kan abubuwa dayawa: amma bukata ɗaya ce: gama Maryamu ta zaɓi rabo mai-kyau, ba kuwa za a amshe mata ba.” (Luk 10:41, 42) Mene ne Yesu yake nufi? Shin yana nufin cewa Martha tana son kayan mallaka fiye da Allah ne? Shin yana tsauta mata ne don ta shagala da girki?

Martha ta ‘damu kuma tana wahala a kan abubuwa da yawa,’ amma ta amince da gyarar da Yesu ya yi mata

10 A’a. Yesu ya ga cewa Martha tana da muradi mai kyau kuma ƙauna ce ke motsa ta. Ban da haka ma, bai nuna cewa halinta na karimci bai dace ba, domin akwai lokacin da ya halarci ‘babban bikin’ da Matta ya shirya a gidansa. (Luk 5:29) Matsalar ita ce Martha ta ɗauki wannan liyafar da tamani sosai, shi ya sa ta mance da abin da ya fi muhimmanci. Me ke nan?

Yesu ya yi hamdala don karimcin Martha kuma ya san tana da muradi mai kyau da kuma ƙauna

11, 12. Ta yaya Yesu ya yi wa Martha gyara a hankali?

11 Yesu Ɗa makaɗaici na Jehobah ya zo gidan su Martha ne don ya koyar da mutane game da Allah. Abincin da ta ɗauki lokaci tana shiryawa bai kai hakan muhimmanci ba. Hakika, Yesu ya damu cewa Martha ba ta yi amfani da wannan damar wajen ƙarfafa bangaskiyarta ba. Duk da haka, ya ƙyale ta ta yi zaɓi. * Amma ’yancinta bai kai na yi wa Maryamu zaɓin abin da ya fi muhimmanci ba.

12 Saboda haka, Yesu ya yi wa Martha gyara a hankali. Ya kira sunanta sau biyu don ya sa hankalinta ya kwanta kuma ya tabbatar mata cewa ba ta bukatar ta sha wahala don ‘abubuwa da yawa.’ Girki mai sauƙi kuma madaidaici zai wadatar, tun da yake ana so a tattauna game da Allah. Saboda haka, ba zai tsauta wa Maryamu ba don ta zaɓi ta saurare shi kuma ya ce wannan ne “rabo mai-kyau.”

13. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga abin da Yesu ya gaya wa Martha?

13 Akwai darussa da yawa da za mu iya koya daga wannan labarin. Kada mu ƙyale kome ya hana mu yin abubuwan da za su kyautata dangantakarmu da Jehobah. (Mat. 5:3) Ko da yake yana da kyau mu yi koyi da Martha ta wajen yin karimci da kuma aiki tuƙuru, amma kada mu riƙa alhini da damuwa game da yin karimci har mu mance da abin da ya fi muhimmanci. Sa’ad da muke cuɗanya da ’yan’uwa, abin da ya fi muhimmanci shi ne samun ƙarfafa da kuma taimaka musu su koyi wani abu, ba rarraba abinci mai yawa ba. (Karanta Romawa 1:11, 12.) Kome ƙanƙantar abinci da muka shirya, cuɗanyar za ta iya zama da ban ƙarfafa sosai.

Ɗan’uwa Ƙaunatacce Ya Mutu, Amma An Ta da Shi

14. Me ya sa za mu ce Martha ta kafa misali mai kyau na yin na’am da gyara?

14 Shin Martha ta amince da gyarar da Yesu ya yi mata kuma ta koyi darasi? Mun san ta yi hakan. A gabatarwar labarin da manzo Yohanna ya rubuta game da ɗan’uwanta Li’azaru, ya ce: “Yesu dai yana ƙaunar Martha, da ’yar’uwarta, da Li’azaru.” (John 11:5) Yanzu an yi watanni da Yesu ya kai musu ziyarar da aka ambata ɗazu. A bayyane yake cewa Martha ba ta daina magana da Yesu ba kuma ba ta yi fushi don gyarar da ya yi mata ba. Ta yi na’am da gyarar. Hakan ma misali ne mai kyau na bangaskiya da ta kafa mana domin dukanmu mukan bukaci gyara a wani lokaci.

15, 16. (a) Mene ne Martha ta yi sa’ad da ɗan’uwanta ya soma rashin lafiya? (b) Me ya sa Martha da Maryamu suke baƙin ciki domin Yesu bai iso da wuri ba?

15 A lokacin da ɗan’uwanta ya yi rashin lafiya, Martha ta kula da shi sosai. Ta yi iya ƙoƙarinta wajen taimaka masa ya samu sauƙi. Amma rashin lafiyar sai daɗa tsanani yake. Martha da Maryamu sun kula da shi a kowane lokaci. Mai yiwuwa, Martha ta riƙa kallon fuskarsa sau da sau kuma ta tuna da yadda suka kasance tare a lokacin farin ciki da kuma baƙin ciki.

16 Sa’ad da Martha da Maryamu suka ga cewa ciwon Li’azaru ya fi ƙarfin su, sai suka aika wa Yesu saƙo. A lokacin yana wa’azi a wani wurin da ke da nisan tafiyar kwana biyu daga Bait’anya. Saƙon da suka aika shi ne: “Ubangiji, ga shi, wanda kana ƙaunatasa yana ciwo.” (Yoh. 11:1, 3) Sun san cewa Yesu yana ƙaunar ɗan’uwansu kuma sun ba da gaskiya cewa zai iya warkar da abokinsa. Wataƙila, sun zata cewa Yesu zai iso da gaggawa. Amma hakan bai yiwu ba. Li’azaru ya mutu.

17. Me ya sa Martha ta yi mamaki kuma mene ne ta yi sa’ad da ta ji cewa Yesu ya kusan isa Bait’anya?

17 Martha da Maryamu sun yi makokin ɗan’uwansu sosai. Sun yi shirin jana’izar sa kuma sun yi ta karɓan baƙi daga Bait’anya da kuma wasu garuruwa da ke kusa. Har ila, ba labarin Yesu. Wataƙila, Martha tana mamakin abin da ya sa Yesu bai zo ba. Yanzu da Li’azaru ya yi kwana huɗu da mutuwa, sai ta sami labari cewa Yesu ya kusan isa ƙauyen. Har ma a wannan lokacin makokin, Martha ta hanzarta ta je ta sami Yesu ba tare da ta gaya wa Maryamu ba.—Karanta Yohanna 11:18-20.

18, 19. Wane bege ne Martha ta nuna cewa tana da shi kuma me ya sa za mu yi koyi da bangaskiyarta?

18 Sa’ad da Martha ta ga Yesu, sai ta furta abin da ya yi ta damun ta da kuma Maryamu. Ta ce: “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Amma, har ila Martha tana da bege da kuma bangaskiya. Ta kuma ce: “Amma na sani ko yanzu, ko mene ne da za ka roƙa ga Allah, Allah zai ba ka.” Nan da nan Yesu ya ƙarfafa ta da cewa: “Ɗan’uwanki zai tashi.”—Yoh. 11:21-23.

19 A ganin Martha, Yesu yana magana ne game da lokacin tashin matattu a nan gaba, shi ya sa ta ce: “Na sani zai tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” (Yoh. 11:24) Ta yi imani da wannan koyarwar sosai. Wasu shugabannin addinin Yahudawa da ake kira Sadukiyawa, ba su amince cewa za a yi tashin matattu ba, ko da yake Littafi Mai Tsarki ya koyar da hakan. (Dan. 12:13; Mar. 12:18) Amma, Martha ta san cewa Yesu ya yi koyarwa game da tashin matattu kuma ya yi wannan mu’ujizar sau da sau, ko da yake bai taɓa ta da wanda ya daɗe da mutuwa kamar Li’azaru ba. Ba ta san abin da zai faru jim kaɗan ba.

20. Mene ne kalamin Yesu da ke cikin littafin Yohanna 11:25-27 yake nufi kuma mene ne amsar da Martha ta bayar take nufi?

20 Yesu ya faɗi abin da Martha ba za ta taɓa mantawa ba. Ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai.” Hakika, Jehobah Allah ya ba Ɗansa ikon ta da matattu a dukan duniya a nan gaba. Yesu ya tambayi Martha cewa: “Kin gaskanta wannan?” Sai ta ba da amsar da muka tattauna a farkon wannan babin. Tana da bangaskiya cewa Yesu ne Kristi ko Almasihu kuma shi ne Ɗan Allah. Ta kuma gaskata cewa shi ne wanda annabawa suka annabta cewa zai zo duniya.—Yoh. 5:28, 29; karanta Yohanna 11:25-27.

21, 22. (a) Ta yaya Yesu ya nuna baƙin cikinsa a gaban waɗanda suke makoki? (b) Ka bayyana abin da ya faru sa’ad da aka ta da Li’azaru.

21 Shin Jehobah da kuma Ɗansa Yesu Kristi suna ɗaukan irin bangaskiyar Martha da muhimmanci kuwa? Abin da ya faru ba da daɗewa ba ya nuna wa Martha cewa amsar e ce. Ta yi hanzari ta kira ’yar’uwarta. Sa’ad da Yesu yake magana da Maryamu da kuma sauran masu makoki, Martha ta lura cewa ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ta ga yadda idanunsa suka cika da hawaye saboda baƙin ciki da mutuwa ke jawowa. Ta ji sa’ad da Yesu ya ba da umurni cewa a kawar da dutsen daga bakin kabarin ɗan’uwanta.—Yoh. 11:28-39.

22 Martha ta ƙi, don ta san cewa yanzu gawarsa da ta yi kwana huɗu a kabari za ta soma ɗoyi. Sai Yesu ya tuna mata da abin da ya faɗa. Ya ce: “Ban ce maki ba, idan kin ba da gaskiya za ki ga girman Allah?” Ta ba da gaskiya kuma ta ga ikon Jehobah Allah. Nan da nan Allah ya ba Ɗansa iko kuma ya ta da Li’azaru. Ka yi tunanin abubuwan da suka faru da Martha ba za taɓa mantawa ba muddar ranta. Za ta riƙa tuna da yadda Yesu ya kira, “Li’azaru, ka fito” da kuma yadda ya fito a hankali ta bakin kogon da aka binne shi ƙafa da hannu a ɗaure da likkafani. Sai Yesu ya ba da umurni a “kwance shi [kuma] a sake shi.” Babu shakka, Martha da Maryamu sun yi farin ciki sosai kuma suka rungumi ɗan’uwansu. (Karanta Yohanna 11:40-44.) Wannan mu’ujizar ta kawar da baƙin cikin da Martha take yi!

An albarkaci Martha don imaninta ga Yesu sa’ad da ita da Maryamu suka ga an ta da ɗan’uwansu

23. Mene ne Jehobah da Yesu suke so su yi maka, kuma mene ne kake bukatar ka yi?

23 Wannan labarin ya ba da tabbaci cewa za a yi tashin matattu. Littafi Mai Tsarki ya koyar da hakan kuma ya faru a dā. (Ayu. 14:14, 15) Jehobah da Ɗansa suna so su yi wa waɗanda suke da bangaskiya albarka, kamar yadda suka yi wa Martha da Maryamu da kuma Li’azaru. Hakazalika, za su albarkace ka idan ka kasance da bangaskiya sosai.

“Martha Tana Hidima”

24. Wane furuci na ƙarshe ne aka yi game da Martha a cikin Littafi Mai Tsarki?

24 An sake ambata Martha sau ɗaya a cikin Littafi Mai Tsarki a mako na ƙarshe kafin a kashe Yesu. Yesu ya san cewa zai sha wahala sosai a wannan makon, sai ya tafi gidan abokansa a ƙauyen Bait’anya. Daga wajen zai yi tafiya na mil biyu zuwa Urushalima. Yesu da Li’azaru suna cin abinci a gidan Siman kuturu a Bait’anya kuma a wajen ne muka ji wannan kalami na ƙarshe game da Martha, cewa: “Tana hidima.”—Yoh. 12:2.

25. Me ya sa mata masu yin koyi da Martha albarka ce ga ikilisiyoyi a yau?

25 Hakika, Martha tana da ƙwazon aiki! Tana aiki a lokaci na farko da Littafi Mai Tsarki ya ambata ta. Har ila, a lokaci na ƙarshe da aka ambata ta tana aiki da kuma yin iya ƙoƙarinta don ta biya bukatun waɗanda suke tare da ita. Akwai mata kamar Martha a cikin ikilisiyoyi da yawa a yau kuma hakan albarka ce. Irin waɗannan ’yan’uwa mata suna da gaba gaɗi da karimci kuma suna da bangaskiya. Suna kuma taimaka wa ’yan’uwansu. Wataƙila Martha ta ci gaba da yin hakan. Bangaskiyarta za ta taimaka mata ta jimre da matsaloli masu wuya a nan gaba.

26. Yaya bangaskiyar Martha ta taimaka mata?

26 Nan da kwanaki kaɗan, za a kashe Ubangijin Martha, wato Yesu kuma hakan zai sa ta baƙin ciki sosai. Bugu da ƙari, munafukai masu kisan kai da suka kashe shi, sun ƙudura niyya su kashe Li’azaru, tun da yake tashinsa daga matattu ya sa mutane da yawa sun ba da gaskiya ga Yesu. (Karanta Yohanna 12:9-11.) Daga baya, mutuwa ta raba Martha da ’yan’uwanta. Ba mu san lokaci da kuma yadda hakan ya faru ba, amma mun tabbata cewa bangaskiyar Martha ta taimaka mata ta jimre har ƙarshe. Shi ya sa ya kamata Kiristoci su yi koyi da bangaskiyar Martha.

^ sakin layi na 11 Yahudawa ba sa tura mata makaranta a ƙarni na farko. An fi koya musu aikace-aikacen gida. Shi ya sa wataƙila Martha ta ga kamar bai dace mace ta zauna kusa da malami tana koyo ba.