Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA BIYAR

“Macen Kirki”

“Macen Kirki”

1, 2. (a) Wane irin aiki ne Ruth take yi? (b) Mene ne Ruth ta koya game da Dokar da Allah ya ba bayinsa?

RUTH ta sunkuya a gaban tarin sha’ir da ta yi kala tun da safe. Yanzu rana ta faɗi a filayen da ke Bai’talami, kuma mutane da yawa sun soma tafiya gida. Babu shakka, Ruth ta gaji tikis domin tun safe take aiki. Duk da haka, ta ci gaba da buga sha’ir ɗin don ta tattara amfanin. Ko da yake aikin yana da wuya, amma ta yi dace.

2 Shin yanayin Ruth ya soma canjawa ne? Kamar yadda muka tattauna a talifin da ya gabata, ta ƙi rabuwa da surukarta Naomi, kuma ta yi alkawari cewa za ta kasance tare da ita kuma za ta bauta wa Allahnta Jehobah. Waɗannan gwauraye biyu da suke makoki sun taho tare daga ƙasar Mowab zuwa Bai’talami. Ba da daɗewa ba, sai Ruth ’yar Mowab ta samu labari cewa Jehobah ya kafa wata Doka mai kyau sosai. Wannan Dokar ta shafi talakawa da ke Isra’ila da kuma baƙi. Bugu da ƙari, ta lura cewa wasu bayin Jehobah da suke bin wannan Dokar suna nunawa ta halinsu cewa suna son Dokar kuma hakan ya ƙarfafa ta sosai.

3, 4. (a) Ta yaya Boaz ya ƙarfafa Ruth? (b) Ta yaya misalin Ruth zai iya taimaka mana a wannan duniyar da tattalin arziki yake taɓarɓarewa?

3 Akwai wani mutum da ke son wannan Dokar sosai, sunansa Boaz kuma shi dattijo ne mai arziki sosai. Ya lura da Ruth, shi ya sa ya ƙyale ta ta yi kala a gonarsa. Babu shakka, ta yi murna sa’ad da ya yaba mata don ta kula da Naomi kuma ta nemi mafaka a ƙarƙashin fukafukan Allah na gaskiya, wato Jehobah.—Karanta Ruth 2:11-14.

4 Duk da haka, Ruth ta yi tunani a kan yadda rayuwarta za ta kasance nan gaba. Da yake ita talaka ce da baƙuwa kuma ba ta da miji da ’ya’ya, ta yaya za ta riƙa biyan bukatunta da na Naomi? Shin da kala ne kawai za ta riƙa yin hakan? Kuma wane ne zai kula da ita sa’ad da ta tsufa? Ba abin mamaki ba ne idan ta yi irin wannan tunanin. Da yake tattalin arziki yana daɗa taɓarɓarewa a yau, mutane da yawa suna irin waɗannan tambayoyin. Yayin da muka koya yadda bangaskiyar Ruth ta taimaka mata ta jimre da waɗannan ƙalubalen, za mu bukaci yin koyi da bangaskiyarta.

Mece Ce Iyali?

5, 6. (a) Shin Ruth ta yi nasara kuwa a rana ta farko da ta yi kala? Ka bayyana. (b) Mene ne Naomi ta yi sa’ad da ta ga surukarta?

5 Bayan Ruth ta gama buga hatsin, sai ta lura cewa ta sami wajen ephah guda na sha’ir. Wataƙila nauyin ya kai kilo 14. Mai yiwuwa ta zuba hatsin cikin ƙyalle, sai ta ɗora shi a kai kuma ta nufi Bai’talami sa’ad da gari ya yi duhu.—Ruth 2:17.

6 Naomi ta yi farin cikin ganin Ruth, kuma wataƙila ta yi mamaki ganinta da sha’ir mai yawa haka. Ruth ta dawo gida da sauran abincin da Boaz ya ba ’yan ƙodagonsa, sai ita da Naomi suka ci abincin tare. Naomi ta tambaye ta: “A ina kika yi kāla yau? A ina kika yi aiki? Albarka gareshi wanda ya lura da ke!” (Ruth 2:19) Naomi tana lura sosai, ta san cewa Ruth ba za ta iya yin kalar dukan wannan hatsi mai nauyi ba, tabbas wani ya taimake ta.

7, 8. (a) Wane ne Naomi take ganin ya sa aka yi musu alheri, kuma me ya sa? (b) Ta yaya Ruth ta nuna cewa tana da aminci da kuma ƙauna ga surukarta?

7 Sai Ruth da Naomi suka soma tattauna yadda Boaz yake da kirki. Abin da suka tattauna ya motsa Naomi sosai, har ta ce: “Ubangiji wanda ba ya bar nuna alherinsa ga masu-rai duka da matattu shi albarkace shi.” (Ruth 2:20) Ta fahimci cewa Jehobah ne ya sa Boaz ya nuna musu alheri. Jehobah yana son a riƙa nuna alheri kuma ya ce zai albarkaci bayinsa da suka yi hakan. *Karanta Misalai 19:17.

8 Naomi ta gaya wa Ruth cewa ta amince da tayin da Boaz ya yi mata. Wane tayi ke nan? Ya ce ta riƙa yin kala tare da matan da suke masa ƙodago a gonarsa don kada masu girbin su kwaɓe ta. Ruth ta bi wannan shawarar. Ta kuma ci gaba da zama “tare da surukarta.” (Ruth 2:22, 23) Waɗannan kalaman sun nuna cewa tana da ƙauna da kuma aminci. Ya kamata misalin Ruth ya motsa mu mu tambayi kanmu ko muna daraja gamin da ke iyalinmu, kuma muna taimaka wa ’yan’uwanmu da suke bukatar taimako. Idan muka nuna irin waɗannan halayen, Jehobah ba zai manta da mu ba.

Misalan Ruth da Naomi sun tuna mana mu riƙa daraja iyalinmu

9. Mene ne misalin Ruth da Naomi ya koya mana game da iyali?

9 Shin ya isa a kira Naomi da Ruth iyali? Wasu sun ce iyali ta ƙunshi miji da mata da yara da kaka da dai sauransu. Amma, misalin Naomi da Ruth ya nuna mana cewa idan iyali ta ragu saboda wata matsala ko kuma bala’i, waɗanda suka rage za su iya haɗa kai su kasance da ƙauna da kuma aminci. Shin kana daraja iyalinka? Yesu ya tunatar mana cewa ikilisiyar Kirista za ta iya zama kamar iyali a gare mu.—Mar. 10:29, 30.

Ruth da Naomi sun taimaka da kuma ƙarfafa juna

“Yana Cikin ‘Waɗanda Suke da Iko Su Fanshe Mu’

10. A wace hanya ce Naomi take son ta taimaka wa Ruth?

10 Ruth ta ci gaba da yin kala a gonar Boaz daga lokacin girbin sha’ir a watan Afrilu zuwa lokacin girbin alkama a watan Yuli. Sa’ad da makonnin suke shigewa, mai yiwuwa Naomi ta yi tunani a kan wani abin da za ta iya yi wa surukarta. A lokacin da suke Mowab, Naomi ta san cewa ba za ta iya taya Ruth neman miji ba. (Ruth 1:11-13) Amma yanzu ta canja ra’ayinta, sai ta gaya wa Ruth cewa: “Ɗiyata, ba sai in nema miki hutawa ba?” (Ruth 3:1) Al’adarsu a dā ta ƙyale iyaye su nema wa ’ya’yansu miji ko mata, kuma har ila Ruth ta zama kamar ’ya a wurin Naomi. Tana so ta samo wa Ruth wurin “hutawa.” Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin irin kāriya da mutum yake samu idan yana da wurin kwana da kuma miji. Amma, mene ne Naomi za ta iya yi?

11, 12. (a) Mene ne Naomi take nufi sa’ad da ta ce Boaz yana da iko ya yi fansa domin su? (b) Shin Ruth ta yi biyayya ga shawarar da surukarta ta ba ta kuwa? Ka bayyana.

11 A lokaci na farko da Ruth ta yi magana game da Boaz, Naomi ta ce: “Mutumin nan danginmu ne na kusa, ɗaya daga cikin waɗanda su ke da iko su yi fansa dominmu.” (Ruth 2:20) Mene ne hakan yake nufi? A Dokar da Jehobah ya ba Isra’ilawa, ya yi tanadi don iyalan da suka talauce ko kuma suke shan wahala sanadin rasuwa. Idan mace ta zama gwauruwa kuma ba ta da yara, tana baƙin ciki sosai domin za a manta da sunan maigidanta. Amma, Dokar Allah ta ƙyale ɗan’uwan mamacin ya auri gwauruwar domin ta haifi ɗa da zai gāji sunan mamacin kuma ya kula da gādonsa. *—K. Sha 25:5-7.

12 Naomi ta gaya wa Ruth shirin da take yi. Ka yi tunanin yadda Ruth take gwaggwale idanunta don mamaki yayin da surukarta take magana. Ruth ba ta saba da Doka da kuma al’adun Isra’ilawa ba tukun. Duk da haka, ta yi ladabi sosai ga Naomi, kuma ta saurare ta. Mutane da yawa ba za su yarda su yi abin da Naomi ta ce Ruth ta yi ba. Me ya sa? Domin hakan zai iya kunyatar ko kuma ya ƙasƙantar da su. Ruth ta ce: “Dukan abin da kika faɗi, sai in yi.”—Ruth 3:5.

13. Wane darasi ne za mu iya koya daga yadda Ruth ta bi shawarar tsohuwa? (Ka kuma duba Ayuba 12:12.)

13 A wasu lokatai, yana wa matasa wuya ainun su bi shawarar wani da ya girme su. Yana da sauƙi matasa su ji cewa waɗanda suka manyanta ba su fahimci ƙalubale da kuma matsalolin da suke fuskanta ba. Misalin Ruth ya tuna mana cewa idan muka bi shawarar waɗanda suka girme mu kuma suke ƙaunarmu, za mu samu sakamako mai kyau. (Karanta Zabura 71:17, 18.) Amma wace shawara ce Naomi ta ba Ruth, kuma shin an albarkaci Ruth kuwa don ta bi shawarar?

Ruth a Masussuka

14. Mece ce masussuka, kuma yaya ake yin sheƙa a dā?

14 Ruth ta nufi masussuka da yammar. Masussuka wuri ne da manoma suke buga da kuma yin sheƙar amfanin gonarsu. Ana yawan zaɓan tsauni inda iska ke hurowa sosai da rana da kuma yamma. ’Yan ƙodago suna yin amfani da shebur mai yatsu ko kuma shebur don ɗaga amfanin gonar sama, sai iska ta hura ƙaiƙayin ko ɓuntun kuma hatsin ya faɗo ƙasa.

15, 16. (a) Ka kwatanta abin da ya faru bayan Boaz ya kammala aiki da yamma. (b) Yaya Boaz ya lura cewa Ruth tana kwance a ƙafafunsa?

15 Ruth ta mai da hankali sosai yayin da ’yan ƙodagon suke kammala aikinsu da yamma. Boaz ya lura da yadda ake yin sheƙar hatsinsa har ya yi yawan gaske. Bayan ya ci abinci, sai ya nemi wuri kusa da inda aka tattara hatsin ya kwanta. Hakan gama gari ne a dā, wataƙila don kada ɓarayi su saci amfanin gonar. Ruth ta hangi Boaz sa’ad da ya kwanta daddaren. Lokaci ya yi da za ta yi abin da Naomi ta ce.

16 Ruth ta soma matsowa kusa, yayin da gabanta na faɗuwa. Ta lura cewa mutumin yana sheƙa barci, sai ta nufi ƙafafunsa ta kware rigarsa kuma ta kwanta. Sai ta jira, kuma babu shakka a ganinta lokaci ba ya guduwa. Amma can da tsakar dare sai Boaz ya juya, wataƙila domin sanyi ya shiga jikinsa, sai ya miƙe don ya rufe ƙafafunsa. Amma ya lura cewa akwai mutum a wurin. Ayar ta ce, “Sai ga mace tana kwance wajen ƙafafunsa.”—Ruth 3:8.

17. Shin abin da Ruth ta yi ya dace kuwa? Ka bayyana.

17 Sai Boaz ya ce: “Wace ce ke?” Wataƙila Ruth ta amsa cike da tsoro: “Ni ce Ruth baiwarka: ka buɗe mayafinka bisa baiwarka; gama kai dangi ne na kusa.” (Ruth 3:9) Wasu mutane a yau sun ce abin da Ruth ta yi bai dace ba, amma akwai abubuwa biyu da ba su fahimta ba. Na farko, Ruth ta bi al’adar zamanin dā ne, wadda an daina bi yanzu. Saboda haka, bai dace a gwada abin da ta yi da abin da ke faruwa a zamaninmu da ake yawan lalata ba. Na biyu kuma, matakin da Boaz ya ɗauka ya nuna cewa Ruth ba ta wuce gona da iri ba.

Ruth ba ta wuce gona da iri ba sa’ad da ta je wurin Boaz

18. Ta yaya Boaz ya ƙarfafa Ruth, kuma waɗanne alheri biyu da ta nuna ne suka ratsa zuciyarsa?

18 Boaz ya yi magana, kuma babu shakka, yadda ya yi magana a hankali ya ƙarfafa Ruth. Ya ce: “Ubangiji ya albarkace ki, ya ɗiyata; wannan alheri na ƙarshe da kika nuna, ya fi na fari, da shi ke ba ki maida hankali ga samari, ko masu-arziki, ko masu-talauci ba.” (Ruth 3:10) “Na fari” da Boaz ya ambata yana nufin aminci da kuma ƙaunar da Ruth ta nuna sa’ad da ta bi Naomi zuwa ƙasar Isra’ila kuma ta kula da ita. “Na ƙarshe” kuma da ya ambata yana nufin yadda Ruth ta yarda ta auri dattijo. Boaz ya lura cewa tun da Ruth matashiya ce, za ta iya nema ta auri saurayi ko da shi mawadaci ne ko a’a. Amma, ta so ta yi alheri ga Naomi da kuma maigidanta da ya rasu. Ta yaya? Tana son sunan mamacin ya ci gaba da wanzuwa a ƙasarsu. Shi ya sa rashin son kai da Ruth ta nuna ya ratsa zuciyar Boaz sosai.

19, 20. (a) Me ya sa Boaz bai auri Ruth nan da nan ba? (b) Ta yaya Boaz ya nuna alheri da kuma fahimi ga Ruth?

19 Boaz ya daɗa ce mata: “Yanzu, ɗiyata, kada ki ji tsoro: dukan abin da kika faɗi, na yi miki: gama dukan mazaunan gari sun sani macen kirki ce ke.” (Ruth 3:11) Ya yi farin ciki domin zai auri Ruth, mai yiwuwa bai yi mamaki ba sa’ad da aka ce shi yake da iko ya fanshe ta. Amma, Boaz mutum ne mai aminci kuma ba ya son ɗaukan mataki da kansa. Ya gaya wa Ruth cewa akwai wani dangi da ya fi shi kusa da mamacin, saboda haka zai fara ba shi damar zama mijinta.

Ruth ta yi suna mai kyau domin ta yi wa mutane da yawa alheri kuma ta daraja su

20 Boaz ya gaya mata ta kwanta har sai gari ya soma wayewa, sai ta koma gida ba tare da kowa ya sani ba. Ba ya son ya ɓata sunanta da kuma nasa, tun da mutane za su iya zato cewa sun yi lalata. Sa’an nan Ruth ta ƙara kwantawa a ƙafafunsa, wataƙila hankalinta ya kwanta sosai don yadda ya amsa roƙonta. Da duku-duku, Boaz ya cika mayafinta da sha’ir kuma ta nufi Bai’talami.—Karanta Ruth 3:13-15.

21. Me ya sa aka san Ruth a matsayin “macen kirki,” kuma ta yaya za mu bi misalinta?

21 Boaz ya ce kowa ya san cewa ita “macen kirki ce.” Babu shakka, hakan ya ratsa zuciyarta. Wannan halinta mai kyau ne ya sa ta yarda ta bauta wa Jehobah. Ta nuna alheri da kuma halin kirki ga Naomi da mutanenta, kuma ta koyi al’adar ƙasarsu. Idan muka yi koyi da bangaskiyar Ruth, za mu so mu daraja mutane da kuma al’adarsu sosai. Hakan kuma zai sa mu kasance da halin kirki.

Ruth Ta Sami Wurin Hutawa

22, 23. (a) Mece ce ma’anar kyautar da Boaz ya ba Ruth? (Ka kuma duba hasiya.) (b) Mene ne Naomi ta gaya wa Ruth ta yi?

22 Sa’ad da Ruth ta iso gida, sai Naomi ta ce: “Wace ce, ya ɗiyata?” Mai yiwuwa ta yi tambayar ce domin gari ya yi duhu, kuma ƙila tana so ta san ko har ila Ruth gwauruwa ce ko kuma wadda ke shirin aure. Nan da nan sai Ruth ta gaya wa surukarta dukan abin da ya faru tsakaninta da Boaz. Ta kuma ba ta kyautar sha’ir da Boaz ya ce a ba ta. *Ruth 3:16, 17.

23 Naomi ta gaya wa Ruth ta zauna a gida maimakon zuwa yin kala. Ta cewa Ruth: “Mutumin nan ba za shi huta ba, sai ya gama zancen yau.”—Ruth 3:18.

24, 25. (a) Ta yaya Boaz ya nuna cewa shi nagari ne kuma ba ya son kai? (b) Ta yaya aka albarkaci Ruth?

24 Naomi ta san cewa abin da Boaz zai yi ke nan. Ya je ƙofar birnin inda dattawa suke yawan zama, kuma ya jira har sa’ad da wanda ya fi shi kusa da mamacin ya zo wucewa. Boaz ya ba mutumin damar auran Ruth a gaban shaidu. Amma, mutumin ya ƙi yin hakan don wai hakan zai iya ɓata nasa gādon. Sai Boaz ya furta a gaban shaidun cewa zai fanshe Ruth. Hakan yana nufin cewa zai sayi filin mijin Naomi, wato Elimelech kuma zai auri Ruth matar Mahlon da ya rasu. Boaz ya faɗi cewa yin hakan zai ‘rayar da sunan matacce tare da gādonsa.’ (Ruth 4:1-10) Boaz kuwa nagari ne kuma ba ya son kai.

25 Boaz ya auri Ruth. Bayan haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji kuwa ya sa ta yi juna biyu, ta haifi ɗa.” Matan Bai’talami sun albarkaci Naomi kuma suka yaba wa Ruth don ta fi ’ya’ya bakwai ga Naomi. A sakamako, ɗan Ruth ya zama kakan-kakannin Sarki Dauda. (Ruth 4:11-22) Dauda kuma ya zama kakan-kakannin Yesu Kristi.—Mat. 1:1. *

Jehobah ya albarkaci Ruth da damar zama kakan-kakannin Almasihu

26. Mene ne misalan Ruth da Naomi suka tuna mana?

26 An albarkaci Ruth da kuma Naomi wadda ta taimaka mata wajen renon ɗan kamar nata. Misalin waɗannan mata biyu ya tuna mana cewa Jehobah yana lura da waɗanda suke ƙoƙartawa don su yi wa iyalansu tanadi kuma su bauta masa tare da bayinsa. Yana sāka wa amintattu da suke da halin kirki, kamar Boaz da Naomi da kuma Ruth.

^ sakin layi na 7 Kamar yadda Naomi ta ce, Jehobah yana nuna alheri ga masu rai da marasa rai. Naomi ta yi rashin mijinta da ’ya’yanta. Ruth kuma ta yi rashin mijinta. Babu shakka, Naomi tana ƙaunar mijinta da ’ya’yanta, kuma Ruth tana ƙaunar mijinta wanda shi ne ɗan Naomi. Duk alherin da aka yi wa waɗannan matan kamar ana yi wa mazajensu ne, domin tabbas, da a ce suna da rai da za su kula da matan.

^ sakin layi na 11 Ɗan’uwan mamacin ne yake da iko ya auri matar, amma idan ya ƙi, sai wani danginsa na kusa ya aure ta. Hakan ma ake yi da gādonsa.—Lit. Lis. 27:5-11.

^ sakin layi na 22 Boaz ya ba Ruth mudu shida na sha’ir, amma ba a san nauyinsa ba. Mai yiwuwa hakan yana nufin cewa kamar yadda ake aiki kwanaki shida kuma a huta a ranar Assabaci, Ruth ma za ta huta yanzu a gidan mijinta bayan wahalar da ta sha. A wani ɓangare kuma, mai yiwuwa mudu shida na sha’ir ne Ruth za ta iya ɗauka.

^ sakin layi na 25 Ruth tana ɗaya daga cikin mata biyar da aka ambata a Littafi Mai Tsarki cewa su kakan-kakannin Yesu ne. Ɗaya daga ciki kuma Rahab ce, wadda ta haifi Boaz. (Mat. 1:3, 5, 6, 16) Kamar Ruth, ita ba Ba’isra’iliya ba ce.