Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

“Ga ni, Baiwar Ubangiji”

“Ga ni, Baiwar Ubangiji”

1, 2. (a) Wace gaisuwa ce wani baƙo ya yi wa Maryamu? (b) Wace shawara ce Maryamu za ta tsai da, kuma ta yaya hakan zai canja rayuwarta?

MARYAMU ta yi mamaki sosai sa’ad da baƙon ya shigo gidansu. Bai nemi ganin mahaifinta ko mahaifiyarta ba, amma ita ya zo gani! Ta tabbata cewa ba ɗan Nazarat ba ne, domin ƙaramin gari ne, kuma baƙi ba su da wuyan ganewa. Yana da sauƙi a gane cewa wannan baƙo ne. Ya gai da Maryamu a hanyar da ba ta saba ji ba, ya ce: “A gaishe ki, ke da ki ke mai-samun alheri, Ubangiji yana tare da ke.”—Karanta Luka 1:26-28.

2 Da waɗannan kalaman ne Littafi Mai Tsarki ya gabatar da Maryamu, ’yar Heli a garin Nazarat da ke Galili. Littafi Mai Tsarki ya gabatar da ita ne a lokacin da za ta yanke shawarwari masu muhimmanci a rayuwarta. An riga an sanya ranar auren Maryamu da Yusufu kafinta, mutum marar arziki amma mai aminci. Saboda haka, za a iya cewa ta riga ta tsara yadda rayuwarta za ta kasance, za ta taimaka wa maigidanta Yusufu su yi rainon yaransu tare. Farat ɗaya, sai ga wannan baƙon da ya kawo mata saƙon da zai canja rayuwarta daga wurin Allah.

3, 4. Idan muna so mu san Maryamu, mene ne muke bukatar mu yi watsi da shi, kuma me ya kamata mu mai da wa hankali?

3 Mutane da yawa sun yi mamaki cewa Littafi Mai Tsarki bai gaya mana abubuwa masu yawa game da Maryamu ba. Ya gaya mana abubuwa kaɗan ne kawai game da yadda ta girma da kuma halayenta, amma bai gaya mana kome game da siffarta ba. Duk da haka, abin da Kalmar Allah ta ce game da ita ya bayyana abubuwa masu yawa.

4 Idan muna so mu san Maryamu sosai, bai kamata mu mai da hankali ga abin da addinai suka koya wa mabiyansu game da ita da kuma irin zane-zane da mutane da yawa suka yi game da ita ba. Ya kamata mu ƙi da koyarwar addinai da ta ɗaukaka wannan mace mai tawali’u ta wajen kiranta da laƙabi kamar “Uwar Allah” da kuma “Sarauniyar Sama.” Maimakon haka, bari mu mai da hankali a kan ainihin abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da ita. Hakan zai sa mu fahimci bangaskiyarta sosai da kuma yadda za mu yi koyi da ita.

Mala’ika Ya Ziyarce Ta

5. (a) Mene ne za mu koya daga Maryamu a yadda ta ji game da gaisuwar Jibra’ilu? (b) Wane darasi mai muhimmanci ne za mu koya daga misalin Maryamu?

5 Wanda ya ziyarci Maryamu ba mutum ba ne. Mala’ika Jibra’ilu ne. Sa’ad da ya kira Maryamu “mai-samun alheri,” sai “hankalinta ya tashi ƙwarai” domin kalamansa kuma ta yi mamakin jin irin wannan gaisuwa. (Luk 1:29) Wane ne ya yi mata alheri? Maryamu ba ta sa ran samun alheri daga wurin mutane ba. Amma mala’ikan yana magana ne game da alherin Jehobah Allah. Al’amarin ya dame ta sosai. Duk da haka, ba ta soma yin fahariya cewa ta sami alherin Allah ba. Misalin Maryamu ya koya mana cewa ya kamata mu yi ƙoƙari mu samu alherin Allah, kuma kada mu yi fahariya cewa mun riga mun samu. Allah ya ƙi jinin masu girman kai, amma yana ƙauna da kuma tallafa wa masu tawali’u.—Yaƙ. 4:6.

Maryamu ba ta yi fahariya cewa ta sami alherin Allah ba

6. Wane aiki ne na musamman mala’ikan ya ba Maryamu?

6 Maryamu tana bukatar ta kasance da tawali’u, domin mala’ikan ya ba ta aiki na musamman. Ya bayyana mata cewa za ta haifi ɗan da zai zama mafi girma a cikin ’yan Adam. Jibra’ilu ya ce: “Ubangiji Allah kuma za ya ba shi kursiyi na ubansa Dawuda: za shi yi mulki kuma bisa gidan Yakubu har abada; mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.” (Luk 1:32, 33) Babu shakka, Maryamu ta san alkawarin da Allah ya yi wa Dauda fiye da shekaru dubu ɗaya da suka shige, wato wani a cikin zuriyarsa zai yi sarauta har abada. (2 Sam. 7:12, 13) Hakan ya nuna cewa ɗanta zai zama Almasihun da mutanen Allah suke begen gani tun ƙarnukan da suka shige!

Mala’ika Jibra’ilu ya ba Maryamu gata na musamman

7. (a) Mene ne tambayar da Maryamu ta yi ya nuna? (b) Mene ne matasa a yau za su iya koya daga wajen Maryamu?

7 Ƙari ga haka, mala’ikan ya gaya mata cewa za a kira ɗanta “Ɗan Maɗaukaki.” Ta yaya mace za ta haifi Ɗan Allah? Hakika, ta yaya Maryamu za ta iya haifar ɗa da yake ita da Yusufu suna shirin aure? Sai Maryamu ta yi wannan tambayar: “Ƙaƙa wannan za shi zama, da shi ke ban san namiji ba?” (Luk 1:34) Ka lura cewa Maryamu ba ta ji kunyar faɗin cewa ba ta san namiji ba. Akasin haka, ta ɗauki yanayinta da tamani. A yau, yawancin matasa suna ɗokin kawar da budurcinsu kuma su yi wa waɗanda ba su yi hakan ba ba’a. Babu shakka wannan duniyar ta canja. Amma, Jehobah bai canja ba. (Mal. 3:6) Kamar yadda yake a zamanin Maryamu, Jehobah yana ɗaukan waɗanda suke bin mizanansa na ɗabi’a da tamani.—Karanta Ibraniyawa 13:4.

8. Ta yaya Maryamu ajiza za ta iya haifar ɗa kamiltacce?

8 Maryamu ajiza ce, ko da yake ita baiwar Allah ce mai aminci. Ta yaya za ta iya haifar ɗa kamiltacce, wato Ɗan Allah? Jibra’ilu ya bayyana mata cewa: “Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, ikon Maɗaukaki kuma za ya inuwantar da ke: domin wannan kuwa [ɗa] da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.” (Luk 1:35) Kalmar nan tsarki tana nufin abu mai “tsabta” da kuma “marar aibi.” Yara suna gādan zunubi daga iyayensu. Amma a wannan batun, Jehobah zai yi mu’ujizar da ba a taɓa yi ba. Zai mai da ran Ɗansa daga sama zuwa cikin mahaifar Maryamu kuma ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki ya “inuwantar da” ita, hakan zai kāre yaron daga zama ajizi. Maryamu ta gaskata da alkawarin da mala’ikan ya yi kuwa? Mene ne ta ce?

Amsar Maryamu ga Jibra’ilu

9. (a) Me ya sa wasu suke shakkar labarin Maryamu? (b) A wace hanya ce Jibra’ilu ya ƙarfafa bangaskiyar Maryamu?

9 Mutane da yawa, tare da wasu ’yan tauhidin Kiristendom ba su yarda cewa budurwa za ta iya haihuwa ba. Duk da iliminsu, sun kasa fahimtar gaskiya marar wuya, wato yadda Jibra’ilu ya ce, “babu magana daga wurin Allah da za ta rasa iko.” (Luk 1:37) Maryamu ta gaskata da abin da Jibra’ilu ya ce, domin ita budurwa ce mai bangaskiya sosai kuma irin wannan bangaskiyar ba mai ruɗarwa ba ce. Hakika, Maryamu tana bukatar tabbaci da zai sa ta kasance da bangaskiya. Jibra’ilu yana a shirye ya ba ta ƙarin bayani. Ya gaya mata game da ’yar’uwarta Alisabatu tsohuwa, wadda ba ta taɓa haihuwa ba. Amma, Allah ya sa ta yi juna biyu ta hanyar mu’ujiza!

10. Me ya sa bai kamata mu yi tunani cewa gatan da aka ba Maryamu bai jawo mata ƙalubale ba?

10 Mene ne Maryamu za ta yi? An ba ta aiki na musamman kuma tana da tabbaci cewa Allah zai yi dukan abin da Jibra’ilu ya gaya mata. Ko da yake tana da gatar haifar ɗan Allah, wannan yanayin ya sa ta fuskanci ƙalubale. Me ya sa? Na farko, domin an riga an sa wa ita da Yusufu rana. Shin zai so ya aure ta idan ya gane cewa tana da juna biyu? Dalili na biyu shi ne, aikin da aka ba ta ja ne. Za ta haifi ɗa mafi girma cikin dukan halittun Allah, wato Ɗansa ƙaunatacce! Tana bukatar ta kula da shi sa’ad da yake jariri kuma ta kāre shi a wannan muguwar duniya. Hakika, wannan jan aiki ne!

11, 12. (a) Mene ne bayin Allah masu aminci suka yi sa’ad da Allah ya ba su aiki mai wuya? (b) Mene ne amsar da Maryamu ta ba Jibra’ilu ta nuna?

11 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa maza masu ƙarfi da kuma aminci sun yi jinkirin karɓan aiki mai wuya daga wurin Allah. Musa ya ce shi mai nauyin baki ne saboda haka bai cancanci zama kakakin Allah ba. (Fit. 4:10) Irmiya ya ce shi “yaro ne,” kuma bai isa yin aikin da Allah ya ba shi. (Irm. 1:6) Yunana kuma ya gudu daga aikin da aka ba shi! (Yun. 1:3) Maryamu kuma fa?

12 Har wa yau, mutane da yawa sun san amsar da ta ba da cikin tawali’u da kuma biyayya. Ta gaya wa Jibra’ilu cewa: “Ga ni, baiwar Ubangiji; bisa ga faɗinka shi zama mani.” (Luk 1:38) Baiwa ce mafi ƙanƙanta a cikin bayi, rayuwarta gabaki ɗaya tana hannun ubangidanta. Yadda Maryamu ta ɗauki Ubangijinta Jehobah ke nan. Ta san cewa Allah zai kāre ta, yana nuna aminci ga masu aminci kuma zai albarkace ta sa’ad da take yin iya ƙoƙarinta wajen yin wannan jan aikin da ke gabanta.—Zab. 31:23.

13. Ta yaya za mu amfana daga misalin Maryamu idan muna ganin aikin da Allah ya ba mu yana da wuya ko kuma ba za mu iya yin sa ba?

13 A wasu lokatai, Allah yakan ce mu yi wani abu da muke ganin yana da wuya ko kuma ba zai yiwu ba. Amma, ya tabbatar mana ta Kalmarsa cewa za mu iya dogara a gare shi kamar yadda Maryamu ta yi. (Mis. 3:5, 6) Shin za mu dogara a gare shi kuwa? Idan muka yi hakan, zai albarkace mu kuma hakan zai sa mu ƙara kasancewa da bangaskiya a gare shi.

Ta Ziyarci Alisabatu

14, 15. (a) Ta yaya Jehobah ya albarkaci Maryamu sa’ad da ta ziyarci Alisabatu da Zakariya? (b) Mene ne kalamin Maryamu da ke rubuce cikin Luka 1:46-55 ya nuna game da ita?

14 Kalamin da Jibra’ilu ya faɗa game da Alisabatu ya ƙarfafa Maryamu sosai. Alisabatu ce kaɗai macen da za ta fahimci yanayinta sosai. Nan da nan Maryamu ta tafi ƙasar Yahudiya mai tsaunuka, tafiyar wajen kwana uku ko huɗu. Sa’ad da ta shiga gidan Alisabatu da Zakariya firist, Jehobah ya albarkace ta ta wajen ba ta ƙwaƙƙwaran tabbaci don ya ƙarfafa bangaskiyarta. Sa’ad da Alisabatu ta ji gaisuwar Maryamu, nan da nan jaririn da ke cikin cikinta ya motsa don murna. An cika ta da ruhu mai tsarki kuma ta kira Maryamu “uwar Ubangijina.” Allah ya nuna wa Alisabatu cewa ɗan Maryamu zai zama Ubangijinta, Almasihu. Bugu da ƙari, an hure ta ta yaba wa Maryamu saboda biyayyar da take yi cikin aminci. Ta ce: “Ita fa da ta bada gaskiya mai-albarka ce.” (Luk 1:39-45) Hakika, dukan alkawuran da Jehobah ya yi wa Maryamu za su cika!

Abotar Maryamu da Alisabatu albarka ce a gare su

15 Bayan haka, sai Maryamu ta yi magana. Kalamin da ta furta yana nan a rubuce cikin Kalmar Allah. (Karanta Luka 1:46-55.) Wannan shi ne kalami mafi yawa da Maryamu ta yi da ke rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma ya bayyana abubuwa masu yawa game da ita. Ya nuna halinta na yin hamdala, yayin da take yaba wa Jehobah domin gatan da ya ba ta na zama mahaifiyar Almasihu. Kalaminta kuma ya nuna irin bangaskiyar da take da shi sa’ad da ta ce Jehobah yana ƙasƙantar da masu girman kai da masu iko, kuma yana taimaka wa masu tawali’u da talakawa da suke so su bauta masa. Hakan kuma ya bayyana cewa ta san Nassosi sosai. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa ta yi ƙaulin Nassosin Ibrananci fiye da sau ashirin! *

16, 17. (a) Ta yaya Maryamu da kuma ɗanta suka nuna halin da ya kamata mu yi koyi da shi? (b) Mene ne ziyarar da Maryamu ta kai wa Alisabatu ta tuna mana?

16 Babu shakka, Maryamu ta yi bimbini sosai a kan Kalmar Allah. Duk da haka, ta kasance da tawali’u, ta gwammace ta yi ƙaulin Nassosi maimakon ta faɗi ra’ayinta. Jaririn da ke girma a cikin mahaifarta ya nuna irin wannan halin sa’ad da aka haife shi kuma ya girma. Ya ce: “Koyarwana ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni.” (Yoh. 7:16) Zai dace mu tambayi kanmu: ‘Ina daraja Kalmar Allah haka kuwa? Ko kuwa na fi son ra’ayina da kuma koyarwata?’ Maryamu ta kasance da halin da ya dace.

17 Maryamu ta zauna tare da Alisabatu wajen wata uku, kuma babu shakka, sun ƙarfafa juna. (Luk 1:56) Labarin Littafi Mai Tsarki game da wannan ziyara ya nuna mana cewa yin abota yakan zama albarka. Idan muka yi abota da waɗanda suke ƙaunar Jehobah sosai, muna da tabbaci cewa za mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. (Mis. 13:20) A ƙarshe, lokaci ya yi da Maryamu za ta koma gida. Mene ne Yusufu zai ce idan ya gane yanayin da take ciki?

Maryamu da Yusufu

18. Mene ne Maryamu ta gaya wa Yusufu, kuma yaya ya ji?

18 Maryamu ba ta jira har sai cikinta ya fito kafin ta gaya wa Yusufu ba. Babu shakka, tana bukatar ta gaya masa. Kafin ta yi hakan, wataƙila ta yi tunanin yadda wannan mutumi mai tsoron Allah zai ji idan ta gaya masa. Duk da haka, ta je ta gaya masa duk abin da ta fuskanta. Abin ya dami Yusufu sosai. Yana so ya gaskata da ita, amma abin da ta gaya masa bai taɓa faruwa ba. Littafi Mai Tsarki bai gaya mana irin tunanin da ya yi a zuciyarsa ba. Amma ya gaya mana cewa ya yanke shawara zai sake ta, domin a zamanin dā ana ɗaukan waɗanda aka sa wa rana a matsayin ma’aurata. Yusufu ba ya so ya kunyatar da ita a gaban jama’a, sai ya yi niyyar ya sake ta a ɓoye. (Mat. 1:18, 19) Maryamu ba ta ji daɗin ganin cewa Yusufu yana baƙin ciki saboda irin wannan yanayin da bai taɓa faruwa ba. Duk da haka, ba ta ga laifin Yusufu na ƙin gaskata da ita ba.

19. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Yusufu ya ɗauki matakin da ya dace?

19 Jehobah bai ƙyale Yusufu ya ɗauki matakin da yake son ya ɗauka ba. A cikin mafarki, mala’ikan Allah ya gaya masa cewa Maryamu ta yi juna biyu ta hanyar mu’ujiza. Hakan ya kwantar masa da hankali! A yanzu, Yusufu ya yi abin da Jehobah ya ce ya yi. Ya auri Maryamu, kuma ya ɗauki nauyin kula da Ɗan Jehobah.—Mat. 1:20-24.

20, 21. Mene ne ma’aurata da waɗanda suke neman aure za su iya koya daga misalin Maryamu da Yusufu?

20 Ya kamata ma’aurata da waɗanda suke tunanin yin aure a nan gaba su bi misalin da wannan ma’auratan suka kafa shekaru 2,000 da suka shige. Sa’ad da Yusufu ya ga yadda matarsa take yin aikinta kuma take kula da yaronta, ya yi farin ciki cewa mala’ikan Jehobah ya yi masa ja-gora. Yusufu ya ga muhimmancin dogara ga Jehobah sa’ad da yake yanke shawarwari masu muhimmanci. (Zab. 37:5; Mis. 18:13) Babu shakka, ya mai da hankali sosai kuma ya nuna sanin yakamata sa’ad da yake yanke shawarwari a matsayin shugaban iyali.

21 A wani ɓangare kuma, mene ne za mu iya koya daga yadda Maryamu ta yarda ta auri Yusufu ko da yake ya yi shakkar abin da ta gaya masa? Duk da cewa a dā bai yarda da labarin da ta ba shi ba, ta ci gaba da yi masa biyayya a matsayin wanda zai zama shugaban iyali. Ta ga cewa yana da muhimmanci ta yi haƙuri kuma wannan darasi ne mai kyau ga mata Kiristoci a yau. A ƙarshe, waɗannan abubuwan da suka faru sun koya wa Yusufu da Maryamu muhimmancin zama masu yin gaskiya da kuma tattaunawa da juna.—Karanta Misalai 15:22.

22. Yaya Yusufu da Maryamu suka soma aurensu, mene ne za su fuskanta a nan gaba?

22 Wannan ma’auratan sun soma aurensu da kyau. Suna ƙaunar Jehobah Allah fiye da kome kuma suna ɗokin yin abin da yake so a matsayin iyaye masu kula. Babu shakka, za su samu albarka mai girma kuma su fuskanci ƙalubale sosai. Suna da hakkin yin rainon Yesu, wanda zai yi girma ya zama mutumi mafi girma a duniya.

^ sakin layi na 15 Kamar dai Maryamu ta yi ƙaulin kalamin Hannatu mace mai aminci, wadda Jehobah ya albarkace ta da ɗa.—Ka duba akwatin nan “Addu’o’i Biyu Masu Ma’ana Sosai,” da ke Babi na 6.

Maryamu ta san cewa Jehobah Allah wanda yake kāre masu aminci zai kāre ta