Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

Ya Shawo Kan Tsoro da Kuma Shakka

Ya Shawo Kan Tsoro da Kuma Shakka

1-3. Mene ne Bitrus ya shaida da ba zai taɓa mantawa ba, kuma me ya faru a daren?

BITRUS ya yi dare yana tuƙa jirgin ruwa. Shin hasken da ya hango ta yamma ya nuna cewa gari ya soma wayewa ne? Ya riga ya gaji da tuƙa jirgin. Iskar da ke kaɗa sumansa tana ta da ruwan Tekun Galili. Raƙuman ruwa suna ta kaɗa jirgin kamun kifin kuma suna ta fesa wa Bitrus ruwa. Duk da haka, ya ci gaba da tuƙi.

2 Bitrus da abokansa sun bar Yesu kaɗai a bakin teku. A ranar, sun ga yadda Yesu ya ciyar da jama’a da gurasa guda biyar da kuma kifi biyu. Mutanen sun nemi su naɗa shi sarki, amma ba ya so ya saka hannu a siyasa. Yana kuma so ya koya wa mabiyansa haɗarin saka hannu a siyasa. Sa’ad da Yesu ya kauce wa jama’ar, sai ya gaya wa almajiransa su tuƙa jirgi zuwa wancan hayin kogin, shi kuma ya hau kan dutse don ya yi addu’a shi kaɗai.—Mar. 6:35-45; karanta Yohanna 6:14-17.

3 Wata ya riga ya fito sa’ad da almajiran suka shiga cikin jirgin kuma a yanzu gari ya soma wayewa. Duk da haka, sun yi ƙoƙari sun yi nisa kaɗan. Ƙarfin raƙuman ruwa da kuma iskar da ake yi sun hana almajiran tattaunawa. Wataƙila, Bitrus yana tunani.

Bitrus ya koyi abubuwa da yawa game da Yesu cikin shekaru biyu, amma ba shi ke nan ba

4. Me ya sa ya dace mu yi koyi da misalin Bitrus?

4 Bitrus yana da abubuwa da yawa da zai yi tunani a kai! Yanzu ya yi wajen shekara biyu yana bin Yesu Banazare. Ya koyi abubuwa da yawa, amma yana da ƙarin abubuwan da zai koya. Bitrus bai ƙyale tsoro da kuma shakka su hana shi bin Yesu da kuma bauta wa Jehobah ba, kuma za mu iya yin koyi da shi. Bari mu ga yadda hakan ya faru.

“Mun Sami Almasihu”!

5, 6. Wane irin aiki ne Bitrus yake yi?

5 Bitrus ba zai taɓa manta da ranar da ya haɗu da Yesu Banazare ba. Ɗan’uwansa Andarawus ne ya soma gaya masa cewa: “Mun sami Almasihu.” Bayan hakan, sai salon rayuwar Bitrus ya canja baki ɗaya.—Yohanna 1:41.

6 Bitrus yana da zama ne a birnin Kafarnahum da ke kusa da Tekun Galili. Shi da Andarawus da kuma yaran Zebedee, wato Yaƙub da Yohanna suna sana’ar kamun kifi tare. Waɗanda suke zama tare da Bitrus su ne matarsa, surukarsa da kuma ɗan’uwansa Andarawus. Biyan bukatun waɗannan mutanen da sana’ar kamun kifi yana bukatar yin aiki tuƙuru da kuzari da kuma gwaninta. Ka yi tunanin daren da suke yi suna aiki mai wuya, suna jefa tarun tsakanin jirage biyu kuma su kwashi duk irin kifin da suka kama zuwa bakin teku. Za mu kuma iya yin tunanin kwanakin da suke yi suna aiki tuƙuru, suna ware kifayen su sayar kuma su gyara tarun.

7. Wane labari ne Bitrus ya ji game da Almasihu, kuma me ya sa hakan albishiri ne?

7 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Andarawus almajirin Yohanna Mai Baftisma ne. Babu shakka, Bitrus ya saurari abin da ɗan’uwansa ya gaya masa game da saƙon Yohanna. Wata rana, Andarawus ya ga Yohanna yana nuna Yesu Banazare yana cewa: “Duba, ga Ɗan rago na Allah!” Nan take Andarawus ya zama mabiyin Yesu kuma ya gaya wa Bitrus wannan albishirin cewa, Almasihun ya bayyana! (Yoh. 1:35-41) Bayan tawayen da aka yi a gonar Adnin shekaru dubu huɗu kafin zamanin su Bitrus, Jehobah ya yi alkawari cewa wani mutumi na musamman zai zo don ya yi tanadin bege na gaske ga ’yan Adam. (Far. 3:15) Andarawus ya haɗu da wannan Mai Ceton, wato Almasihu! Bitrus ma ya hanzarta don ya haɗu da Yesu.

8. Mece ce ma’anar sunan da Yesu ya sa wa Bitrus, kuma me ya sa wasu suke ganin sunan bai dace da shi ba?

8 Kafin wannan ranar, ana kiran Bitrus, Siman ko Saminu. Amma Yesu ya kalle shi kuma ya ce: “Kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas, wato Bitrus.” (Yoh. 1:42, Littafi Mai Tsarki) “Kefas” suna gama gari ne wanda ke nufin “dutse” ko “fa.” Babu shakka, kalaman Yesu annabci ne. Ya ga cewa Bitrus zai zama kamar dutse, wanda zai kasance da tasiri ga mabiyan Kristi. Bitrus ya ga kansa hakan kuwa? Da kyar. Wasu da ke karanta Linjila a yau ba sa ganin Bitrus a matsayin mutum mai tsayin daka, wanda za a dogara da shi. Wasu sun ce labarin Bitrus da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ba ya tsayin daka kuma bai iya tsai da shawara ba.

9. Mene ne Jehobah da Ɗansa suke mai da wa hankali, kuma me ya sa za mu amince da ra’ayinsu?

9 Bitrus ya yi kuskure da yawa kuma Yesu ya san da hakan. Amma Yesu da kuma Jehobah sun fi mai da hankali ga hali mai kyau na mutane. Yesu ya lura cewa Bitrus yana da halaye masu kyau, kuma yana so ya taimaka masa ya ci gaba da nuna waɗannan halayen. Jehobah da Ɗansa ma a yau suna mai da hankali ga halayenmu masu kyau. Muna iya yin shakka cewa muna da halaye masu kyau. Amma, muna bukatar mu amince da ra’ayinsu kuma mu yarda su koyar da mu kuma su yi mana gyara kamar yadda suka yi wa Bitrus.Karanta 1 Yohanna 3:19, 20.

“Kada Ka Ji Tsoro”

10. Mene ne Bitrus ya shaida, kuma ga mene ne ya koma?

10 Wataƙila Bitrus ya bi Yesu sa’ad da ya soma wa’azi. Mai yiwuwa, ya ga sa’ad da Yesu ya yi mu’ujizarsa ta farko, wato juya ruwa zuwa inabi a bikin auren da aka yi a Kana. Mafi muhimmanci ma, ya ji koyarwar Yesu mai daɗaɗawa game da Mulkin Allah. Duk da haka, ya bar Yesu kuma ya koma sana’arsa ta kamun kifi. Watanni kaɗan bayan hakan, Bitrus ya sake haɗuwa da Yesu, sai Yesu ya ce ya ci gaba da bin sa muddar ransa.

11, 12. (a) Wane irin aiki ne Bitrus ya yi daddare? (b) Mene ne wataƙila Bitrus yake tunani yayin da Yesu yake wa’azi?

11 Bitrus bai daɗe da kammala aiki mai ban haushi da ya yi daddare ba. Sun jefa tarunsu sau da yawa, amma ba su kama kifi ba. Babu shakka, Bitrus ya yi amfani da dukan gwanintarsa kuma ya gwada wurare dabam-dabam don ya tabbata cewa ya kama kifi. Kamar sauran masunta, babu shakka da akwai lokacin da ya ji kamar ya faɗa cikin kogin ya kakkamo kifayen ya saka su cikin tarunsa. Amma, irin wannan tunanin zai daɗa sa shi takaici ne kawai. Bitrus bai fito yin wasa ba domin da wannan sana’ar yake ciyar da iyalinsa. A ƙarshe, ya dawo bakin kogin da hannu wofi. Duk da haka, yana bukatar ya wanke tarun. Yayin da yake yin hakan, sai Yesu ya iso wurinsa.

Bitrus bai taɓa gajiya da jin Yesu yana nanata jigon wa’azinsa ba, wato Mulkin Allah

12 Jama’a sun yi yawa kuma sun kewaye Yesu suna sauraron wa’azinsa, shi ya sa ya shiga cikin jirgin Bitrus kuma ya gaya masa ya ɗan ja jirgin zuwa cikin ruwa. Sai Yesu ya koyar da taron da babbar murya. Bitrus da mutanen da ke bakin kogin sun saurara sosai. Bai taɓa nuna cewa ya gaji da jin yadda Yesu yake tattauna ainihin jigon wa’azinsa ba, wato Mulkin Allah. Gata ne ga Bitrus ya taimaka wa Kristi wajen yaɗa wannan saƙon bege a ƙasar baki ɗaya! Amma, hakan zai kasance da sauƙi kuwa? Ta yaya Bitrus zai riƙa ciyar da iyalinsa? Wataƙila hankalinsa ya sake komawa ga wahalar da ya sha da daddare yana sū.—Luk. 5:1-3.

13, 14. Wace mu’ujiza ce Yesu ya yi don Bitrus, kuma yaya Bitrus ya ji?

13 Sa’ad da Yesu ya kammala, sai ya ce wa Bitrus: “A zakuɗa zuwa wuri mai-zurfi, ku jefa tarorinku, domin sū.” Bitrus yana cike da shakka. Ya ce: “Ubangiji, dukan dare muka yi wahala, ba mu sami kome ba: amma bisa maganarka sai in jefa tarori.” Babu shakka, Bitrus bai so ya sake jefa tarunsa ba, domin bai daɗe da ya gama wanke shi ba. Ban da haka ma, kifaye ba sa fita cin abinci a lokacin! Duk da haka, ya yi biyayya, kuma wataƙila ya gaya wa abokan aikinsa da suke ɗayan jirgin su bi shi.—Luk 5:4, 5.

14 Bitrus ya ji wani irin nauyi sa’ad da ya soma jan tarun. Abin mamaki, ya sake ja da ƙarfi kuma nan da nan, ya ga kifaye da yawa a cikin tarun! A razane, ya kira mutanen da ke ɗayan jirgin su zo su taimaka masa. Sa’ad da suka zo, sai suka ankara cewa jirgi guda ba zai iya ɗaukan kifayen ba. Suka cika jiragen biyu, amma duk da haka, da akwai saura da yawa. Sai nauyi ya soma nitsar da jiragen. Bitrus ya cika da mamaki. Ya ga yadda Kristi ya yi amfani da ikonsa a dā, amma na wannan karon ya shafe shi da iyalinsa! Yesu yana da iko ya saka kifaye cikin tarun! Tsoro ya kama Bitrus. Ya durƙusa kuma ya ce: “Ka rabu da ni, ya Ubangiji, gama ni mutum mai-zunubi ne.” Ta yaya zai taɓa iya yin tarayya da mutumin da ke amfani da ikon Allah a waɗannan hanyoyin?Karanta Luka 5:6-9.

‘Ubangiji, ni mutum mai zunubi ne’

15. Ta yaya Yesu ya nuna wa Bitrus cewa bai kamata ya ji tsoro ko kuma ya yi shakka ba?

15 Yesu ya ce: “Kada ka ji tsoro; daga nan gaba za ka kama mutane.” (Luk 5:10) Yanzu ba lokacin yin shakka ko jin tsoro ba ne. Bitrus yana bukatar ya mai da hankali ga yin wa’azi, ba ga yadda zai biya bukatun iyalinsa da kuma kasawarsa ba. Yesu yana da aiki mai girma da zai yi, wato hidimar da za ta canja rayuwar mutane. Yana bauta wa Allahn da ke “gafara a yalwace.” (Isha. 55:7) Ya kamata Bitrus ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa ya kula da iyalinsa kuma ya yi hidimarsa.—Mat. 6:33.

16. Mene ne Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna suka yi sa’ad da Yesu ya gayyace su, kuma me ya sa shawarar da suka yanke take da kyau?

16 Bitrus ya ɗauki mataki nan da nan, kamar yadda Yaƙub da Yohanna suka yi. “Suka zo da jiragensu a wajen gaɓa, suka rabu da abubuwa duka, suka bi shi.” (Luk 5:11) Bitrus ya ba da gaskiya ga Yesu da kuma Allahn da ya aiko shi. Wannan shawara ce mafi kyau da ya yanke. Kiristoci a yau da suka shawo kan shakka da kuma tsoron yin hidimar Allah suna da bangaskiya kamar Bitrus. Jehobah yana kula da waɗanda suke dogara gare shi.—Zab. 22:4, 5.

“Don Me Ka Yi Shakka?”

17. Mene ne Bitrus ya tuna bayan ya yi shekara biyu yana bin Yesu?

17 Shekaru biyu bayan lokaci na farko da Bitrus ya haɗu da Yesu, sai ya tuƙa jirginsa a Tekun Galili kamar yadda aka ambata a farkon wannan babin. Ko da yake ba mu san tunanin da yake yi a lokacin ba, amma da akwai abubuwa da yawa da zai iya yin tunani a kai! Yesu ya warkar da surukarsa. Ya ba da Huɗuba a Kan Dutse. Koyarwarsa da ayyukansa masu ban al’ajabi sun nuna sau da yawa cewa shi ne Almasihun da Jehobah ya zaɓa. Bayan ’yan watanni, wataƙila tsoro da kuma shakkar da Bitrus yake yi sun ɗan ragu. Yesu ya zaɓi Bitrus ya zama ɗaya cikin manzanninsa 12! Duk da haka, Bitrus bai daina jin tsoro da yin shakka baki ɗaya ba, kamar yadda za mu tattauna a gaba.

18, 19. (a) Ka bayyana abin da Bitrus ya gani a Tekun Galili. (b) Ta yaya Yesu ya biya bukatar Bitrus?

18 Wajen ƙarfe uku na safe, Bitrus ya daina tuƙa jirgin sai ya ɗaga kansa, kuma ya hangi wani abu a can gaba da raƙuman ruwa yana tafiya! Shin wata ne ke haskaka raƙuman ruwan? A’a, abin da ya hango yana a tsaye. Mutum ne yake tafiya a kan tekun! Sa’ad da mutumin ya yi kusa da su, sai ya so ya wuce su. Cike da tsoro, almajiran suka yi tsammani cewa fatalwa ce. Sai mutumin ya ce: “Kwantar da hankalinku ni ne; kada ku ji tsoro.” Wane ne wannan mutumin? Yesu ne!—Mat. 14:25-27.

19 Bitrus ya amsa: “Ubangiji, idan kai ne, ka umurce ni in zo wurinka a bisa ruwaye.” (Mat. 14:28) Ya nuna gaba gaɗi a matakin da ya fara ɗauka. Cike da sha’awa don wannan mu’ujiza ta musamman, Bitrus ya so ya daɗa nuna zurfin bangaskiyarsa. Ba ya so a bar shi a baya. Sai Yesu ya ce masa ya taho. Bitrus ya hau bakin jirgin sai ya dira a kan tekun. Ka yi tunanin yadda Bitrus ya ji sa’ad da ya ga yana tafiya a kan ruwa. Babu shakka, ya yi mamaki sa’ad da ya soma tafiya zuwa wurin da Yesu yake. Amma, sai wani abu ya soma damunsa.Karanta Matta 14:29.

“Sa’an da ya ga iska, ya ji tsoro”

20. (a) Ta yaya Bitrus ya soma shakka kuma me ya biyo bayan hakan? (b) Wane darasi ne Yesu ya koya masa?

20 Bitrus yana bukatar ya dogara ga Yesu. Yesu ne yake yin amfani da ikon Jehobah wajen sa Bitrus ya yi tafiya a kan raƙuman ruwa. Kuma Yesu yana yin hakan ne don Bitrus yana da bangaskiya. Amma sai hankalin Bitrus ya rabu. Ayar ta ce: “Sa’an da ya ga iska, ya ji tsoro.” Bitrus ya ga yadda raƙumin ruwan yake tura jirgin, yana ta da ruwan, sai ya ji tsoro. Wataƙila ya yi tsammani yana nitsewa cikin ruwan. Sa’ad da ya daɗa jin tsoro, sai bangaskiyarsa ta ragu. Mutumin da ake kira Dutse saboda gaba gaɗinsa, ya soma nitsewa kamar dutse saboda rashin bangaskiya. Bitrus ya iya iyo sosai, amma bai dogara da wannan iyawar ba a yanzu. Sai ya ta da muryarsa, ya ce: “Ubangiji, ka cece ni.” Sai Yesu ya kama hannunsa kuma ya jawo shi. Sa’ad da suke kan tekun, Yesu ya koya wa Bitrus wani darasi mai muhimmanci, ya ce: “Kai mai-ƙanƙantar bangaskiya, don me ka yi shakka?”—Mat. 14:30, 31.

21. Me ya sa shakka take da lahani sosai kuma me ya sa ya kamata mu shawo kanta?

21 ‘Yin shakka.’ Wannan furuci ne mai muhimmanci! Me ya sa? Domin yin shakka yana da lahani sosai. Idan muka ƙyale shakka ta shawo kanmu, bangaskiyarmu za ta iya raunana kuma za mu daina bauta wa Jehobah. Muna bukatar mu daina yin shakka! Ta yaya? Ta wajen yin hankali shimfiɗe. Idan muka mai da hankali ga abubuwan da ke tsorata mu da sa mu sanyin gwiwa da kuma waɗanda za su iya raba hankalinmu daga Jehobah da Ɗansa, shakkarmu za ta ƙaru. Idan muka mai da hankali ga abin da Jehobah da Ɗansa suka yi wa mutanen da suka ƙaunace su da abubuwan da suke yi wa masu ƙaunarsu a yanzu da kuma waɗanda za su yi musu a nan gaba, za mu kasance da bangaskiya sosai.

22. Me ya sa ya kamata mu yi koyi da bangaskiyar Bitrus?

22 Sa’ad da Bitrus ya bi Yesu zuwa cikin jirgin, ya ga raƙumin ruwan na kwantawa. Bitrus tare da sauran almajiran suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.” (Mat. 14:33) Babu shakka, Bitrus ya yi farin ciki sosai sa’ad da safiya ta soma yi. Ya koyi cewa bai kamata ya riƙa shakka da kuma tsoro ba. Hakika, yana da ayyuka masu yawa da zai yi kafin ya zama Kirista mai kama da dutse da Yesu ya annabta. Amma, ya duƙufa ya ci gaba da yin ƙoƙari da kuma samun ci gaba. Abin da kai ma ka duƙufa ka yi ke nan? Idan haka ne, za ka ga cewa bangaskiyar Bitrus abin koyi ne.