Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA BAKWAI

Ya Ci Gaba da Yin Girma a Gaban Jehobah

Ya Ci Gaba da Yin Girma a Gaban Jehobah

1, 2. Wane yanayi ne Isra’ilawa suke ciki sa’ad da Sama’ila ya yi musu magana, kuma me ya sa yake bukatar ya sa su tuba?

SAMA’ILA wanda ya yi hidima a matsayin annabi da kuma alƙali shekaru da yawa, yana kallon mutanensa da ya ce su taru a garin Gilgal. Lokacin rani ne, wataƙila watan Mayu ko kuma Yuni a kalandar zamani. Alkama da ke gonaki sun isa girbi. Mutanen sun yi tsit. Ta yaya Sama’ila zai iya sa mutanen su yi tunani?

2 Mutanen ba su san cewa yanayinsu ya yi muni sosai ba. Sun nace a naɗa musu sarki. Ba su fahimci cewa rashin kunya ne ga Allahnsu Jehobah da kuma annabinsa ba. Sun ƙi da Jehobah a matsayin Sarkinsu! Mene ne Sama’ila zai yi don su tuba?

Misalin Sama’ila sa’ad da yake yaro ya koya mana cewa za mu iya kasancewa da bangaskiya duk da mummunan tasiri

3, 4. (a) Me ya sa Sama’ila ya yi magana game da ƙuruciyarsa? (b) Ta yaya za mu iya amfana daga bangaskiyar Sama’ila?

3 Sama’ila ya gaya wa mutanen cewa: “Ni kuwa na tsufa na yi furfura.” Furfurarsa ta sa mutanen su ga muhimmancin maganarsa. Ya daɗa cewa: “Ni kuwa tun ina saurayi ina tafiya a gabanku har wa yau.” (1 Sam. 11:14, 15; 12:2) Ko da yake Sama’ila ya tsufa, har ila bai mance da ƙuruciyarsa ba. Shawarwarin da ya tsai da tun yana yaro sun taimaka masa ya kasance da bangaskiya kuma ya ci gaba da bauta wa Jehobah.

4 Sama’ila ya kasance da bangaskiya, ko da yake yana tare da mutane masu rashin aminci da kuma biyayya. Hakazalika, yana da wuya mu kasance da bangaskiya a yau domin muna zama da mutane marasa aminci da bangaskiya. (Karanta Luka 18:8.) Bari mu ga abin da za mu iya koya daga misalin da Sama’ila ya kafa sa’ad da yake yaro.

“Yana Hidima a Gaban Ubangiji” Tun Yana Yaro

5, 6. Ta yaya Sama’ila ya bambanta da tsararsa, amma me ya sa iyayensa suke da tabbaci cewa za a kula da shi?

5 Sama’ila bai yi girma kamar tsararsa ba. Me ya sa? Domin ba da daɗewa ba da aka yaye shi, wataƙila sa’ad da yake ɗan shekara uku ko fiye da haka, sai ya soma hidima a mazaunin Jehobah da ke Shiloh. Shiloh yana da nisan mil 20 daga garinsu, wato Ramah. Iyayensa Elkanah da Hannatu, sun keɓe shi ga Jehobah don ya yi masa hidima ta musamman, sun sa ya zama Naziri muddar ransa. * Shin hakan yana nufi cewa iyayensa sun ƙi da shi ne ko kuma ba sa ƙaunarsa?

6 A’a! Sun san cewa za a kula da ɗansu a Shiloh. Babu shakka, Babban Firist Eli zai ɗauki wannan hakkin, don Sama’ila yana aiki tare da shi. Akwai kuma mata da yawa da suke hidima a mazaunin.—Fit. 38:8; Alƙa. 11:34-40.

7, 8. (a) Ta yaya iyayen Sama’ila suke ƙarfafa shi a kowace shekara? (b) Mene ne iyaye a yau za su iya koya daga Hannatu da Elkanah?

7 Ban da haka ma, Hannatu da mijinta ba su mance da ɗansu ƙaunatacce ba, wanda haihuwarsa amsar addu’a ce. Hannatu ta roƙi Allah ya ba ta ɗa, kuma ta yi alkawari cewa za ta keɓe shi ga Jehobah domin ya yi masa hidima muddar ransa. A kowace shekara da Hannatu take ziyartarsa, takan ɗinka masa riga don ya yi hidima da ita a mazaunin. Babu shakka, Sama’ila yana farin ciki sosai sa’ad da suka ziyarce shi. Kuma yana jin daɗin ƙarfafa da kuma ja-gorar da iyayensa suke masa yayin da suke gaya masa cewa yin hidima a mazaunin Jehobah gata ne sosai.

8 Hannatu da Elkanah sun kafa wa iyaye misali mai kyau a yau. Yawancin iyaye sukan fi mai da hankali ga bukatun yaransu, maimakon su taimaka musu su kusaci Jehobah. Iyayen Sama’ila sun sa bauta wa Jehobah kan gaba a rayuwarsu, kuma hakan ya shafi ɗansu sosai sa’ad da ya yi girma.—Karanta Misalai 22:6.

9, 10. (a) Ka kwatanta mazaunin da kuma yadda Sama’ila yake ji game da wannan wuri mai tsarki. (Ka kuma duba hasiya.) (b) Wane aiki ne Sama’ila yake yi, kuma ta yaya matasa a yau za su iya yin koyi da shi?

9 Muna iya yin tunanin yadda yaron yake girma kuma yake sanin wurare dabam dabam da ke tuddan Shiloh. Sa’ad da yake kallon garin da kuma kwarin da ya kewaye shi, yakan yi farin ciki sosai sa’ad da ya ga mazaunin Jehobah. Hakika wannan mazaunin wuri ne mai tsarki. * Musa ne ya ja-goranci ginin mazaunin tun shekara 400 da ta shige, kuma a lokacin, wurin cibiyar bauta wa Jehobah ne a dukan duniya.

10 Sama’ila yana son mazaunin. Littafin da ya rubuta daga baya ya ce: “Sama’ila yana hidima a gaban Ubangiji, yana yaro, yana ɗamarce da [riga ta linen].” (1 Sam. 2:18) Wannan rigar da ya sanya, ta nuna cewa shi mataimakin firistoci ne a mazaunin. Sama’ila ba firist ba ne, amma aikinsa ya ƙunshi buɗe ƙofofin farfajiyar mazaunin kowane safe kuma yana yi wa Eli hidima. Ko da yake yana jin daɗin hidimarsa, amma bayan wasu lokatai, wani abu ya faru a mazaunin Jehobah da ya ɓata masa rai.

Bai Saka Hannu a Ɓatanci Ba

11, 12. (a) Waɗanne irin mutane ne Hophni da Finehas? (b) Wane irin mugunta da ɓatanci ne Hophni da Finehas suka yi a mazaunin? (Ka duba hasiya.)

11 Sa’ad da Sama’ila yake matashi, ya ga mugunta da kuma ɓatanci da suka zama ruwan dare. Eli yana da yara biyu, sunayensu Hophni da Finehas ne. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Amma ’ya’yan Eli ’yan Belial ne: ba su san Ubangiji ba.” (1 Sam. 2:12) Furuci biyu da ke wannan ayar suna da nasaba. Littafi Mai Tsarki ya ce Hophni da Finehas “’yan Belial” ne, domin ba su yi biyayya ga Jehobah ba. Kuma a Ibrananci, kalmar tana nufin “marasa kirki.” Sun ƙi bin mizanan Jehobah, kuma hakan ya sa suka yi wasu zunubai.

12 An bayyana ayyukan firistoci dalla-dalla da kuma yadda za su riƙa miƙa hadayu a mazaunin a cikin Dokar Allah. Me ya sa? Waɗannan hadayun suna wakiltar abubuwan da Allah ya yi don ya gafarta zunubai domin mutane su iya faranta masa rai, kuma su samu albarka da ja-gorarsa. Amma, Hophni da kuma Finehas sun sa sauran firistocin su ƙi daraja waɗannan hadayun. *

13, 14. (a) Ta yaya muguntar da ake yi a mazaunin ta shafi mutane masu aminci? (b) Ta yaya Eli ya kasa cika hakkinsa a matsayin uba da kuma babban firist?

13 Ka yi tunanin irin mamakin da Sama’ila ya yi sa’ad da yake ganin abubuwan da suke faruwa. Yakan ga mutane da yawa, har da talakawa da kuma fakirai da suke zuwa mazaunin, maimakon a taimake su su ƙulla dangantaka da Allah kuma su sami ƙarfafa, sai dai a ci mutuncinsu kuma su tafi ransu a ɓace. Shin yaya Sama’ila ya ji sa’ad da ya ga Hophni da Finehas suna taka Dokar Allah ta wajen yin lalata da wasu matan da ke hidima a mazaunin? (1 Sam. 2:22) Wataƙila Sama’ila ya sa rai cewa Eli zai daidaita yanayin.

Muguntar ’ya’yan Eli ta dami Sama’ila sosai

14 A matsayin babban firist, Eli ne yake da iko ya canja wannan yanayin, kuma shi ne ya kamata ya kula da duk abin da ke faruwa a mazaunin. A matsayin uba, shi ne ya kamata ya yi wa ’ya’yansa gyara. Suna jawo wa kansu da kuma mutane da yawa a ƙasar lahani ta wajen ayyukansu. Amma, Eli bai cika hakkinsa ba a matsayin uba da kuma babban firist. Ya ɗan gargaɗar da su ne kawai. (Karanta 1 Sama’ila 2:23-25.) ’Ya’yansa suna bukatar horo mai tsanani. Sun cancanci mutuwa don zunubansu.

15. Wane saƙo ne Jehobah ya aika wa Eli, kuma mene ne iyalin Eli suka yi bayan sun ji saƙon?

15 Sa’ad da yanayin ya yi tsanani sosai, sai Jehobah ya aika wa Eli saƙon hukunci ta bakin wani annabi da ba a ambata sunansa ba. Jehobah ya ce masa: “Ka fi bada girma ga ’ya’yanka bisa gareni.” Allah ya annabta cewa ’ya’yan Eli za su mutu a rana ɗaya kuma dukan iyalinsa za su sha wuya sosai, za su yi rashin gatan da suke da shi na zama firistoci. Shin wannan hukuncin ya sa sun canja halinsu ne? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sun ƙi yin hakan.—1 Sam. 2:27–3:1.

16. (a) Ta yaya Sama’ila ya samu ci gaba? (b) Shin ci gabansa ya sa ka farin ciki kuwa? Ka bayyana.

16 Ta yaya wannan ɓatancin ya shafi Sama’ila? Duk da wannan yanayin, Sama’ila ya yi girma kuma yana samun ci gaba a hidimarsa ga Jehobah. Littafin 1 Sama’ila 2:18 ya ce: “Sama’ila yana hidima a gaban Ubangiji, yana yaro.” Har sa’ad da Sama’ila yake yaro, ya mai da hankali a hidimarsa ga Allah. Aya ta 21 ta wannan surar ta ce: “Yaron fa Sama’ila ya yi girma a gaban Ubangiji.” Sa’ad da yake girma, dangantakarsa da Jehobah ta daɗa danƙo kuma irin wannan dangantakar ce za ta iya kāre mutum daga kowane irin ɓatanci.

17, 18. (a) Ta yaya matasa Kiristoci za su iya yin koyi da misalin Sama’ila sa’ad da suka fuskanci ɓatanci? (b) Mene ne ya nuna cewa Sama’ila ya bi gurbi mai kyau?

17 Zai kasance da sauƙi Sama’ila ya yi tunani cewa tun da babban firist da kuma yaransa suna yin zunubi, shi ma zai yi duk abin da ya ga dama. Ɓatancin da wasu suke yi har da masu matsayi, ba hujja ba ce na yin zunubi. A yau, matasa Kiristoci da yawa sun bi misalin Sama’ila kuma sun ci gaba da yin “girma a gaban Ubangiji,” har ma sa’ad da wasu suka ƙi ƙafa musu misali mai kyau.

18 Mene ne sakamakon biyayyar da Sama’ila ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ɗan yaro fa Sama’ila ya yi ta girma, yana da tagomashi a wurin Ubangiji duk da mutane.” (1 Sam. 2:26) Mutanen da suka kafa wa Sama’ila misali mai kyau sun ƙaunace shi sosai. Jehobah ma yana son yaron domin amincinsa. Sama’ila ya san cewa Allahnsa zai kawo ƙarshen dukan ɓatanci da ake yi a Shiloh, amma wataƙila yana mamaki ko yaushe ne hakan zai faru. Wani abu ya faru wata rana daddare da ya sa ya daina mamaki.

Ka “Yi Magana, Gama Bawanka Yana Ji”

19, 20. (a) Mene ne ya faru da Sama’ila wata rana daddare a mazaunin? (b) Ta yaya Sama’ila ya san wanda yake kiransa, kuma yaya yake ɗaukan Eli?

19 Gari ya kusan wayewa, kuma wutar babban fitilar tanti tana ci. Sai Sama’ila ya ji ana kiransa. Ya yi zato cewa Eli da ya kusan makancewa ne yake kiransa. Sai ya tashi ya “sheƙa” gudu zuwa wurin Eli. Ka yi tunanin yadda yaron yake sauri ba takalma don ya je ya san abin da Eli yake bukata. Sama’ila yana daraja Eli kuma yana masa alheri. Duk da zunuban Eli, har ila shi babban firist ne na Jehobah.—1 Sam. 3:2-5.

20 Sama’ila ya tashi Eli, sai ya ce masa: ‘Ga ni: gama ka kira ni.’ Amma Eli ya ce wa yaron bai kira shi ba, ya je ya kwanta. Hakan ya faru har sau uku! Daga baya, Eli ya fahimci abin da ke faruwa. Jehobah ba ya cika saukar wa mutanensa da wahayi, kuma dalilin a bayyane yake. Amma Eli ya san cewa Jehobah ne yake kiran yaron. Eli ya ce wa Sama’ila ya je ya kwanta, kuma ya gaya masa abin da zai faɗa sa’ad da Jehobah ya sake kiransa. Sama’ila ya yi biyayya. Ba da daɗewa ba, sai ya ji kira: “Ya Sama’ila, Sama’ila. Sa’annan Sama’ila ya ce, Yi magana; gama bawanka yana ji.”—1 Sam. 3:1, 5-10.

21. Ta yaya za mu iya sauraron Jehobah a yau, kuma me ya sa ya kamata mu ci gaba da yin hakan?

21 Jehobah ya sake samun bawan da ke yi masa biyayya a Shiloh. Sama’ila ya ci gaba da yi wa Jehobah biyayya muddar ransa. Kai kuma fa? Shin kana yin hakan a koyaushe kuwa? Ko da yake Jehobah ba ya mana magana kai tsaye a yau, amma za mu iya sauraronsa ta wajen karanta Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki. Idan muna sauraron Jehobah kuma muna masa biyayya, za mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya kamar Sama’ila.

Amincin Sama’ila ne ya sa ya idar da sakon Jehobah ga Eli duk da tsoron da yake ji

22, 23. (a) Ta yaya saƙon da Sama’ila ya ji tsoron idarwa ya cika? (b) Ta yaya Sama’ila ya ci gaba da samun daraja?

22 Sama’ila ba zai taɓa manta da daren nan ba. Me ya sa? Domin a daren ne ya ƙulla dangantaka ta musamman da Jehobah kuma ya zama annabi da kuma kakakinsa. Da farko, yaron ya ji tsoron idar da saƙon Jehobah ga Eli. Wannan saƙon hukunci ne da Jehobah zai yi wa iyalin Eli, kuma hakan zai faru ba da daɗewa ba. Amma, Sama’ila ya kasance da gaba gaɗi kuma ya idar da saƙon. Eli ya karɓi saƙon. Ba da daɗewa ba, dukan annabcin Jehobah ya cika. Isra’ilawa sun kai wa Filistiyawa hari, kuma aka kashe Hophni da Finehas a ranar. Eli kuma ya mutu sa’ad da ya sami labari cewa an ƙwace sanduƙi mai tsarki na Jehobah.—1 Sam. 3:10-18; 4:1-18.

23 Duk da haka, Sama’ila ya ci gaba da samun daraja a matsayin annabi. An ambata a labarin cewa Jehobah ya ci gaba da kasancewa tare da shi, kuma ya cika dukan annabcin da ya sa Sama’ila ya yi.—Karanta 1 Sama’ila 3:19.

‘Sama’ila Ya Yi Kira ga Ubangiji’

24. Wace shawara ce Isra’ilawa suka yanke, kuma me ya sa hakan zunubi ne mai tsanani?

24 Shin Isra’ilawa sun ci gaba da bin misalin Sama’ila kuma sun kasance da aminci ga Jehobah kuwa? A’a. Daga baya, sun tsai da shawara cewa ba annabi kawai suke bukata ba. Suna son a naɗa musu sarki, kamar sauran al’ummai. Sai Jehobah ya umurci Sama’ila ya yi hakan. Amma, ya ce ya bayyana musu cewa abin da suke so su yi zunubi ne mai tsanani. Jehobah ne suka ƙi, ba mutum ba. Sai ya ce su taru a Gilgal.

Sama’ila ya yi addu’a da bangaskiya, kuma Jehobah ya sa aka yi ruwa

25, 26. Ta yaya Sama’ila ya taimaka wa mutanensa a Gilgal su fahimci cewa sun yi zunubi mai tsanani?

25 Bari mu sake yin la’akari da abin da ya faru sa’ad da Sama’ila yake yi wa Isra’ilawa magana a Gilgal. Wannan tsohon ya tuna musu yadda ya kasance da aminci ga Jehobah. Bayan haka, sai ‘Sama’ila ya yi kira ga Ubangiji.’ Ya roƙi Jehobah ya sa a yi ruwa.—1 Sam. 12:17, 18.

26 Hakan abin mamaki ne sosai. Me ya sa? Domin ba a taɓa yin ruwan sama a lokacin rani ba. Amma, mutanen ba su sami zarafin yin shakka ba. Kafin a ce kwabo, hadari ya taru, iska ya ɓarnatar da hatsi da ke gonaki. Sai aka yi tsawa mai ƙarfi, kuma aka soma ruwa. Mene ne mutanen suka yi? “Dukan jama’a kuwa suka ji tsoron Ubangiji.” Yanzu sun fahimci cewa sun yi zunubi mai tsanani.—1 Sam. 12:18, 19.

27. Mene ne Jehobah zai yi wa waɗanda suka yi koyi da bangaskiyar Sama’ila?

27 Jehobah ne ya sa waɗannan masu taurin zuciya tunani, ba Sama’ila ba. Tun daga lokacin da Sama’ila yake ƙarami har yanzu da ya tsufa, ya kasance da bangaskiya ga Allahnsa kuma Jehobah ya albarkace shi. A yau ma, Jehobah bai canja ba, zai taimaka wa dukan waɗanda suka yi koyi da bangaskiyar Sama’ila.

^ sakin layi na 5 Naziri ya ɗauki alkawari cewa ba zai sha giya ba ko kuma ya haske gashinsa. Yawanci sun ɗauki wannan alkawari na ɗan lokaci, amma wasu kamar su Samson da Sama’ila da kuma Yohanna Mai Baftisma sun yi hakan muddar ransu.

^ sakin layi na 9 Wannan wuri mai tsarki na da tsawon ƙafa 43 da rabi da kuma faɗin ƙafa 14 da rabi, kuma tanti ne mai girma da aka gina da katakai. An gina shi da kayayyakin gini masu kyau, kamar su fata da riguna masu kyau da kuma katakai masu tsada da aka shafe da azurfa da zinariya. Mazaunin yana tsakanin farfajiya da ke da tsawon ƙafa 146 da kuma faɗin ƙafa 73, kuma akwai bagadi mai girma don miƙa hadayu. Daga baya kuma, an gina wa firist ɗakuna kusa da mazaunin. Wataƙila a waɗannan ɗakunan ne Sama’ila yake kwana.

^ sakin layi na 12 An ambata misalai biyu na rashin biyayya a cikin labarin. A Dokar, an faɗi sashen hadayun da ya kamata firistoci su ci. (K. Sha 18:3) Amma waɗannan mugayen firistocin suna yin wani abu dabam a mazaunin. Tun naman yana wuta, suna aika bayinsu su ɗauki rino su caka cikin tukunyar nama, duk sashen da ya cako shi ne zai zama na firistocin. Kuma sa’ad da mutane suka kawo hadayunsu a bagadi, sai mugayen firistocin su sa bayinsu su ci zalin su. Sukan karɓi ɗanyen naman tun kafin a miƙa kitsen ga Jehobah.—Lev. 3:3-5; 1 Sam. 2:13-17.