Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Me Za Ka Yi Idan Ka Kadaita?

Me Za Ka Yi Idan Ka Kadaita?

 Kana ji kamar kana fama kai kadai ne ko ka kadaita? Idan haka ne, yanayinku daya ne da wani marubucin Zabura da ya ce: “Na zama kamar tsuntsu a saman daki, tsuntsun da yake shi kadai.” (Zabura 102:7) Shawarar da ke Littafi Mai Tsarki za ta iya taimaka maka ka magance matsalolin da ke tattare da kadaici.

 Ka kusaci Allah

 Ko da ka kadaita, za ka iya yin farin ciki idan ka san cewa kana bukatar ka kulla dangantaka mai kyau da Allah kuma ka kokarta ka yi hakan. (Matiyu 5:​3, 6, New World Translation) Ga wasu abubuwa da za su taimaka maka ka yi hakan.

Ka karanta Nassosin da za su karfafa ka

 Nassosin nan sun karfafa mutane da yawa. Maimakon ka karanta Nassosi da yawa a tāke, ka karanta su kadan-kadan, sai ka yi tunani a kansu kuma ka yi addu’a.​—Markus 1:35.

  •    Zabura 23:​1-6

  •   Zabura 34:​1-22

  •   Zabura 46:​1-11

  •   Zabura 63:​6-8

  •   Zabura 91:​1-6

  •   Matiyu 6:​25-34

  •   2 Korintiyawa 1:​3, 4

  •   Filibiyawa 4:​6, 7

  •   1 Bitrus 5:​6, 7

Ka bincika abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa

 Idan kana fama da wata matsala, sanin abin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa da kuma yadda Allah zai kawar da su zai taimake ka ka jimre.​—Ishaya 65:17.

Ka guji yawan alhini ko damuwa

 Talifofin da ke kasa za su iya taimaka maka ka magance matsalolin da ke tattare da kadaici kuma su sa ka daina yawan ‘damuwa.’​—Matiyu 6:25.

Ka nemi abokan kirki

 Zama da abokan kirki zai sa ka kasance da ra’ayi mai kyau kuma za ka yi murna. Hakan na da muhimmanci musamman idan ba zai yiwu ka kasance tare da su ba. Idan kana zama a gida kai kadai, za ka iya amfani da manhajar sadarwa da ake amfani da ita wajen kira ana ganin juna wato, videoconferencing, ko ka rika kiran abokanka ta waya kuma ka nemi sabbin abokai. Talifofi na gaba za su taimaka maka ka nemi abokan kirki kuma ka san yadda za ka zama abokin kirki.​—Karin Magana 17:17.

 Ka rika motsa jiki

 Littafi Mai Tsarki ya ce, “wasa jiki tana da amfaninta.” (1 Timoti 4:​8, Tsohuwar Hausa a Saukake) Motsa jiki zai iya taimaka maka ka yi tunani da kyau kuma ka yi farin ciki musamman idan ka kadaita. Ko da ba za ka iya fita daga gida ba, akwai wasu abubuwa da za ka iya yi don ka rika motsa jiki.