Koma ka ga abin da ke ciki

Mene Ne Mulkin Allah Zai Yi?

Mene Ne Mulkin Allah Zai Yi?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Mulkin Allah zai canja dukan gwamnatocin ’yan Adam kuma ya yi sarauta a dukan duniya. (Daniel 2:44) Muddin wannan ya faru, Mulkin Allah zai . . .

  •   Kawar da miyagu, waɗanda son kansu ke jawo wa dukanmu matsala. “Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”—Misalai 2:22.

  •   Kawo ƙarshen yaƙoƙi. “[Allah ya] sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.”—Zabura 46:9.

  •   Kawo wa duniya ni’ima da zaman lafiya. “Kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratar da su.”—Mikah 4:4.

  •   Sa duniya ta zama aljanna. “Hamada za ta yi farin ciki. Furanni za su hudo a ƙasa da ba ta da amfani.”—Ishaya 35:1, Hausa Revised version.

  •   Sa kowa ya sami aiki mai kyau da ake morewa. “Zaɓaɓuna [Allah] kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu. Ba za su yi aiki a banza ba.”—Ishaya 65:21-23.

  •   Kawar da cuta. “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24.

  •   Kawar da tsufa. “Namansa za ya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin ƙuruciyarsa ke nan.”—Ayuba 33:25.

  •   Ta da matattu. “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa [Yesu], su fito kuma.”—Yohanna 5:28, 29.