Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

A Mulkin Allah, mutane ‘za su faranta zuciyarsu cikin yalwar salama.’​—Zabura 37:11

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Shin Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka ka daina alhini?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Kuna zuba dukan alhininku [a wurin Allah], domin yana kula da ku.” (1 Bitrus 5:7) Littafi Mai Tsaki ya gaya mana cewa Allah zai iya taimaka mana mu magance yawan alhini.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Idan ka yi addu’a, za ka sami “salamar Allah” da za ta sa ka daina damuwa.​—Filibiyawa 4:​6, 7, Littafi Mai Tsarki.

  • Ƙari ga haka, karanta Kalmar Allah za ta taimaka maka ka jimre matsaloli.​—Matta 11:​28-30.

Shin za mu taɓa daina yin alhini kuwa?

Wasu sun yi imani cewa . . .wajibi ne mu yi alhini a matsayinmu na ’yan Adam, wasu kuma sun gaskata cewa mutum zai daina alhini ne bayan ya mutu. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Allah zai cire abubuwan da ke sa mu damuwa. “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?