Koma ka ga abin da ke ciki

Bidiyoyi a kan Muhimman Koyarwar Littafi Mai Tsarki

Wadannan gajerun bidiyoyin suna amsa tambayoyi masu muhimmanci kuma suna dauke da darussa daga kasidar nan Albishiri daga Allah!

Halittar Sama da Kasa Aka Yi?

Mutane da yawa ba su fahimci labarin halitta da ke Littafi Mai Tsarki ba, wasu ma sun ce tatsuniya ce kawai. Abin da Littafi Mai Tsarki ya fada daidai ne?

Allah Yana da Suna Ne?

Allah yana da lakabi da yawa, har da Madaukaki, Mahalicci, da Ubangiji. Amma Allah yana da suna wanda aka yi amfani da shi wajen sau 7,000 a Littafi Mai Tsarki.

Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki?

Tun da mutane ne suka rubuta shi, zai dace a kira shi Kalmar Allah kuwa? Maganar wane ne ke cikin Littafi Mai Tsarki?

Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne?

Idan Allah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki, ya kamata ya fi kowane irin littafi.

Me Ya Sa Allah Ya Halicci Duniya?

Duniya tana cike da kyawawan abubuwa. An sanya ta a daidai inda ya kamata, nisan da ke tsakanin duniya da rana ya dace, hakan ya sa duniya ta zauna da kyau a inda aka ajiye ta da kuma yadda za ta iya juyawa daidai yadda ya kamata. Me ya sa Allah ya dauki dogon lokaci don ya tsara duniyar nan da kyau?

Da Gaske Za A Kona Mutane a Gidan Wuta?

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “Allah kauna ne,” don haka ba zai taba ba mutane azaba a wuta don laifin da suka yi a baya ba.

Duniya Ta Canja Sosai Tun Daga 1914

Abubuwan da suke faruwa a duniya da kuma halayen mutane sun nuna cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya fada game da “kwanakin karshe,” yana faruwa tun daga 1914.

Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutuwar Yesu tana da muhimmanci sosai. Mutuwarsa tana da ma’ana kuwa?

Mene ne Mulkin Allah?

Sa’ad da Yesu ya duniya, ya koya wa mutane game da Mulkin Allah fiye da wani batu. Mutane sun dade suna addu’a cewa Mulkin ya zo.

Mulkin Allah Ya Soma Sarauta a 1914

Fiye da shekaru 2,600 da suka shige, Allah ya sa wani sarki mai iko ya yi mafarkin da ke cika a yau.

Allah Yana So Mu Yi Amfani da Siffofi a Ibada Kuwa?

Za su iya sa mu kusaci Allah da yake ba ma ganinsa?

Allah Yana Amsa Dukan Addu’o’i Kuwa?

Idan mutum ya yi addu’a don sonkai fa? Idan mutum ya wulakanta matarsa kuma ya roki Allah ya albarkace shi fa?