Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Albarkar da Ake Samu Don Bayarwa

Albarkar da Ake Samu Don Bayarwa

“KU ƘYALE motar ta tafi, amma wannan ɗan Caina ya tsaya!” Abin da Alexandra ta ji wani ya ce ke nan. A lokacin tana zaune cikin mota tana jiran motar ta kai su wata ƙasa a nahiyar Amirka ta Kudu. Sa’ad da ta fito ganin abin da ke faruwa, sai ta ji wani ɗan Caina yana faman bayyana matsalarsa ga wani jami’in kwastam da Sifanisanci, amma bai iya yaren ba sosai. Da yake Alexandra tana halartar taron Shaidun Jehobah a yaren Caina, sai ta yarda ta taimaka wajen yin fassara.

Mutumin ya ce shi ɗan ƙasar ne, amma an sace takardunsa da kuma kuɗinsa. Da farko jami’in bai yarda da labarin ba kuma ya ɗauka cewa Alexandra tana sace mutane ta sayar da su a ƙasar waje. A ƙarshe, sai ya yarda, amma ya ce dole ne mutumin ya biya tara don ba shi da takardun da suka dace. Tun da mutumin ba shi da kuɗi, sai Alexandra ta ba shi rancen dalla 20. Mutumin ya yi mata godiya sosai kuma ya ce zai biya ta fiye da dalla 20. Alexandra ta gaya masa cewa ta taimaka masa ne don ta san cewa abin da ya kamata ta yi ke nan ba don ta samu riɓa ba. Sai ta ba shi littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki kuma ta ƙarfafa shi ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah.

Muna farin ciki idan muka ji labarin yadda ‘yan’uwanmu suke taimaka wa baƙi. Babu shakka, mutane gabaki ɗaya har da waɗanda ba su da addini sukan taimaka wa wasu. Shin idan kai ne, za ka taimaka wa wannan mutumin? Wannan tambayar tana da kyau domin Yesu ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayyukan Manzanni 20:35) Ban da haka ma, masu bincike sun gano cewa bayarwa tana taimaka mana sosai. Bari mu ga wasu dalilai.

“MAI-BAYARWA DA DAƊIN RAI”

Labarai da yawa sun nuna cewa bayarwa da kuma farin ciki suna da alaƙa. Manzo Bulus ya ce “Allah na son mai bayarwa da daɗin rai.” Bulus yana magana ne da Kiristoci da suka ba da kyauta don a taimaka wa ‘yan’uwansu da suke shan wahala. (2 Korintiyawa 8:4; 9:7) Bulus ba ya nufin cewa Kiristoci suna ba da kyauta don suna farin ciki. Amma yana nufin cewa suna farin cikin domin sun ba da kyauta.

Hakika, wani bincike ya nuna cewa bayarwa “tana kyautata wani ɓangaren ƙwaƙwalwar mutum da ke sa mu murna da cuɗanya da mutane da dai sauransu.” Wani bincike ya ƙara nuna cewa “mutum zai fi farin ciki idan ya ba wani kyautar kuɗi fiye da in ya yi amfani da kuɗin da kansa.”

Shin ka taɓa jin cewa ba za ka iya taimaka wa wasu ba don irin yanayin da kake cikin? Gaskiyar ita ce, dukanmu za mu iya ɗanɗana farin cikin da ake morewa idan mutum ya yi “bayarwa da daɗin rai.” Ba lallai ba ne sai ka ba da abu mai tsada ba, amma bayarwa da zuciya ɗaya ce ta fi muhimmanci. Wata Mashaidiya ta tura wasiƙa da kuma gudummawarta ga waɗanda suka wallafa wannan mujallar kuma ta ce: “Shekaru da yawa yanzu, kuɗin da nake bayarwa a matsayin gudummawa a Majami’ar Mulki ba su da yawa. Amma abin da Jehobah ya ba ni ya ninka wanda na bayar. . . . Ina godiya sosai don wannan zarafin da kuka ba ni na ba da kyauta domin hakan yana ƙarfafa ni.”

Ba kuɗi ne kawai za ka iya bayarwa ba. Da akwai abubuwa da yawa da za ka iya ba da kyautar su.

BAYARWA TANA ƘARA LAFIYAR JIKI

Bayarwa tana amfanar ka da kuma wasu

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-jinƙai yakan yi ma ransa alheri: amma mai-baƙin hali jiki nasa yake wahalarwa.” (Misalai 11:17) Mutanen kirki suna yin amfani da lokacinsu da kuzarinsu da kuma ƙarfinsu don su kula da wasu. Wannan halin yana amfanar su sosai, kuma ɗaya daga ciki shi ne yana ƙara musu lafiyar jiki.

Bincike ya nuna cewa mutanen da suke ba da kansu don su taimaka wa wasu ba sa cika rashin lafiya ko kuma baƙin ciki. Ban da haka ma, suna kasancewa da ƙoshin lafiya. Bayarwa tana inganta lafiyar mutanen da ke fama da cututtuka masu tsanani kamar ciwon ƙwaƙwalwa da ƙashin baya da kuma cutar Sida. Binciken ya sake gano cewa idan waɗanda suke so su daina maye da giya suna taimaka wa wasu, hakan yana hana su yawan damuwa kuma yana ɗauke hankalinsu daga shan giya.

Abin da ya sa shi ne, idan mutum yana “da tausayi da kuma halin kirki, hakan zai iya hana shi yin mugun tunani.” Ƙari ga haka, bayarwa tana kāre mu daga yawan damuwa da kuma hawan jini. Bayarwa tana taimaka wa ma’aurata su daina baƙin ciki sa’ad da ɗaya daga cikinsu ya rasu.

Babu shakka, bayarwa tana ƙara maka lafiyar jiki.

MUTANE ZA SU BI MISALINKA NA BAYARWA

Yesu ya ƙarfafa mabiyansa cewa: “Ku bayar, za a ba ku, mudu mai-kyau, danƙararre, girgizajje, mai-zuba, za su bayar cikin ƙirjinku. Gama da mudun da kuke aunawa, da shi za a auna muku.” (Luka 6:38) Idan ka ba da kyauta, hakan zai sa mutane su nuna godiya kuma su yi koyi da kai ta wajen ba da kyauta. Saboda haka, bayarwa tana ƙarfafa haɗin kai da kuma abokantaka.

Bayarwa tana ƙarfafa haɗin kai da kuma abokantaka

Masu bincike a kan dangantakar mutane sun gano cewa “mutanen da suke damuwa game da lafiyar wasu suna sa wasu su bi misalinsu a yin hakan.” Ban da haka ma, “wasu mutane suna kasancewa da halin bayarwa sa’ad da suka karanta game da yadda wani ya taimaka wa wani.” Shi ya sa wani bincike ya ce, “halin mutum ɗaya yana iya shafan mutane da yawa sosai, har da waɗanda bai sani ba.” Ma’ana, mutumin da yake yawan bayarwa yana iya sa mutane a yankinsu su soma ba da kyauta. Shin ba za ka so ka zauna a irin wannan wajen ba? Hakika, za a samu albarka sosai idan mutane da yawa suna bayarwa.

Abin da ya faru a jihar Florida da ke Amirka ya nuna gaskiyar wannan al’amarin. Wasu Shaidun Jehobah sun ba da kansu don su kai kayan agaji a wani wajen da aka yi girgizar ƙasa. Yayin da suke jira a kawo kayan aiki, sai suka lura cewa katangar gidan wani mutum a unguwar ya lalace. Sai Shaidun suka je suka gyara katangar. Bayan wani lokaci, mutumin ya rubuta wasiƙa ga hedkwatar Shaidun Jehobah cewa: “Ina matuƙar godiya. Tun da nake ban taɓa ganin mutanen kirki kamar waɗannan mutanen ba.” Hakan ya motsa shi ya ba da gudummawar kuɗi, kuma ya ce wannan aikin da Shaidun suke yi, aiki ne mai ban al’ajabi.

KA BI MISALIN WANDA YA YI FICE A BAYARWA

’Yan kimiyya sun yi wani bincike kuma suka gano cewa “ ’yan Adam suna da halin son taimaka wa wasu.” Binciken ya ƙara nuna cewa, “ko yara ma suna damuwa da mutane tun kafin su soma magana.” Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya faɗi amsar sa’ad da ya ce an halicci ‘yan Adam ne “cikin kamanin Allah.” Kuma hakan ya sa muna da halaye masu kyau irin na Allah.Farawa 1:27.

Bayarwa tana ɗaya daga cikin halaye masu ban sha’awa da mahaliccinmu Jehobah Allah yake da su. Allah ya ba mu rai da kuma dukan abubuwan da muke bukata don mu kasance da farin ciki. (Ayyukan Manzanni 14:17; 17:26-28) Za mu iya kusantar Ubanmu na sama kuma mu san nufinsa ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki ya ƙara gaya mana cewa Allah ya yi shiri da zai sa mu more rayuwa mai kyau a nan gaba. * (1 Yohanna 4:9, 10) Jehobah ne tushen bayarwa, kuma ya halicce ka cikin kamaninsa. Saboda haka, bai kamata ka yi mamaki cewa misalinsa da kake bi na ba da kyauta yana ƙara maka ƙoshin lafiya kuma yana sa shi farin ciki ba.Ibraniyawa 13:16.

Shin ka tuna da Alexandra da muka ambata a farkon wannan talifin? Yaya labarin ya ƙaya? Ko da yake wasu da ke cikin motar sun ce Alexandra ta yi hasarar kuɗinta, amma sa’ad suka isa inda za su, sai mutumin da ta taimaka masa ya kira abokansa kuma ya karɓi dalla 20 a wurinsu ya ba wa Alexandra. Ƙari ga haka, mutumin ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kamar yadda Alexandra ta ƙarfafa shi ya yi. Bayan wata uku, Alexandra ta yi farin cikin sake haɗuwa da mutumin a taron yanki na Shaidun Jehobah da aka yi a ƙasar Peru a yaren Caina. Don ya ƙara nuna godiyarsa ga abin da Alexandra ta yi masa, sai mutumin ya gayyace ta da mutanen da suka zo taron da ita zuwa shagonsa na sayar da abinci.

Bayarwa da kuma taimaka wa mutane yana kawo farin ciki sosai. Taimaka wa mutane su san Jehobah Allah, wanda shi ne Tushin bayarwa ya fi sa mutane farin ciki! (Yaƙub 1:17) Shin kana moran wannan albarkar kuwa?

^ sakin layi na 21 Don ƙarin bayani, ka duba littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki? Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi kuma za ka iya samunsa a www.pr418.com/ha. Ka duba ƙarƙashin LITTATTAFAI > LITTATTAFAI da ƘASIDU..