Koma ka ga abin da ke ciki

Yaushe Ne Karshen Duniyar Nan Za Ta Zo?

Yaushe Ne Karshen Duniyar Nan Za Ta Zo?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kafin mu iya sanin lokacin da karshen wannan duniyar za ta zo, muna bukatar mu fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya yi amfani da kalmar nan “duniya.” Kalmar Helenancin nan koʹsmos da aka fassara ta zuwa “duniya” tana nufi ’yan Adam, musamman ma wadanda ba sa yin nufin Allah. (Yohanna 15:18, 19; 2 Bitrus 2:5) A wasu lokatai, koʹsmos tana nufin ayyukan da ’yan Adam suke yi.​—1 Korintiyawa 7:31; 1 Yohanna 2:15, 16. a

Mene ne ake nufi da “karshen wannan duniyar”?

 Wannan furucin “karshen wannan duniyar” da ta bayyana a fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa tana iya nufin “cikar zamani.” (Matta 24:3) Ba ta nufin cewa za a halaka duniya gabaki daya ko kuma ’yan Adam, amma tana nufin za a kawo karshen ayyuka marasa kyau da ’yan Adam suke yi.​—1 Yohanna 2:17.

 Littafi Mai Tsarki ya ce, “za a datse masu-aika mugunta” don mutanen kirki su ji dadin rayuwa a duniya. (Zabura 37:9-11) Wannan zai faru ne a lokacin “ƙunci mai-girma,” wadda za ta kai ga yakin Armageddon.—Matta 24:21, 22; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.

Yaushe ne karshen duniyar nan za ta zo?

 Yesu ya ce: “Amma zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku na sama, ko Ɗa, sai Uba kaɗai.” (Matta 24:36, 42) Yesu ya kara cewa lokacin zai zo a ‘sa’ar da ba mu yi tsammaninsa ba.’—Matta 24:44.

 Duk da cewa ba za mu iya sanin ainihin ranar ko kuma lokacin da karshen duniya za ta zo ba, amma Yesu ya ba mu ‘alama’ ko kuma abubuwan da za su faru da za su nuna cewa karshen duniya ta kusa. (Matta 24:3, 7-14) Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lokacin “kwanakin karshe.”​—Daniyel 12:4; 2 Timotawus 3:1-5.

Bayan an kawo karshen wannan duniyar, akwai wani abin da zai rage kuma?

 Kwarai kuwa. Ba za a halaka wannan duniya ba domin Littafi Mai Tsarki ya ce, “ba kuwa za a iya kawar da ita ba har abada.” (Zabura 104:5) Bayan haka, duniya za ta cika da mutane. A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya yi alkawarin cewa: “Masu-adalci za su gāji kasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Allah zai mai da duniya ta zama kamar yadda yake so tun da farko:

  •   Za ta zama aljanna.​—Ishaya 35:1; Luka 23:43.

  •   Za mu samu kwanciyar hankali da kuma ni’ima.​—Mikah 4:4.

  •   Za mu yi aiki mai kyau da kuma mai gamsarwa.​—Ishaya 65:21-23.

  •   Ba za a sake yin rashin lafiya ko kuma tsufa ba.​—Ayuba 33:25; Ishaya 33:24.

a Kari ga haka, an fassara kalmar Helenancin nan ai·onʹ zuwa “duniya” a cikin wasu Littafi Mai Tsarki. Idan aka fassara ta haka, ai·onʹ tana da ma’ana kusan irin daya da koʹsmos, wato tana nufin ayyukan da ’yan Adam suke yi.