Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Yakin Armageddon?

Mene ne Yakin Armageddon?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Yakin Armageddon yaki ne tsakanin gwamnatocin ’yan Adam da Allah. Wadannan gwamnatocin da magoya bayansu har yanzu sun ki amincewa da sarautar Allah. (Zabura 2:2) Saboda haka, yakin Armageddon zai kawo karshen sarautar ’yan Adam.​—Daniyel 2:​44.

 A littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:16 ne kawai aka ambata kalmar nan “Armageddon.” Wahayin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya nuna cewa za a tattara “dukan sarakunan duniya” domin “yaki a babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka” a “wurin da ake ce da shi Armageddon” da Ibrananci.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 16:14.

 Su wa za su yi yakin Armageddon? Yesu Kristi ne zai ja-goranci mala’iku don su yaki magabtan Allah. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:​11-16, 19-21) Wadannan magabtan su ne wadanda suke gāba da Allah kuma suna rena shi.​—Ezekiyel 39:7.

 A Gabas ta Tsakiya ce za a yi yakin Armageddon? A’a. Yakin Armageddon zai shafi dukan duniya ba a wuri daya kawai ba.​—Irmiya 25:​32-34; Ezekiyel 39:​17-20.

 A wasu lokuta akan kira Armageddon “Har–​Magedon” (Har Meghiddohnʹ a Ibrananci), wanda yake nufin “Dutsen Megiddo.” Megiddo wani birni ne a Isra’ila a zamanin dā. Tarihi ya nuna cewa an yi yake-yake sosai a Megiddo kuma an rubuta wasu labaran a Littafi Mai Tsarki. (Alkalai 5:​19, 20; 2 Sarakuna 9:27; 23:29) Amma Armageddon ba ya nufin wani wuri kusa da birnin Megiddo. Kari ga haka, babu wani babban dutse a wurin kuma Kwarin Jezreel ba zai iya daukan dukan magabtan Allah ba. Saboda haka, yakin Armageddon zai shafi dukan duniya domin dukan ’yan siyasa za su yi gāba da sarautar Allah.

 Yaya abubuwa za su kasance a lokacin yakin Armageddon? Ko da yake ba mu san yadda Allah zai yi amfani da ikonsa ba, amma zai iya yin amfani da dusar kankara ko girgizar kasa ko ambaliyar ruwa ko wuta ko walkiya ko kuma cututtuka kamar yadda ya tāba yi a dā. (Ayuba 38:​22, 23; Ezekiyel 38:​19, 22; Habakkuk 3:​10, 11; Zakariya 14:12) A lokacin wasu magabtan Allah za su rikice kuma su soma kakkashe junansu, amma daga baya za su gane cewa Allah ne yake yakan su.​—Ezekiyel 38:​21, 23; Zakariya 14:13.

 Za a hallaka duniya a yakin Armageddon ne? A’a, ba za a hallaka duniya da muke zama a ciki ba domin an halicce ta ne don ’yan Adam su zauna a cikinta har abada. (Zabura 37:29; 96:10; Mai-Wa’azi 1:4) Yakin Armageddon ba zai hallaka dukan mutane ba domin “babban taro” wato, taro mai girma za su tsira.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 14; Zabura 37:34.

 A wasu lokuta Littafi Mai Tsarki yana amfani da kalmar nan “duniya” don ya yi nuni ga mugayen mutane da ba sa bin Allah. (1 Yohanna 2:​15-17) Don haka, yakin Armageddon zai kawo “karshen zamani” ko karshen duniya, wato, karshen mugayen mutane.​—Matiyu 24:3.

 Yaushe za a yi yakin Armaggedon? Sa’ad da Yesu yake magana game da “azaba mai zafi” wato kunci mai girma da zai sa a yi yakin Armageddon, ya ce: “Ba wanda ya san ranar ko a karfe nawa ne wannan zai faru, ko mala’ikun da suke sama, ko Dan, sai dai Uban kadai.” (Matiyu 24:​21, 36) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa a lokacin bayyanuwar Yesu ne za a yi yakin Armageddon, wanda ya soma a shekara ta 1914.​—Matiyu 24:​37-39.