Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA TARA

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na Karshe”?

Muna Rayuwa ne a “Kwanaki na Karshe”?
  • Waɗanne abubuwa ne a zamaninmu aka annabta a Littafi Mai Tsarki?

  • Yaya Kalmar Allah ta ce mutane za su zama a “kwanaki na ƙarshe”?

  • Game da kwanaki na ƙarshe, waɗanne kyawawan abubuwa ne Littafi Mai Tsarki ya annabta game da zamaninmu?

1. A ina za mu iya sanin abin da ke zuwa a nan gaba?

KA TAƁA kallon labarai a telibijin kuma ka yi mamaki, ‘Shin menene duniyarmu take juyawa ta zama?’ Masifu suna faɗowa ba zato ba tsammani da babu mahalukin da zai iya faɗan abin da zai faru gobe. (Yaƙub 4:14) Amma, Jehobah ya san abin da zai faru a nan gaba. (Ishaya 46:10) Tun a dā can Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ta faɗi miyagun abubuwa da suke faruwa a zamaninmu da kuma abubuwa masu ban sha’awa da za su faru a nan gaba ba da daɗewa ba.

2, 3. Wace tambaya ce almajiran suka yi wa Yesu, kuma yaya ya amsa?

2 Yesu Kristi ya yi magana game da Mulkin Allah, wanda zai kawo ƙarshen dukan mugunta kuma ya mai da duniya ta zama aljanna. (Luka 4:43) Mutane suna so su san lokacin da Mulkin zai zo. Almajiran Yesu sun tambaye shi: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” (Matta 24:3) Yesu ya amsa musu cewa Jehobah Allah ne kaɗai ya san daidai lokacin da ƙarshe zai zo. (Matta 24:36) Amma Yesu ya faɗi abubuwa da za su faru a duniya kafin Mulkin ya kawo salama da kwanciyar hankali na ƙwarai ga ’yan adam. Abin da ya faɗa yana faruwa a yanzu!

3 Kafin mu bincika tabbacin cewa muna rayuwa a “cikar zamani,” bari mu ɗan binciki yaƙi da babu mutumin da ya gani. Yaƙin ya faru ne a duniya marar ganuwa ta ruhohi, kuma sakamakonsa ne yake shafanmu duka.

YAƘI A SAMA

4, 5. (a) Menene ya faru a sama ba da daɗewa ba bayan an naɗa Yesu Sarki? (b) In ji Ru’ya ta Yohanna 12:12, menene sakamakon yaƙin na sama?

4 Babi na baya na wannan littafin ya yi bayanin cewa Yesu Kristi ya zama Sarki a samaniya a shekara ta 1914. (Daniel 7:13, 14) Ba da daɗewa ba bayan ya sami ikon Mulki, Yesu ya ɗauki mataki. “Aka yi yaƙi cikin sama,” in ji Littafi Mai Tsarki. “Mika’ilu [wani suna na Yesu] da nasa mala’iku suna fita su yi gāba da dragon [Shaiɗan Iblis], dragon kuma ya yi gāba da nasa mala’iku.” * Aka yi nasara a kan Shaiɗan da miyagun mala’ikunsa, wato aljanu, aka jefo su duniya daga sama. ’Ya’yan Allah na ruhu masu aminci suka yi farin ciki cewa Shaiɗan da aljanunsa sun bar sama. Amma mutane ba za su sami irin wannan farin ciki ba. Maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kaiton duniya . . . domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.”—Ru’ya ta Yohanna 12:7, 9, 12.

5 Don Allah ka lura da abin da ya faru a yaƙin nan na sama. Cikin fushinsa, Shaiɗan zai haddasa kaito, ko kuma masifa, ga waɗanda suke duniya. Kamar yadda za ku gani, a yanzu muna cikin lokaci ne na wannan kaito. Amma zai kasance marar tsawo sosai—‘zarafin kaɗan ne.’ Shaiɗan kansa ya fahimci haka. Littafi Mai Tsarki yana kiran wannan lokaci “kwanaki na ƙarshe.” (2 Timothawus 3:1) Lalle ya kamata mu yi farin ciki cewa ba da daɗewa ba Allah zai kawar da rinjayar Iblis bisa duniya! Bari mu bincika abubuwa da aka faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki da suke faruwa a yanzu. Waɗannan sun tabbatar da cewa muna kwanaki na ƙarshe kuma sun nuna cewa Mulkin Allah ba da daɗewa ba zai kawo madawwamiyar albarka ga waɗanda suke ƙaunar Jehobah. Da farko, bari mu bincika ɓangarori huɗu na alamun da Yesu ya ce za su kasance a lokacin da muke rayuwa.

MUHIMMAN AUKUWA NA KWANAKI NA ƘARSHE

6, 7. Ta yaya kalmomin Yesu game da yaƙi da yunwa suke cika a yau?

6 “Al’umma za ta tasa ma al’umma, mulki kuma za ya tasa ma mulki.” (Matta 24:7) An kashe miliyoyin mutane a yaƙe-yaƙe na ƙarnin da ya shige. Wani ɗan tarihin Britaniya ya rubuta: “An zubar da jini a ƙarni na 20 fiye da kowane a dukan rubutaccen tarihi. . . . Ƙarni da aka yi ta yaƙi babu kama hannun yaro, sai dai da ’yan gajerun lokatai da babu tsararren yaƙi a wani wuri.” Rahoto daga Hukumar Sa wa Duniya Ido ya ce: “Mutane da suka mutu a yaƙi a ƙarni [na 20] sun yi ninki uku na mutanen da suka mutu a dukan yaƙe-yaƙe daga ƙarni na fari A.Z., zuwa shekara ta 1899.” Fiye da mutane miliyan 100 suka mutu saboda yaƙe-yaƙe tun daga shekara ta 1914. Idan ma mun san baƙin cikin rashin wanda muke ƙauna a yaƙi, sai dai mu riƙe baki idan aka ninka wannan baƙin cikin sau miliyoyi.

7 “Za a yi yunwa.” (Matta 24:7) Bincike ya nuna cewa noman abinci ya ƙaru sosai a cikin shekaru 30 da suke shige. Duk da haka, yunwa ta ci gaba domin mutane da yawa ba su da isashen kuɗin da za su sayi abinci ko kuma gonar da za su yi noma. A ƙasashe masu tasowa, fiye da mutane biliyan suna rayuwa ne bisa dala guda ko kuma ƙasa da haka a rana. Yawancin waɗannan suna wahala daga matsananciyar yunwa. Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya ta kimanta cewa yunwa ita ce kan gaba wajen sanadin mutuwar yara fiye da miliyan biyar kowace shekara.

8, 9. Menene ya nuna cewa annabcin Yesu game da raurawar ƙasa da annoba sun kasance gaskiya?

8 “Za a yi manyan rayerayen duniya.” (Luka 21:11) Bisa ga binciken yanki na Amirka, tun daga shekara ta 1990 ana yin matsakaicin raurawar ƙasa 17 kowace shekara da suke da ƙarfin da za su rushe gine-gine kuma su tsaga ƙasa. Kuma raurawar ƙasa da take da ƙarfin halaka gidaje gaba ɗaya tana faruwa kowace shekara. Wani bincike kuma ya nuna cewa: “Raurawar ƙasa ta kashe dubban rayuka a cikin shekara 100 da ta shige, kuma mutuwar da ci gaba a fasaha ya rage, bai taka kara ya karya ba.”

9 “Za a yi . . . annoba.” (Luka 21:11) Duk da ci gaba a kimiyyar kiwon lafiya, tsofaffin cututtuka da sababbi suna ci gaba da halaka mutane. Wani rahoto ya nuna cewa cututtuka 20—da suka haɗa da tarin fuka, zazzabin cizon sauro, kwalara—sun ƙaru a shekarun baya bayan nan, kuma wasu irin cututtuka suna da wuyar magani. Kuma aƙalla, sababbin cututtuka talatin suka ɓullo. Waɗansun su ba su da magani kuma suna kisa.

MUTANEN KWANAKI NA ƘARSHE

10. Waɗanne halaye da aka faɗa a 2 Timoti hawus 3:1-5 kake gani a mutane a yau?

10 Ban da abubuwa da za su auku a duniya, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa zamanin ƙarshe zai ga canji a zamanta kewa na mutane. Manzo Bulus ya kwatanta yadda galibin mutane za su kasance. A 2 Timothawus 3:1-5, mun karanta: “Cikin kwanaki na ƙarshe miyagun zamanu za su zo.” Bulus ya ce mutane za su zama

  • masu sonkai

  • masu son kuɗi

  • marasa bin iyayensu

  • marasa tsarki

  • marasa ƙauna

  • marasa kamewa

  • masu zafin hali

  • masu son annashuwa fiye da son Allah

  • masu riƙe da surar ibada, amma sun musunci ikonta

11. Ta yaya Zabura 92:7 ta kwatanta abin da zai faru da miyagu?

11 Haka mutane suke a unguwarku? Hakika haka suke. Da mutane a ko’ina da suke da mugayen halaye. Wannan ya nuna cewa ba da daɗewa ba Allah zai aikata, domin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Lokacin da masu-mugunta suna tsiro kamar ciyawa, sa’anda dukan masu-aikin mugunta suna yabanya: domin su hallaka ke nan har abada.”—Zabura 92:7.

AUKUWA MASU KYAU!

12, 13. Ta yaya “ilimi” ya ƙaru a “kwanakin ƙarshe”?

12 Hakika zamanin ƙarshe yana cike da kaito, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa. A cikin wannan duniya da take cike da wahala, da akwai abubuwa masu kyau da suka auku a tsakanin masu bauta wa Jehobah.

13 “Ilimi kuma za ya ƙaru,” an annabta wannan a littafin Daniel. A yaushe wannan zai faru? A “kwanakin ƙarshe.” (Daniel 12:4) Musamman tun shekara ta 1914, Jehobah ya taimaki waɗanda da gaske suke da muradin su bauta masa suka ƙara ilimin Littafi Mai Tsarki. Suka fahimci gaskiya mai tamani game da sunan Allah da kuma nufinsa, da kuma hadayar fansa ta Yesu Kristi, yanayin matattu, da kuma tashin matattu. Bugu da ƙari, bayin Jehobah sun koyi yadda za su rayu a hanyar da za ta amfane su kuma ta ɗaukaka Allah. Sun kuma fahimci matsayin Mulkin Allah da kuma yadda zai daidaita abubuwa a duniya. Menene suka yi da wannan ilimin? Wannan tambayar ta kawo mu ga wani annabci kuma da yake cika a wannan zamanin ƙarshe.

“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.”​—Matta 24:14

14. A ina ake yin wa’azin bisharar Mulki a yau, kuma su waye suke yin wa’azin?

14 “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya,” in ji Yesu Kristi a annabcinsa na “cikar zamani.” (Matta 24:3, 14) Miliyoyin Shaidun Jehobah suna wa’azi na bisharar Mulki da ƙwazo a dukan duniya a fiye da ƙasashe 230 kuma a cikin fiye da harsuna 400, suna sanar da Mulkin, abin da Mulkin zai yi, da kuma yadda za mu sami albarkarsa. Sun fito daga “Dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) Shaidun suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki a gida da miliyoyin mutane waɗanda suke so su san abin da Littafi Mai Tsarki ainihi yake koyarwa. Wannan cikar annabci ce mai ban sha’awa, musamman ma tun da Yesu ya annabta cewa Kiristoci na gaskiya za su “zama abin ƙi”!—Luka 21:17.

MENENE ZA KA YI?

15. (a) Ka gaskata cewa muna rayuwa a zamanin ƙarshe, me ya sa? (b) Mecece “matuƙa” take nufi ga waɗanda suka yi hamayya da Jehobah ga kuma waɗanda suka miƙa kai ga sarautar Mulkinsa?

15 Tun da annabce-annabce da yawa na Littafi Mai Tsarki suna cika a yau, ba ka yarda ba cewa muna zamani na ƙarshe? Bayan an yi wa’azin bisharar yadda ya gamsar da Jehobah, “matuƙa” babu shakka za ta zo. (Matta 24:14) “Matuƙa” tana nufin lokaci da Allah zai halaka miyagu daga duniya. Zai halaka dukan waɗanda suka yi hamayya da Shi da son rai, Jehobah zai yi amfani da Yesu da mala’iku. (2 Tassalunikawa 1:6-9) Shaiɗan da aljannunsa ba za su sake yaudarar al’ummai ba. Bayan haka, Mulkin Allah zai zubo albarka ga dukan waɗanda suka miƙa kai ga sarautarsa ta adalci.—Ru’ya ta Yohanna 20:1-3; 21:3-5.

16. Menene zai kasance hikima a gare ka ka yi?

16 Tun da ƙarshen zamanin Shaiɗan ya yi kusa, muna bukatar mu tambayi kanmu, ‘Menene ya kamata na ci gaba da yi?’ Hikima ce mu ci gaba da koyo game da Jehobah da kuma abin da yake bukata a gare mu. (Yohanna 17:3) Ka kasance ɗalibin Littafi Mai Tsarki mai ƙwazo. Ka sa yin hulɗa a kai a kai da waɗanda suke yin nufin Jehobah ya zama maka jiki. (Ibraniyawa 10:24, 25) Ka nemi ilimi da Jehobah Allah ya bayar ga mutane a dukan duniya, kuma ka yi gyare-gyare da suka wajaba a rayuwarka saboda ka more tagomashin Allah.—Yaƙub 4:8.

17. Me ya sa halakar miyagu za ta faɗo wa yawancin mutane ba zato?

17 Yesu ya annabta cewa yawancin mutane za su yi watsi da tabbacin cewa muna rayuwa a zamanin ƙarshe. Halakar miyagu za ta zo ba zato ba tsammani. Kamar ɓarawo cikin dare, za ta faɗa wa mutane ba zato. (1 Tassalunikawa 5:2) Yesu ya yi gargaɗi: “Kamar yadda kwanakin Nuhu su ke, hakanan kuma bayanuwar Ɗan Mutum za ta zama. Gama kamar yadda suna ci, suna sha, suna aure, suna aurarwa a cikin kwanakin da ke gaban ruwan Rigyawa, har randa Nuhu ya shiga cikin jirgi, ba su sani ba har rigyawa ta zo ta kwashe su dukan; hakanan kuma bayanuwar Ɗan mutum za ta zama.”—Matta 24:37-39.

18. Wane gargaɗi na Yesu ya kamata mu ɗauka da muhimmanci?

18 Saboda haka, Yesu ya gaya wa waɗanda suke sauraronsa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko: gama hakanan za ta humi dukan mazaunan fuskar duniya duk. Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya [da yardar Allah] kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luka 21:34-36) Hikima ce a ɗauki maganar Yesu da muhimmanci. Me ya sa? Domin waɗanda suka sami yardar Jehobah Allah da kuma “ɗan mutum,” Yesu Kristi, suna da begen tsira daga ƙarshen zamanin Shaiɗan kuma su rayu har abada a cikin sabuwar duniya mai ban sha’awa da ta yi kusa sosai!—Yohanna 3:16; 2 Bitrus 3:13.

^ sakin layi na 4 Domin ƙarin bayani da ya nuna cewa Mika’ilu wani sunan Yesu Kristi ne, dubi Rataye, shafi na 218-219.