Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Kunci Mai Girma?

Mene ne Kunci Mai Girma?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kunci mai girma zai kawo wahala sosai da ’yan Adam ba su taba fuskanta ba. Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa zai faru a “kwanaki na karshe.” (2 Timotawus 3:1; Daniyel 12:4) Zai zama kunci “irin da ba a taba yin kamarsa ba tun farkon halitta wadda Allah ya halitta har yanzu, ba kuwa za a yi ba dadai.”—2 Timotawus 3:1; Daniyel 12:4; Markus 13:19; Daniyel 12:1; Matta 24:21, 22.

Abubuwan da za su faru a lokacin kunci mai girma

  •   Za a halaka addinin karya. Za a halaka addinin karya nan da nan. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 5; 18:9, 10, 21) Allah zai sa rukunin siyasa ya yi nufinsa sa’ad da suka dauki wannan matakin halaka addinin karya.—Ru’ya ta Yohanna 17:3, 15-18. a

  •   Za a kai wa mutanen da ke bin addinin gaskiya hari. Al’ummai da suka hada kai da aka kira “Gog na kasar Magog” za su yi kokari su halaka wadanda suke bin addini na gaskiya. Amma, Allah zai kāre masu bauta masa don kada a halaka su.—Ezekiyel 38:1, 2, 9-12, 18-23.

  •   Za a yi wa mazaunan duniya shari’a. Yesu zai yi wa dukan ’yan Adam shari’a kuma zai “rarraba su da juna, kamar yadda makiyayi yakan rarraba tumaki da awaki.” (Matta 25:31-33) Yesu zai yi wannan shari’a bisa yadda kowannenmu ya tallafa wa ‘’yan’uwansa,’ wato wadanda za su yi sarauta tare da shi a sama.—Matta 25:34-46.

  •   Za a tattara wadanda za su yi sarauta. Masu aminci da aka zaba su yi sarauta da Kristi za su gama rayuwarsu a duniya kuma a ta da su don su soma rayuwa a sama.—Matta 24:31; 1 Korintiyawa 15:50-53; 1 Tasalonikawa 4:15-17.

  •   Armageddon. Wani sunan da ake kiran wannan “babbar rana ta Allah Mai-iko duka” ita ce “ranar Ubangiji.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; Ishaya 13:9; 2 Bitrus 3:12) Kristi zai halaka dukan wadanda ya same su da laifi. (Zafaniya 1:18; 2 Tasalonikawa 1:6-10) Hakan ya kunshi kungiyoyin siyasa na fadin duniya da ke wakiltar dabba mai kawuna bakwai a cikin Littafi Mai Tsarki.​—Ru’ya ta Yohanna 19:19-21.

Abubuwan da za su faru bayan kunci mai girma

  •   Za a daure Shaidan da aljanu. Wani babban mala’ika zai jefa Shaidan da aljanu “cikin rami marar-matuka,” wato wurin da ba za su iya yin kome ba. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3) Za a iya kwatanta yanayin Shaidan a cikin wannan ramin da zama a cikin fursuna don ba zai iya yaudarar mutane a wurin ba.​—Ru’ya ta Yohanna 20:7.

  •   Yesu zai soma sarauta na shekara dubu. Mulkin Allah zai soma sarauta na shekara dubu, kuma hakan zai sa ’yan Adam su sami albarka sosai. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 20:4, 6) Kari ga haka, “taro mai-girma” za su “fito daga cikin babban tsananin,” kuma su tsira su ga somawar sarauta na shekaru dubu a duniya.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14; Zabura 37:9-11.

a Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ce addinin karya yana wakiltar Babila Babba, wato “babbar karuwa.” (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 5) Dabbar ja wur, wadda za ta halaka Babila tana wakiltar kungiyar da take da’awar sa dukan al’umman duniya su kasance da hadin kai. Da farko ana kiranta Tsohuwar Majalisar Dinkin Duniya amma yanzu Majalisar Dinkin duniya ce.