Koma ka ga abin da ke ciki

Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?

Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?

 Shaidun Jehobah suna tattaunawa ne da mutane don taimaka musu su fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Idan ka zabi ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki tare da mu, binciken zai taimaka maka:

  •   Ka yi rayuwa mai gamsarwa

  •   Ka zama aminin Allah

  •   Ka san alkawuran da Allah ya yi mana

A wannan shafin, za a amsa tambayoyin nan:

 Yaya ake gudanar da nazarin?

 Za ka sami wanda zai taimaka maka ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da batutuwa dabam-dabam, daya bayan daya. (Idan mace ce, za a hada ta da mace.) Littafin nan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! ne za ku yi amfani da shi. Littafin yana da tambayoyi da nassosi. Yayin da kuke tattauna nassosin, a hankali za ka fahimci ainihin sakon da ke Littafi Mai Tsarki da kuma yadda zai amfane ka. Don karin bayani, ka kalli bidiyon nan.

 Sai na biya kudi kafin a yi nazarin da ni?

 Aꞌa. Umurnin da Yesu ya ba wa mabiyansa ne muke bi. Ya ce: “Kun samu a kyauta, ku kuma bayar kyauta.” (Matiyu 10:8) Kuma ba a biya kafin a ba mutum kayan binciken, wato Littafi Mai Tsarki da littafin nan Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!

 In mutum ya fara, yaushe zai gama?

 Darussa 60 ne suke cikin littafin. Yawan lokacin da za ka yi kana nazarin darussan nan ya dangana ne da yawan lokacin da za ka bayar don yin nazarin. Dalibai da yawa sun fi so su gama darasi daya ko fiye da haka a mako.

 Me zan yi don a fara nazarin da ni?

  1.  1. Ka cika wannan fom da ke dandalinmu. Iyakacin abin da za mu yi da bayananka shi ne mu sa wani Mashaidin Jehobah ya ziyarce ka ko ya tuntube ka kamar yadda ka ce.

  2.  2. Wanda zai yi nazarin da kai zai tuntube ka. Zai yi maka bayani a kan abubuwan da za ku tattauna. Kuma zai amsa duk wata tambayar da kake da ita.

  3.  3. Kai da wanda zai yi nazarin da kai ne za ku shirya yadda za ku yi shi. Zai iya zuwa inda kake don ku dinga yin nazarin. Ko ya kira wayarka ko ku yi nazarin ta sakonnin waya ko wasika ko imel. Idan aka zauna yin nazarin, yakan ci wajen awa daya. Amma bisa lokacin da kake da shi, zai iya kasa awa daya ko ya fi awa daya.

 Zan iya gwada in ga yadda ake yinsa kafin in amince?

 Kwarai kuwa. Idan kana so ka gwada ka gani, ka cika wannan fom da ke dandalinmu. Idan wanda zai yi nazarin da kai ya tuntube ka (ko ta tuntube ki idan ke mace ce), ka gaya masa kana so ka gwada ne ka ga ko za ka so nazarin ko aꞌa. Zai yi amfani da karamin littafin Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada! don ya fara nazarin da kai. Wannan littafin ko kuma kasida yana dauke da darussa uku da suke farko-farkon babban littafin.

 Idan na soma nazarin nan, za a sa ni lallai in zama Mashaidin Jehobah?

 Aꞌa. Muna son taimaka wa mutane su san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, amma ba ma tirsasa mutane ko mu sa su dole su zama Shaidun Jehobah. A maimakon haka, abin da muke yi shi ne mu nuna wa mutum abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. Muna girmama mutane. Mun san cewa kowa ne zai zabi abin da zai yi imani da shi.​—1 Bitrus 3:15.

 Zan iya amfani da nawa Littafi Mai Tsarki?

 Kwarai kuwa, za ka iya amfani da juyin Littafi Mai Tsarki da ka fi so. Akwai fassarar New World Translation of the Holy Scriptures a yaruka da yawa. Muna son amfani da shi don yana da saukin fahimta kuma ya yi daidai da ainihin rubutun Littafi Mai Tsarki na dā. Amma kuma mun san cewa mutane da yawa sun fi son juyin Littafi Mai Tsarki da suka saba da shi.

 Zan iya ce ma wasu su zo mu yi nazarin tare?

 E, za ka iya kiran abokanka ko ka ce ma duka iyalinka su zo ku yi nazarin tare.

 Idan na taba nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a dā, zan iya koma yi kuma?

 Kwarai kuwa. Kila ma ka ji dadin yadda ake nazarin yanzu fiye da wanda ka yi a dā, domin an inganta tsarin sosai yadda zai taimaka wa mutane a yau. Yawancin nazarin yanzu tattaunawa ne kuma ana amfani da bidiyoyi da hotuna sosai.

 Kuna ba wa mutum dama ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kansa ba tare da waninku ba?

 E. Ko da yake yawancin dalibai sun fi son su sami wanda zai rika taimaka musu, wasu sun fi so su fara nazarin su kadai. Shafinmu na Kayan Nazarin Littafi Mai Tsarki yana dauke da abubuwa da dama da za su taimaka maka idan kana son ka yi nazarin kai kadai. Ga wasu kayan binciken da za su taimaka maka:

  •   Bidiyoyi a kan Littafi Mai Tsarki. Wadannan bidiyoyin sun yi bayani a kan wasu muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki.

  •   Amsoshin tambayoyin Littafi Mai Tsarki. A nan za ka sami amsar tambayoyi da yawa da ake yi game da Littafi Mai Tsarki.

  •   Nazarin Littafi Mai Tsarki a Intane (Online Bible Study Lessons). A wannan nazarin, akwai tambayoyi da amsoshi da za su taimaka wa mutum ya yi tunani kuma ya fahimci wasu batutuwa masu muhimmanci sosai, kamar: Wane ne Allah Madaukaki? Me ya jawo mugunta da shan wahala? Wata rana Allah zai sa a daina shan wahala kuwa? Ba mu da wannan sashen da Hausa amma akwai shi a yaruka da yawa. Har da Turanci da Larabci da dai sauransu.