Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki

Zai yiwu a kasance a duniya babu talauci?

Ta yaya Allah zai cire talauci a duniya?—Matta 6:9, 10.

Miliyoyin mutane suna mutuwa kowace shekara sanadiyyar rashin isasshen abinci da cuta, kuma ainihin abin da ke jawo hakan shi ne talauci. Ko da yake wasu ƙasashe suna da wadata, yawancin mutane suna cikin matsananciyar talauci. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa mutane sun daɗe suna fama da talauci.—Karanta Yohanna 12:8.

Gwamnatin da zai yi sarauta bisa dukan duniya ne zai iya kawar da talauci. Wannan gwamnatin zai kasance da ikon biyan bukatun ’yan Adam kuma ya cire yaƙe-yaƙe domin ainihin abin da ke jawo talauci ke nan. Allah ya yi alkawari cewa zai kafa gwamnatin da zai yi hakan.—Karanta Daniyel 2:44.

Wa zai iya kawo ƙarshen talauci?

Allah ya naɗa Ɗansa Yesu don ya yi sarauta bisa ’yan Adam. (Zabura 2:4-8) Yesu zai ceci matalauta kuma zai kawo ƙarshen mugunta.—Karanta Zabura 72:8, 12-14.

Kamar yadda aka annabta, “Sarkin Salama,” wato Yesu zai sa a sami salama da kwanciyar hankali a duniya baki ɗaya. A lokacin, kowa zai sami gidan kansa da aiki mai kyau da kuma abinci a yalwace.—Karanta Ishaya 9:6, 7; 65:21-23.