Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YIN ADDU’A ƁATA LOKACI NE?

Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Rika Addu’a?

Me Ya Sa Allah Ya Ce Mu Rika Addu’a?

Allah yana so mu zama aminansa.

Aminai suna tattaunawa da juna don dangantakarsu ta yi danƙo. Hakazalika, Allah yana so mu riƙa tattauna da shi don dangantakarmu da shi ta yi ƙarfi. Ya ce: “Za ku kira gareni, ku tafi ku yi mani addu’a, ni ma in ji ku.” (Irmiya 29:12) Idan kana tattaunawa da Allah, za ka ‘kusace [shi], shi ma zai kusace ka.’ (Yaƙub 4:8, Littafi Mai Tsarki) Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi.’ (Zabura 145:18) Idan mun ci gaba da yin addu’a ga Allah, babu shakka, dangantakarmu da shi za ta yi ƙarfi.

“Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda suke kira bisa gareshi.”—Zabura 145:18

Allah yana so ya taimake ka.

Yesu ya ce: “To, wane ne a cikinku ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse? Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji? To, [idan kun] . . . san yadda za ku ba ’ya’yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?” (Matta 7:9-11, LMT) Hakika, Allah yana so ka riƙa addu’a domin “yana kula da” kai kuma yana so ya taimake ka. (1 Bitrus 5:7) Ya ma ce ka gaya masa dukan matsalolinka. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Kada ka yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ka bar roƙe-roƙenka su sanu ga Allah.’—Filibiyawa 4:6.

’Yan Adam suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.

Masana a kan yanayin ’yan Adam sun lura cewa miliyoyin mutane suna jin cewa ya dace su riƙa yin addu’a. Har wasu mutanen da ba su gaskata da wanzuwar Allah ba da kuma masu shakkar wanzuwarsa sun yarda da hakan. * Wannan ya nuna cewa an halicci ’yan Adam da sha’awar ƙulla dangantaka da Allah. Yesu ya ce: “Masu farin ciki ne waɗanda suka san cewa suna bukatar ƙulla dangantaka da Allah.” (Matta 5:3, New World Translation) Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce ta wurin tattaunawa da Allah a kai a kai.

Ta yaya za mu amfana idan muka amince da gayyatar da Allah yake mana cewa mu riƙa yin addu’a?

^ sakin layi na 8 Wani bincike da aka yi a shekara ta 2012 ya ce kashi 11 cikin 100 na mutanen da ba su gaskata da wanzuwar Allah ba da kuma waɗanda suke shakkar wanzuwarsa a ƙasar Amirka suna addu’a aƙalla sau ɗaya a wata.