Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Kasar Rasha

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai a Kasar Rasha

A SHEKARA ta 1991, Shaidun Jehobah a Rasha sun yi farin ciki sosai da aka ɗaga takunkumi da aka yi game da aikinsu da daɗewa kuma sun sami izinin gudanar da ayyukansu. A wannan lokacin, mutane da yawa ba su yi zaton cewa adadin Shaidu zai ƙaru daga wajen 17,000 zuwa wajen 170,000 a yau ba! Waɗannan masu shelar Mulki da ƙwazo sun ƙunshi wasu Shaidu da suka ƙaura zuwa Rasha don su yi wa’azi. (Mat. 9:37, 38) Bari mu ji daga bakin wasu a cikinsu.

’YAN’UWA MAZA SUN ƘARFAFA IKILISIYOYI

Matthew daga Biritaniya ɗan shekara 28 ne a shekarar da aka ɗaga takunkumin. A wannan shekarar, an ba da wani jawabi a wani babban taro da ya nuna cewa ana bukatar taimako a ikilisiyoyi da ke ƙasashen Gabashin Turai. Mai ba da jawabin ya ba da misalin wata ikilisiya da ke birnin St. Petersburg a Rasha da babu dattijo sai bawa mai hidima ɗaya kawai. Duk da haka, masu shela suna nazarin Littafi Mai Tsarki da ɗarurruwan mutane! Matthew ya ce: “Bayan wannan jawabin, na ci gaba da tunani game da Rasha, sai na yi addu’a ga Jehobah musamman game da burina na ƙaura zuwa wajen.” Sai ya yi ajiyar kuɗi, ya sayar da yawancin kayayyakinsa kuma ya ƙaura zuwa Rasha a shekara ta 1992. Mene ne sakamakon wannan matakin da ya ɗauka?

Matthew

Matthew ya ce: “Yaren yana da wuya, ba na iya wa’azi da kyau a yaren. . . . Wani ƙalubale da na fuskanta kuma shi ne samun gida. Na sha ƙaura daga wani gida zuwa wani, kuma na yi hakan cikin ƙarancin lokaci.” Duk da waɗannan matsalolin, Matthew ya ce: “Ƙaura zuwa Rasha shi ne shawara mafi kyau da na taɓa tsai da.” Ya bayyana cewa: “Hidimar da nake yi a nan ta sa na dogara ga Jehobah kuma na amfana daga ja-gorarsa a hanyoyi da yawa.” Daga baya, an naɗa Matthew dattijo da majagaba na musamman kuma yanzu yana hidima a ofishin Shaidun Jehobah da ke kusa da birnin St. Petersburg.

A shekara ta 1999, Hiroo ɗan shekara 25 ya sauke karatu daga Makarantar Koyar da Masu Hidima a ƙasar Japan, kuma wani malaminsa ya ƙarfafa shi ya je hidima a wata ƙasa. Hiroo ya ji cewa ana bukatar masu shela sosai a Rasha kuma ya soma koyon yaren Rasha. Ya kuma ɗauki wani mataki mai kyau. Ya ce: “Na je na yi watanni shida a Rasha. . . . Da yake ana sanyi sosai a ƙasar, na je a watan Nuwamba don na ga ko zan iya jimrewa da sanyin.” Bayan ya ga zai iya zama a ƙasar a lokacin sanyi, sai ya koma Japan kuma ya sauƙaƙa rayuwarsa saboda ya sami isashen kuɗin tafiya Rasha don ya yi hidima.

Hiroo da Svetlana

Hiroo ya yi shekaru 12 yanzu a Rasha kuma ya yi hidima a ikilisiyoyi da dama. Akwai wani lokacin da shi kaɗai ne dattijo da ke kula da masu shela fiye da ɗari. A wata ikilisiya, a kowane mako, shi ne yake gudanar da yawancin ayyuka a Taron Hidima, da kuma gudanar da Makarantar Hidima ta Allah da Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ƙari ga haka, yana gudanar da Taron Rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya guda biyar a lokacin. Ƙari ga haka, ya yi ziyarar ’yan’uwa da yawa don ya ƙarfafa su. Da yake magana game da waɗannan shekaru, Hiroo ya ce: “Na yi farin ciki matuƙa don na taimaka wa ’yan’uwa su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah.” Ta yaya yin hidima a wurin da ake bukatar masu shela sosai ya shafe shi? Ya ce: “Kafin na je Rasha, ina hidima a matsayina na dattijo da kuma majagaba, amma ji nake kamar na ƙulla wata sabuwar abota da Jehobah bayan na zo nan. Yanzu ina dogara ga Jehobah sosai a dukan fannonin rayuwata.” A shekara ta 2005, Hiroo ya auri Svetlana, kuma sun ci gaba da yin hidimar majagaba tare.

Michael da Olga da Marina da Matthew

Matthew mai shekara 34 da ƙanensa Michael, ɗan shekara 28 ’yan Kanada ne da suka kai ziyara ƙasar Rasha. Sun yi mamaki cewa mutane da yawa ne suke halartan taro, amma ’yan’uwa maza kaɗan ne kawai suke gudanar da taron. Matthew ya ce: “Mutane 200 ne suka halarci taro a ikilisiya da na kai ziyara, kuma dattijo guda da ya ɗan tsufa da kuma wani matashi bawa mai hidima ne suka gudanar da dukan taron. Ganin wannan yanayin ne ya sa na kasance da burin ƙaura zuwa wurin don na taimaka wa ’yan’uwa da suke wajen.” Ya ƙaura zuwa Rasha a shekara ta 2002.

Bayan shekara huɗu, Michael ya ƙaura zuwa Rasha kuma ya ga cewa har ila ana bukatar taimakon ’yan’uwa maza sosai. A matsayinsa na bawa mai hidima, an ce ya kula da lissafin kuɗi da littattafai da kuma yanki. Kuma an gaya masa ya yi wasu ayyuka da sakatare na ikilisiya yake yi da kuma ba da jawabi ga jama’a. Ƙari ga haka, an ce ya taimaka wajen tsara manyan taro da kuma gina Majami’un Mulki. Ko a yanzu, ikilisiyoyi a ƙasar suna bukatar taimako sosai. Ko da yake kula da waɗannan ayyuka ba shi da sauƙi, Michael wanda dattijo ne yanzu ya ce: “Taimaka wa ’yan’uwa ya sa ni farin ciki sosai. Ita ce hanya mafi kyau na tafiyar da rayuwata!”

Matthew ya auri Marina kuma Michael ya auri Olga. Waɗannan ma’aurata tare da wasu ’yan’uwa da yawa da suka ba da kansu sun ci gaba da taimakawa kuma ikilisiyoyin suna ƙaruwa.

’YAN’UWA MATA MASU ƘWAZO SUNA TAIMAKAWA

Tatyana

A shekara ta 1994, sa’ad da Tatyana take ’yar shekara 16, majagaba na musamman guda shida daga Jamhuriyar Czech da Polan da Sulobakiya sun soma hidima a ikilisiyarsu a Yukiren. Ta tuna da su, tana farin ciki, kuma ta ce: “Waɗannan majagaba suna da ƙwazo da sauƙin kai, su masu kirki ne, kuma sun san Littafi Mai Tsarki sosai.” Ta ga yadda Jehobah ya albarkace su, sai ta yi tunani cewa ‘Ina son in zama kamar su.’

Misalin da waɗannan majagaba suka ƙafa ya sa Tatyana ta yi amfani da lokacin hutunta don ta je wa’azi tare da wasu a yankuna masu nisa da ke ƙasashen Yukiren da Belarus, inda Shaidun Jehobah ba su taɓa zuwa yin wa’azi ba. Ta ji daɗin waɗannan tafiye-tafiye da ta yi don wa’azi, kuma hakan ya sa ta yi shirye-shirye don ta ƙara ƙwazo a hidimarta. Saboda haka, ta yi shirin ƙaura zuwa Rasha. Da farko, ta ziyarci wata ’yar’uwa da ta je ƙasar hidima. Ƙari ga haka, ta nemi aikin da zai taimaka mata a hidimarta na majagaba. Daga baya, ta ƙaura zuwa Rasha a shekara ta 2000. Shin yin hakan yana da sauƙi ne?

Tatyana ta ce: “Tun da yake ba ni da kuɗin hayar gidan kaina, na yi hayar ɗaki a gidan wasu. Hakan ba shi da sauƙi. Akwai lokatan da na yi niyyar komawa gida. Amma Jehobah ya taimaka mini in ga cewa zan amfana idan na ci gaba da hidimata.” A yanzu Tatyana ta zama mai wa’azi a ƙasar waje a Rasha. Ta ce: “Shekarun da na yi ina hidima a ƙasashen waje sun ba ni damar shaida abubuwa masu amfani kuma na yi abokai da yawa. Mafi muhimmanci, hakan ya ƙarfafa bangaskiyata sosai.”

Masako

Masako ’yar Japan ce da take da shekara 50 da wani abu, kuma ta daɗe tana burin yin hidima a wata ƙasa, amma rashin lafiya ya hana ta. Duk da haka, sa’ad da ta sami ɗan sauƙi, sai ta tsai da shawara ta ƙaura zuwa Rasha don ta yi wa’azi. Ko da yake ya yi mata wuya ta sami gida da aiki mai kyau, ta yi ƙoƙari ta kula da kanta a hidimar majagaba ta wajen koyar da yaren Japan da kuma yin aikin shara. Mene ne ya taimaka mata ta ci gaba da hidimarta?

Da take magana game da hidimar fiye da shekara 14 da ta yi a Rasha, Masako ta ce: “Farin ciki da nake yi a hidimata ya wuce matsaloli da nake fuskanta. Yin wa’azi a wuraren da ake bukatar masu wa’azin bisharar Mulki sosai yana sa mutum ya kasance da ƙwazo kuma ya yi farin ciki a rayuwa.” Ta daɗa cewa: “Yadda Jehobah ya yi mini tanadin abinci da tufafi da gida a cikin waɗannan shekaru ya zama mu’ujiza a gare ni.” Ban da yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai a Rasha, Masako ta yi wa’azi a ƙasar Kirgizistan. Ƙari ga haka, ta taimaka wa rukunin harsunan Turanci da Caina da kuma Uighur. A yanzu, tana hidimar majagaba a birnin St. Petersburg.

IYALAI SUN TAIMAKA KUMA SUN SAMI ALBARKA

Inga da Mikhail

Saboda taɓarɓarewar tattalin arziki, iyalai sukan ƙaura zuwa wasu ƙasashe don su kyautata yanayinsu kuma su biya bukatunsu. Amma kamar Ibrahim da Saratu, wasu iyalai sun ƙaura zuwa wata ƙasa don su cim ma maƙasudai a bautar Jehobah. (Far. 12:1-9) Alal misali, Mikhail da Inga, wasu ma’aurata ’yan ƙasar Yukiren, sun ƙaura zuwa Rasha a shekara ta 2003. Ba da daɗewa ba suka sami mutane da suke neman su san gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

Mikhail ya ce: “Akwai lokacin da muka yi wa’azi a wurin da Shaidu ba su taɓa yin wa’azi ba. Sai wani tsoho ya buɗe ƙofa kuma ya ce, ‘Ku masu wa’azi ne?’ Sa’ad da muka ce e, sai ya ce: ‘Na san za ku zo wata rana. Wajibi ne kalmomin Yesu su cika.’ Sai mutumin ya faɗi abin da aka rubuta a Matta 24:14.” Mikhail ya daɗa cewa: “A wannan yankin, mun ga rukunin mata goma da suke zuwa cocin Baptist. Waɗannan matan masu kirki suna so su san gaskiya game da Jehobah. Suna da littafin nan Kana Iya Rayuwa Har Abada Cikin Aljanna a Duniya kuma kowane ƙarshen mako suna nazarin Littafi Mai Tsarki da wannan littafin. Mun yi sa’o’i da yawa muna amsa tambayoyinsu kuma muka rera waƙoƙin Mulki tare da su, sa’an nan muka ci abincin dare tare. Ba zan taɓa mantawa da wannan ziyarar ba.” Mikhail da Inga sun ce yin hidima a wurin da ake bukatar masu wa’azin bisharar Mulki sosai ya sa sun kusaci Jehobah kuma hakan ya sa sun daɗa ƙaunar mutane. Ƙari ga haka, rayuwarsu ta kasance da ma’ana. A yanzu, suna hidimar masu kula da da’ira.

Oksana da Aleksey da Yury

A shekara ta 2007, Yury da Oksana, wasu ma’aurata daga Yukiren sun ziyarci ofishin Shaidun Jehobah a ƙasar Rasha. Yanzu shekarunsu wajen 34 zuwa 36 ne, kuma ɗansu Aleksey yana da shekara 13. A wurin, sun ga taswira na ƙasar Rasha da ta nuna cewa ƙasar tana da yankuna da ba a tura mutane ko ikilisiya wa’azi ba. Oksana ta ce: “Bayan mun ga wannan taswira, mun fahimci cewa ƙasar na bukatar masu wa’azin bisharar Mulki sosai. Hakan ya taimaka mana mu tsai da shawarar ƙaura zuwa Rasha.” Mene ne ya daɗa taimaka musu? Yury ya ce: “Karanta talifofi da ke cikin littattafanmu kamar su ‘Can You Serve in a Foreign Field?’ (Za Ka Iya Yin Hidima a Wata Ƙasa?) ya taimaka mana sosai. * Mun ziyarci yankin Rasha da ofishin Shaidun Jehobah suka nuna mana kuma mun nemi gida da kuma aiki.” Sun ƙaura zuwa Rasha a shekara ta 2008.

Da farko, samun aiki ya yi musu wuya, kuma sun ƙaura sau da yawa daga wani gida zuwa wani. Yury ya ce: “Mun sha yin addu’a don kada mu yi sanyin gwiwa, muka ci gaba da yin wa’azi, kuma mun dogara ga Jehobah ya taimaka mana. Mun shaida yadda Jehobah yake kula da mu sa’ad da muka saka al’amuran Mulkinsa kan gaba. Wannan hidimar ta ƙarfafa iyalinmu.” (Mat. 6:22, 33) Ta yaya yin hidima inda ake bukatar masu shela ya shafi Aleksey? Oksana ta ce: “Hakan ya taimaka masa sosai. Ya keɓe kansa ga Jehobah kuma ya yi baftisma sa’ad da yake ɗan shekara tara. Da yake ya ga cewa ana bukatar masu wa’azin bisharar Mulki sosai, hakan ya motsa shi ya riƙa yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a duk lokacin da suka sami hutun makaranta. Muna farin ciki sosai yayin da muke ganin yadda yake son yin wa’azi da kuma ƙwazonsa.” A yanzu, Yury da Oksana suna hidimar majagaba na musamman.

“ABIN DA NA YI DA-NA-SANI A KAI KAWAI”

Kamar yadda furucin waɗannan masu wa’azi ya nuna, ƙaura zuwa wasu wurare don ƙara yin hidima yana bukatar ka dogara sosai ga Jehobah. Hakika, waɗanda suke hidima a inda ake bukatar masu shela suna fuskantar ƙalubale a sabon yankinsu, amma suna farin ciki sosai don suna wa’azi ga mutanen da suke son jin saƙon Mulki. Shin za ka iya taimaka ta yin wa’azi a yankin da har ila ana bukatar masu wa’azin bisharar Mulki sosai? Idan ka tsai da shawarar yin haka, kana iya jin kamar Yury, wanda ya ce game da shawararsa na yin hidima a inda ake bukatar masu shela sosai: “Abin da na yi da-na-sani a kai kawai shi ne ban soma da wuri ba.”

^ sakin layi na 20 Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 1999, shafuffuka na 23-27, na Turanci.