Koma ka ga abin da ke ciki

Sun Ba Da Kansu da Yardan Rai​—A Albaniya da Kosovo

Sun Ba Da Kansu da Yardan Rai​—A Albaniya da Kosovo

 Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Gwen daga kasar Ingila ta fada yadda ta ji saꞌad da ta je hidima a inda ake bukatar masu waꞌazi a kasar Albaniya. a Ta ce: “Ban taba sanin cewa zan je inda ake bukatar masu waꞌazi don in yi wa Jehobah hidima a irin wannan hanyar ba.”

 ꞌYarꞌuwa Gwen, tana cikin Shaidu da yawa da suka kaura zuwa Albaniya don su tattara ‘arzikin’ dukan alꞌummai. (Haggai 2:7) Me ya sa suka yanke wannan shawarar? Wane shiri suka yi don su iya kaura? Me ya taimaka musu su ci gaba da hidimarsu duk da matsaloli da suka fuskanta?

Yanayinsu Dabam-dabam ne, Amma Burinsu Daya Ne

 Duka masu shela da suka kaura zuwa Albaniya don su taimaka suna da buri daya: Suna kaunar Jehobah kuma suna so su taimaka wa mutane su san shi.

 Wadannan ꞌyanꞌuwan sun yi wasu canje-canje a rayuwarsu kafin su kaura. Kuma hakan ya taimaka musu su iya hidima a kasar waje. Gwen ta ce: “Da farko, na shiga rukunin masu yaren Albaniya da ke inda nake zama. Saꞌan nan na je Albaniya don in halarci taron yanki. Daga baya, na koma na yi zama a wurin na dan lokaci don in koyi yaren da kyau.”

Hoton Gwen

 Akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Manuela. A lokacin da take shekara 23, ta bar yankin da take zama a kasarsu Italiya, kuma ta kaura zuwa wata karamar ikilisiya don ta taimaka. Ta ce: “Na yi hidima a wurin na tsawon shekara hudu sai na ji labari cewa ana bukatar masu waꞌazi sosai a Albaniya. Na shirya kuma na je wurin hidima na ꞌyan watanni.”

Manuela (A tsakiya)

 Akwai wata ꞌyarꞌuwa mai suna Federica. Da take shekara bakwai kuma ta halarci wani taron yanki, ta ji labari cewa ana bukatar masu waꞌazi a Albaniya. Ta ce: “Danꞌuwan da ya ba da rahoton ya ce masu shela da ke hidima a Albaniya suna nazari da mutane da yawa. Yawancin mutanen na zuwa taro. Sai na gaya ma iyayena cewa ni ma zan so in je hidima a Albaniya. Da jin hakan, sun yi mamaki sosai sai babana ya ce, ‘Ki sa shi a adduꞌa kuma idan nufin Jehobah ne, za ki je hidimar.’ Bayan wasu ꞌyan watanni, sai aka ce iyalinsu su je kasar Albaniya su yi hidimar!” Yanzu Federica ta yi girma kuma ta auri wani danꞌuwa mai suna Orges. Su biyun suna hidima ta cikakken lokaci a Albaniya.

Hoton Orges da Federica

 Akwai wani danꞌuwa mai suna Gianpiero da ya yi murabus daga aiki, sai shi da matarsa Gloria suka kaura zuwa Albaniya. Ya ce: “Mun yi renon yaranmu biyar a kasar Italiya. Uku daga cikinsu sun kaura kasar waje don su yi hidima a inda ake bukatar masu waꞌazi. Akwai wata Hasumiyar Tsaro da ta fito kuma muka karanta wani talifi a ciki mai jigo ‘Za Ka Iya Ketaro Zuwa Makidoniya?’ Talifin ya sa mu tunani sosai. Sai muka zauna muka shirya yadda za mu yi amfani da fensho dina don mu iya yin hidima a kasar Albaniya.”

Hoton Gianpiero da Gloria

Sun Yi Shiri da Kyau

 Wadanda suke so su yi hidima a inda ake bukatar masu waꞌazi suna bukatar su zauna kuma su yi shiri da kyau. (Luka 14:28) Daya daga cikin abin da za su yi shi ne su tabbata cewa za su iya kula da kansu a wurin. Gwen da aka ambata dazu ꞌyar Ingila, ta koma zama da ꞌyarꞌuwarta don ta iya tara kudi. Christopher da matarsa Sophia daga kasar Ingila sun ce: “Mun sayar da motarmu da kujerunmu don mu tara kudi. Burinmu shi ne mu yi hidima a Albaniya akalla shekara daya.” Amma sun fi shekara daya suna hidima a wurin.

Hoton Christopher da Sophia

 Abin da wasu masu shela suke yi shi ne su tara kudi sai su tafi kasar Albaniya. Bayan kudin ya kare sai su koma kasarsu su yi aiki su tara kudi sai su sake dawowa. Abin da Eliseo da Miriam suka yi ke nan. Eliseo ya ce: “Miriam ta fito ne a wani birni a Italiya inda baki suke yawan zuwa. A wurin, samun aiki na dan lokaci bai da wuya. A shekara mukan je wurin da rani mu yi wata uku muna aiki don mu tara kudi. Bayan haka, sai mu dawo Albaniya mu ci gaba da hidima na wata tara. Kudin da muka tara ne muke kashewa. Mun yi hakan na tsawon shekara biyar.”

Hoton Miriam da Eliseo

Yadda Suka Magance Matsaloli

 Masu zuwa inda ake bukatar masu waꞌazi suna bukatar su koyi sabbin abubuwa bayan sun kaura. Idan suka bi shawara da misalin ꞌyanꞌuwa da ke wurin, hakan zai taimaka musu su magance matsalolinsu. Sophia, da aka ambata dazun ta ce: “A kasar Albaniya, a lokacin sanyi, gidaje sukan yi sanyi fiye da inda na fito. Na lura da yadda ꞌyanꞌuwa mata suke sa tufafi a wurin, sai ni ma na fara sa tufafi kamar su.” Akwai wani danꞌuwa mai suna Grzegorz da matarsa, Sona, sun fito ne daga kasar Poland don su taimaka a wani kyakkyawan birnin Prizren, a Kosovo. b Grzegorz ya ce: “ꞌYanꞌuwa da ke wurin suna da saukin kai da kirki kuma da hakuri! Suna taimaka mana mu koyi yaren da kuma wasu abubuwa. Alal misali, sun nuna mana shaguna da ake sayar da kaya araha kuma sun nuna mana yadda za mu yi cefane a kasuwar da ke garin.”

Abubuwan da Suka Sa Su farin Ciki

 Wadanda suka kaura zuwa kasashen waje don su yi hidima a inda ake da bukata sukan kulla abota da ꞌyanꞌuwa da ke wurin kuma sun gane alꞌadarsu. Sona ta ce: “Na ga yadda kaunar da Jehobah yake nuna mana take gyara rayuwar mutane. ꞌYanꞌuwan sun karfafa bangaskiyata. Da suka koya game da Jehobah, na ga yadda suka bar abubuwan da suka yi imani da su a dā kuma suka gyara rayuwarsu. ꞌYanꞌuwa a ikilisiyar sun nuna suna bukatar taimakonmu kuma mun taimaka musu. Mun yi hidima tare da ꞌyanꞌuwa maza da mata da suka zama abokanmu.” (Markus 10:​29, 30) Gloria ta ce: “Na san ꞌyanꞌuwa mata da yawa da suka jimre tsanantawa daga mutanen garinsu da ba sa son Shaidu. Ganin irin kaunar da suke wa Jehobah ya karfafa ni sosai.”

Hoton Grzegorz da Sona

 Masu zuwa hidima a inda ake bukatar masu waꞌazi suna samun damar koyan darussa da yawa da ba za su koya a gida ba. Alal misali, sun gano cewa yin wani abu mai wuya a hidimar Jehobah yana sa farin ciki. Wani mai suna Stefano ya ce: “A kasarmu, na saba yin waꞌazi ta waya kuma furuci kadan ne kawai nake yi. Amma mutanen albaniya suna son yin dogon hira musamman idan suna shan shayi. Da yake ni mai jin kunya ne, da farko akan kunyatar da ni kuma in rasa abin da zan fada. Amma yanzu ina mai da hankali a kan mutanen kuma ina jin dadin yin hira da su. Ban da haka ma, ina jin dadin waꞌazin da nake yi.”

Hoton Alida da Stefano

 Leah da maigidanta William sun kaura daga Amirka zuwa kasar Albaniya. Ta ce: “Yin hidima a nan ya taimaka mana kada mu nace a kan raꞌayinmu kuma ya kyautata yadda muke rayuwa. Mun koyi yadda za mu karbi baki, mu daraja mutane kuma mu kulla abota! Mun koyi sabbin hanyoyin yin waꞌazi da yadda za mu tattauna da mutane daga Littafi Mai Tsarki da kuma yadda za mu yi magana ba tsoro.” William ya ce: “Yawancin mutanen da suke zuwa Albaniya suna son yadda bakin tekunsu yake da kyaun gani. Ina son hawan manyan duwatsun da ke Albaniya. Amma mutanen da ke zama a nan ne suka sa na fi son wurin. Mutanen da ke kauyuka da yawa a yankinmu ana musu waꞌazi ne kawai a lokacin da aka shirya yin waꞌazi na musamman. A wasu lokuta idan muka fita waꞌazi, mukan yi yini muna wa iyalai kadan kawai waꞌazi.”

Hoton William da Leah

 Abin da ya fi sa masu hidima a inda ake bukatar masu waꞌazi farin ciki shi ne ganin yadda mutanen suke jin waꞌazi. (1 Tassalonikawa 2:​19, 20) Laura, wata matashiya ce da ta kaura zuwa kasar Albaniya don ta yi hidima. Ta ce: “Na yi hidima a Fier na dan lokaci. A cikin shekaru biyu da rabi, na ga sabbin mutane 120 da suka cancanci fita waꞌazi. Ni ce na yi nazari da 16 a cikinsu!” Wata kuma mai suna Sandra, ta tuna wani abu da ya faru kuma ta ce: “Na yi ma wata mata da ke aiki a kasuwa waꞌazi. Ta zama Mashaidiyar Jehobah kuma ta koma kauyensu. A lokacin da na ji daga gare ta, ta ce ta soma nazari da mutane goma sha biyar!”

Hoton Laura

Hoton Sandra

Jehobah Ya Albarkaci Hakurin da Suka Yi

 Wasu masu hidima da suka zo taimakawa a Albaniya shekaru da yawa da suka shige har ila suna wurin kuma suna jin dadin hidimarsu. Sun yi mamakin ganin cewa wadanda suka yi musu waꞌazi tun dā can daga baya sun soma bauta wa Jehobah. (Mai-wa’azi 11:6) Christopher da aka ambata dazun ya ce: “Na hadu da wani mutum da na soma nazari da shi a lokacin da na fara zuwa Albaniya. Na yi mamakin yadda ya tuna yadda muka tattauna Kalmar Allah a baya. Yanzu shi da matarsa sun zama Shaidun Jehobah.” Federica da aka ambata a baya ta ce: “Na je wata ikilisiya, sai wata ꞌyarꞌuwa ta zo ta same ni ta tambaye ni ko na tuna da ita. Ta ce na taba mata waꞌazi shekaru tara suka shige. Bayan wani lokaci da na kaura zuwa wani gari, ta yi nazari kuma ta yi baftisma. Na dauka shekarunmu na farko a Albaniya banza ne. Amma ba haka ba ne!”

 ꞌYanꞌuwa maza da mata da suka kaura zuwa kasar Albaniya ko Kosovo sun gan yadda Jehobah ya albarkaci kokarce-kokarcensu kuma ya taimaka musu su yi rayuwa mai kyau. Eliseo da ya yi hidima a Albaniya na shekaru da yawa ya takaita labarinsa ya ce: “Mu ꞌyan Adam mukan yi tunani cewa ba mu da matsala idan muka dogara ga kayan duniya. Amma hakan ba gaskiya ba ne. Kaꞌidodin Jehobah ne kadai za su iya sa rayuwarmu ta kasance da maꞌana kuma ta yi kyau. Hidimar da nake yi a inda ake da bukata ta sa na ga tabbacin hakan. Na ga cewa ina da daraja kuma ina da amfani. Yanzu ina da abokai da burinmu daya ne.” Sandra ma ta yarda da hakan, ta ce: “A lokacin da na kaura zuwa wurin da ake bukatar masu waꞌazi, na ji cewa Jehobah ya sa in cika burina na yin hidima a kasar waje. Kuma ban yi da-na-sanin kaura zuwa kasar Albaniya ba, ba farin ciki da ya fi irin wannan.”

a Don samun karin bayani a kan tarihin aikin waꞌazinmu a kasar Albaniya, karanta 2010 Yearbook of Jehovah’s Witnesses.

b Kosovo yana arewaci maso gabashin Albaniya. A wannan yankin, mutane suna yin daya daga cikin yarukan Albaniya. Shaidun Jehobah daga kasar Albaniya da kasashen Turai da kuma Amirka, sun ba da kai kuma sun je Kosovo don su yi ma mutanen da suke wani yaren mutanen Albaniya waꞌazi. A shekara 2020, an riga an samu masu shela 256 da suke ikilisiyoyi takwas da rukunoni biyar.