Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Alisa

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Turkiya

Sun Ba da Kansu da Yardar Rai​—A Turkiya

KIRISTOCI a ƙarni na farko sun saka ƙwazo sosai don su taimaka wa mutane da yawa su ji wa’azin ‘mulkin’ Allah. (Mat. 24:14) Wasu ma har sun yi tafiya zuwa ƙasashe don su yi wa’azi. Alal misali, a lokacin da manzo Bulus yake yin tafiye-tafiyensa don wa’azi, ya je wani yanki da yanzu ake kira Turkiya kuma ya yi wa’azi sosai a wurin. * A shekara ta 2014 bayan wajen shekaru 2,000, an ƙarfafa ’yan’uwa su je Turkiya domin yin kamfen na wa’azi na musamman a wurin. Me ya sa ake bukatar a yi wannan kamfen na wa’azi? Kuma su waye ne suka je yin wa’azin?

“ME KE FARUWA A NAN?”

Shaidun Jehobah wajen 2,800 ne suke Turkiya, amma mutanen ƙasar sun fi miliyan 79. Wannan yana nufin cewa kowane Mashaidi yana bukatar ya yi wa mutane 28,000 wa’azi. Hakan ya nuna nufin cewa Shaidun Jehobah sun yi wa mutane kaɗan ne kawai wa’azi a ƙasar. Abin da ya sa ake bukatar a yi wannan kamfen na wa’azi na musamman a Turkiya shi ne don a iya yi wa mutane da yawa wa’azi a ɗan lokaci. ’Yan’uwa maza da mata ’yan ƙasar Turkiya guda 550 daga wasu ƙasashe suka je Turkiya don yin wa’azi tare da ’yan’uwan da ke ƙasar. Shin sun yi nasara kuwa?

An yi wa’azi a ƙasar sosai. ’Yan’uwa daga wata ikilisiya a Istanbul sun rubuta: “Da mutane suka gan mu, sai suka tambaye mu: ‘Shin kuna yin babban taro ne a nan? Muna ganin Shaidun Jehobah a ko’ina!’” Ban da haka, ’yan’uwa a wata ikilisiya a birnin Izmir sun rubuto cewa: “Wani mutum mai aiki a tashar taksi ya zo ya sami wani dattijo kuma ya tambaye shi, ‘Me ke faruwa a nan? Kamar kun ƙara ƙwazo a wa’azinku fiye da dā?’” Babu shakka, mutane sun lura da wannan wa’azi na musamman da aka yi.

Steffen

’Yan’uwan da suka zo daga wasu ƙasashe sun ji daɗin wa’azin sosai. Wani ɗan’uwa mai suna Steffen da ya zo daga ƙasar Denmark ya ce: “Kowace rana ina haɗuwa da mutanen da ba su taɓa ji game da Jehobah ba. Hakan ya sa na san cewa ina koya wa mutane sunan Jehobah.” Wani kuma mai suna Jean-David da ya zo daga ƙasar Faransa ya rubuto mana cewa: “Mun yi wa’azi a wani titi sa’o’i da yawa kuma mun ji daɗin wa’azin sosai, yawancin mutane a wurin ba su san Shaidun Jehobah ba, kuma idan muka shiga kowane gida, mukan sami wanda za mu yi masa wa’azi da nuna masa bidiyo kuma mu ba shi littafi.”

Jean-David (tsakiya)

’Yan’uwa guda 550 da suka je yin wa’azi a ƙasar sun ba wa mutane littattafai kusan 60,000 a cikin sati biyu kawai! Babu shakka, mutane da yawa a wurin sun ji wa’azi.

’Yan’uwan sun ƙara ƙwazo sosai a yin wa’azin. Wannan wa’azin da aka yi a ƙasar ya ƙarfafa ’yan’uwa da ke wurin sosai. Hakan ya sa ’yan’uwa da yawa sun soma yin tunanin fara hidima ta cikakken lokaci. Kuma adadin majagaba na kullum a ƙasar Turkiya ya ƙaru da 82 bayan shekara ɗaya da aka yi wannan wa’azin.

Şirin

Waɗanda suka zo daga wata ƙasa don yin wa’azin sun faɗi yadda hidimar nan ta taimaka musu bayan sun koma ƙasarsu. Wata ’yar’uwa daga ƙasar Jamus mai suna Şirin ta rubuto mana cewa: “’Yan’uwa da ke ƙasar Turkiya suna yin wa’azi a ko’ina ba tare da matsala ba. Ina jin kunyar yi wa mutane wa’azi sa’ad da nake harkokina na yau da kullum. Amma ganin yadda ’yan’uwan da suke wurin suke wa’azi da kuma yin addu’a sosai ya taimaka min na kasance da gaba gaɗi, ba kamar dā ba. Kuma na yi wa’azi a tashar jirgin ƙasa, na ba da warƙoƙi, yanzu ba na jin kunya kamar yadda nake ji dā.”

Johannes

Wani ɗan’uwa mai suna Johannes daga ƙasar Jamus ya ce: “Na koyi darussa da za su taimaka min a hidimata. ’Yan’uwa a Turkiya suna so su yi wa mutane da yawa wa’azi. Don haka, suna amfani da duk wata damar da suka samu don su yi wa’azi, sai ni ma na ƙuduri aniya cewa idan na koma ƙasar Jamus zan yi wa’azi a duk lokacin da na samu dama. Kuma yanzu ina yi wa mutane da yawa wa’azi fiye da dā.”

Zeynep

Wata ’yar’uwa mai suna Zeynep daga ƙasar Faransa ta ce: “Wannan wa’azin da muka je ya taimaka min sosai don yanzu ina dogara ga Jehobah da kuma saka ƙwazo a wa’azi fiye da dā.”

’Yan’uwan sun kusaci juna sosai. Ba zan taɓa manta da yadda suke ƙaunar juna kuma suka kasance da haɗin kai duk da cewa sun fito daga ƙasashe dabam-dabam ba. Jean-David wanda aka ambata ɗazu ya ƙara da cewa: “Mun ga cewa ’yan’uwan suna karɓan baƙi, don sun ɗauke mu a matsayin abokansu da kuma iyalinsu, gidansu ya zama kamar gidanmu. Ina yawan karantawa a littattafanmu cewa muna da ’yan’uwa a duk faɗin duniya. Amma yanzu ne na san cewa hakan gaskiya ne. Ina alfahari cewa ni Mashaidin Jehobah ne, kuma ina yi masa godiya saboda wannan gata.”

Claire (a tsakiya)

Wata ’yar’uwa mai suna Claire daga ƙasar Faransa ta ce: “Ko da yake mun fito ne daga ƙasashe kamar su Denmark ko Faransa ko Jamus ko kuma Turkiya, dukanmu ɗaya ne. Kamar dai Allah ya kawar da duk wani abin da yake kawo bambanci tsakanin mutane.”

Stéphanie (a tsakiya)

Wata ’yar’uwa mai suna Stéphanie da ta fito daga ƙasar Faransa ta ce: “Wannan wa’azin da muka je ya koya mana cewa abin da yake sa mu kasance da haɗin kai ba al’adarmu ko yarenmu ba ne, amma ƙaunar da dukanmu muke yi wa Jehobah ne.”

AN SAMU ALBARKA SOSAI

’Yan’uwa da yawa da suka je yin wa’azin, sun soma yin tunanin ƙaura zuwa ƙasar Turkiya don su taimaka da yin wa’azi. Kuma ’yan’uwa kaɗan daga cikinsu sun riga sun ƙaura. Muna yaba wa waɗannan ’yan’uwa da suke ƙaura zuwa inda ake bukatar masu wa’azi.

Alal misali, akwai wani rukunin da ba a mai da shi ikilisiya ba da suke da masu shela guda 25. Dattijo guda ɗaya ne kawai ke wurin shekaru da yawa. Amma a shekara ta 2015, ’yan’uwa shida daga ƙasar Jamus da kuma Netherland sun ƙauro zuwa wurin don su taimaka. Babu shakka, ’yan’uwan da ke wurin sun yi farin ciki sosai.

YIN HIDIMA A INDA AKE BUKATAR MASU SHELA

Mene ne waɗanda suka ƙaura zuwa Turkiya suka ce game da irin rayuwa da suke yi a wurin? Babu shakka, a wasu lokuta suna fuskantar matsaloli, amma yin wa’azi a inda ake bukatar masu shela yana kawo albarka sosai. Bari mu ji abin da wasun su suka ce:

Federico

Wani magidanci mai suna Federico da ya ƙauro daga ƙasar Sifen kuma shekarunsa 40 da wani abu, ya ce: “Da yake ba ni da dukiyar da za ta iya raba hankalina, ina mai da hankali ga abin da ya fi muhimmanci.” Shin zai iya ba ma wasu shawara su soma yin irin wannan hidimar? E, ya ce, “Babu tantama zan yi hakan! Idan ka ƙaura zuwa wata ƙasa don ka taimaka wa mutane su san Jehobah, hakan yana nufin ka dogara gare shi. Kuma hakan zai taimaka maka ka ga yadda Jehobah yake kula da kai fiye da dā.”

Rudy

Wani ɗan’uwa magidanci mai suna Rudy daga ƙasar Netherland da shekarunsa ya kusan 60, ya ce: “Muna farin cikin kasancewa a kan gaba sa’ad da muke hidima da kuma yi wa mutanen da ba su taɓa ji game da Jehobah ba wa’azi. Ganin yadda mutane suke farin ciki sa’ad da suka soma bauta wa Jehobah yana sa mu farin ciki sosai.”

Sascha

Wani ɗan’uwa magidanci mai suna Sascha daga ƙasar Jamus da shekarunsa 40 da wani abu, ya ce: “A kowane lokaci da na je wa’azi ina haɗuwa da mutanen da ba su taɓa jin wa’azi ba. Kuma taimaka wa irin waɗannan mutanen su san Jehobah yana sa ni farin ciki sosai.”

Atsuko

Wata ’yar’uwa mai suna Atsuko daga ƙasar Jafan da shekarunta 35 ne da wani abu, ta ce: “A dā ina son Armageddon ya zo da sauri. Amma da na ƙaura zuwa Turkiya, na gode wa Jehobah sosai don haƙurin da yake nuna wa har yanzu. Ganin yadda da Jehobah yake ja-gorancin batutuwa da suka shafi yin wa’azi a dukan duniya ya sa in kusace shi sosai.”

Wata ’yar’uwa mai suna Alisa daga ƙasar Rasha da shekarunta 30 ne da wani abu ta ce: “Hidimar nan ta sa ni na ga yadda Jehobah yake nuna mana alheri.” (Zab. 34:8) Ta daɗa cewa: “A gare ni Jehobah Ubana ne da kuma aminina wanda ko a wane irin yanayi ina samun damar sanin shi. Ina farin ciki da kuma godiya don albarkar da Jehobah yake min a rayuwa!”

“KU DUBA GONAKI”

Saboda wa’azin nan da aka yi a ƙasar Turkiya, mutane masu dumbin yawa sun ji game da Jehobah. Amma duk da haka, akwai yankunan da har ila ba a yi wa’azi a wurin ba. A kowace rana, masu shela da suka ƙaura zuwa ƙasar Turkiya suna haɗuwa da mutanen da ba su taɓa ji game da Jehobah ba. Shin za ka so yin hidima a irin wannan wurin? Idan haka ne, muna ƙarfafa ka: ‘Ka tāda idanunka, ka duba gonaki, sun rigaya sun yi fari [ko sun nuna], sun isa girbi.’ (Yoh. 4:35) Shin za ka so ka taimaka a wata ƙasa da gonaki “sun rigaya sun yi fari [ko nuna]”? Idan za ka so yin haka, zai dace ka soma yin shiri don ka cim ma burinka. Kuma ka kasance da tabbacin cewa: Idan ka saka ƙwazo a yin wa’azi ‘har zuwa iyakan duniya’ za ka sami albarka ba kaɗan ba.​—A. M. 1:8.

^ sakin layi na 2 Ka duba ƙasidar nan “See the Good Land,” shafuffuka na 32-33 a Turanci.