Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana

Sa’ad da Bala’i Ya Abko Mana

Andrew, daga ƙasar Saliyo ya ce: “Da farko mun yi baƙin ciki sosai domin zaftarewar ƙasa da ambaliyar ruwa ta hallaka dukiyarmu gaba ɗaya.”

David daga Virgin Islands ya ce: “Bayan da aka yi wata guguwa da iska, mun koma gida kuma muka tarar da cewa ba abin da ya rage. Mun yi baƙin ciki sosai kuma ’yata ta sunkuya tana ta kuka.”

IDAN bala’i ya taɓa abko maka, wataƙila hakan ya sa ka rikice, ka damu kuma ka kasa yin barci kamar yadda ya faru da mutane da yawa. Yawancin mutanen da bala’i ya abko musu sukan ƙaraya kuma su gaji da rayuwa.

Idan kai ma ka rasa dukiyarka sanadiyar wani bala’i, hakan zai iya sa ka ji cewa ka gaji da jimrewa ko kuma ka ji cewa rayuwa ba ta da wani amfani. Amma Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa rayuwa tana da amfani kuma ya ƙara tabbatar mana da cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA FAƊA YANA SA MU KASANCE DA BEGE

Littafin Mai-Wa’azi 7:8 ya ce: “Gwamma ƙarshen abu da farawarsa.” Idan bai jima da bala’i ya same ka ba, za ka iya jin cewa rayuwarka ta taɓarɓare. Amma idan ka jimre kuma ka yi aiki da ƙwazo, za ka iya kyautata rayuwarka kuma abubuwa za su yi kyau kamar yadda suke a dā.

Littafi Mai Tsarki ya ce lokaci yana zuwa da “ba za a sake jin muryar kuka . . . ko ƙarar kukan azaba” ba. (Ishaya 65:19) Hakan zai faru a lokacin da aka mai da duniya aljanna a ƙarƙashin Mulkin Allah. (Zabura 37:​11, 29) Bala’i ba zai sake abko ma kowa ba. Duk wani baƙin ciki ko ɓarnar da bala’i ya janyo mana za su shuɗe domin Allah Mai Iko Duka ya yi alkawari cewa: “Ba za a sāke tunawa da abubuwan dā ba, tunaninsu ma ba zai zo wa mutane ba.”​—Ishaya 65:17.

Ka yi la’akari da wannan: Mahaliccinmu yana shirin ba mu “bege mai kyau a ƙarshe,” wato begen yin rayuwa mai kyau a Mulkin Allah. (Irmiya 29:11) Shin sanin wannan gaskiyar za ta sa ka ɗauki rayuwa da muhimmancin kuwa? Matar da muka yi maganar ta a talifi na farko mai suna Sally, ta ce, “Yin tunani a kan abubuwan da Mulkin Allah zai yi mana a nan gaba zai taimaka mana mu manta da matsalolinmu kuma mu mai da hankali a kan abubuwan da suke faruwa a yanzu.”

Muna ƙarfafa ka ka koyi wasu abubuwan da Mulkin Allah zai yi wa ’yan Adam. Yin hakan zai ba ka tabbaci cewa duk da bala’in da ya abko maka, rayuwa za ta ci gaba da kasance da muhimmanci a gare ka yayin da kake jiran lokacin da bala’i ba zai sake abko maka ba. Ko a yanzu ma, Littafi Mai Tsarki ya ba da shawarwari masu amfani da za su taimaka maka ka jimre a lokacin da bala’i ya abko maka. Bari mu ga kaɗan daga cikin shawarwarin.